Sashe 48
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu shi babu labarinsa fa, kiran nan sai ta wuni tana yi da kyar ya daga idan kuma ya daga din kayya de mata maganarta yake yi a kullum baya bari su zurfafa zaurance ko yayane, muryarta na rawar nan a tausashe ta ce" Baban Abah, shikenan idan na tafi kuma babu wani maganar da muka tsayar ?
"
Sai da ya gama dan rike rike maganarsa sannan ya ce" Dangane da me?"
Dik irin iya takunta sai ta ji wani dar dar da kuma nauyin maganar a harshenta bayan ta riga ta shirya tsaf yaki da duk wanda zai nemi tare hanyarta a kan maganar Babangida ciki kuwa koda shi ne.
Muryarta a sanyaye ta ce " MARSHAL, shin baka amshi soyayata bane?, Ina nufin ko na maka tsufa ne?....."
Tsabar rigima irin ta MARSHAL sai ya samu kansa da yin dan murmushi, domin shi ai bai ga wani girman da wannan zata wani yi masa ba, duka duka shekarar nawa cema tsakaninsu?
Ai yarinya ce mana!.....zai kuma tabbatar mata cewa yarinyar ce ita a hankali
Gannin murmushi a saman lebensa ya sakata a halin rudu da rabuwar tunani kashi biyu
Sai dai jin muryarsa a nutse yana fadin magana kamar haka ya sakata lumshe idannuwanta tana ji a ranta eh lalle wannan din shine daya tak namijin da ya isa ya ganta a matsayin matar aure" Minal, ai ba wannan maganar......., Kar ki wani damu kanki da wannan, lokaci nake jira..........ke fa jinnin mimi ce, dole kece zaki iya bani farin ciki............, Ki dan bani time na sake daidaita lamarin gidanmu,zan zo da kaina"
Hankali kwonce take ta murmushi da wani sassada kai irin ta ji kunyar nan, sosai kalamansa suka sakata farin ciki marar misaltuwa dan bai taba fada mata haka ba gaskiya
Farin cikinta bai katse ba ya dora da fadin" Yaushe ne auren Yaran nan?"
Da dan karsashi ta sanar masa cewa bai fi saura sati biyu ba
Kai ya gyada a hankali ya ce" Kin san na ce ba zan yi masu gadaje ba, dan hurumin mahaifinsu ne ko?"
Kai ta sake gyadawa tana jin kamar tace masa mahaifinsun banza mahaifinsun wofi, mema yake da shi da zai iya yiwa
anta gadajen daki?, Mutumen da ya so nuna dayar ba zai badata wa Elhaji tanko ba wai bincike ya nuna baa mutumen kirki bane?
Ai maganar mutumen kirki ta kare tunda ya tara
an banki, shi da bashi da su sai ya yi hakuri kawai yaa tattare tsohuwar dardumarsa, mutun sai shegiyar akidar tsiya shi mai talautaciyar zuciya
"Amma Amir zai ganki kafin ki tafi, plz ki kula da kanki......" Ya karashe a dan gajiye da hayaniyar sannan ya bude jaridarsa ya dora daga inda ya tsaya
Kai subahanalah, kwarankwatsa wannan gayen duniya ne, bama irin da ya wani sasauta murya ya furta mata ta kula da kan nan nata sai ya sakata sakin baki tana kallon tsararan gys tana hango abubuwa da dama a cikin kwakwaluwarta
Da kyar ta iya rarashin kanta ta bar inda yake ta koma bangaren su sai watsa hakora take suka idasa kimtsawa ta kuma haye wajen Mama
Sallama ta yi a lokacin Maman na zaune saman gado, hijabin nan dai da ta mayar abin zama koda yaushe zumbulele mai kaurin tsiya da kuma duhu ne a jikinta, baka gannin komai na jikinta sai carbinta dake hannunta tana ja, tana zaune a saman gado ne tana jan carbin bayanta kuwa wannan shegiyar yarinyar mai kama da ya'yan nasaru ce kwonce tana barci ita yar gata kafafuwanta daya a saman cinyar ta Mama wai bigewa ta yi kuma ta saka Maman a gaba tana hawaye shine aka shafa mata man zafi barci ya kwasheta bata fara harbe harben gigin barcin ba da tuni sun raba wajen zaman
Gashin kan yarinyar take kallo bayan ta duka nan kusan gadon sai kuma taa dauke kanta tana jin wannan yarinyar sam bata yi mata ba, ita fa in zata tuna bata taba gaisheta ba, yarinyar kamar wata mai asali sai shegen girman kan tsiya, ita da ta fahimci wacece ita sai da ta yi mamaki ta zata ai Yar Maman ce itama ta cikinta dan ta ga ai su MARSHALma farare ne ko farin ABAH ta yi, sai kuma ta gane inda zancen ya dosa, itama Maman in ba wani neman fitina ba meye dadinka da kishiya har da zaka dauki shegenta ka runguma?
Idan wata yar mai kunnar bakin wake ce ta tashi dare daya ta kone uban kowa a huta ko?
Jarabar yayume yayumen tsiya
Murya a tausashe ta ce" Mama mu mun gama shiryawa, zamu tafi in sha Allah, dan Allah idan na bata maki ki yafe min Mama"
Mama ta yi murmushi tana fadin" Haba dai yata, ai ba wani batawa, ni dai zan nemi afuwa masha Allah kin zo banda aiki babu abinda aka ringa saka ki, na gode na gode sosai Minal Allah ya saja maki da alkhairi ya biya, dan gaskiya ni ban isa in biyaki ba, na gode sosai, ki ce yau zaku wuce kuma?"
Minal na murmushi ta ce" Eh mama yau zamu tafi gidan Aunty kawar Hajia sai mu wuce da asuba wannan wace suka zo gaisuwar nan kusan sau uku"
Mama na sauke kafar Zahra daga cinyarta ta muzguna ta mike tana fadin" Allah sarki, eh kwarai na gane matar mai mutunci, na gode sosai Minal Allah ya biya , gaskiya kin kyauta mun gode sosai Minal"
Wajen sif dinta ta je ta ja zata bude amma ta ji a rufe, dole ta dawo inda Fatima take kwonce ta shiga tashinta a hankali tana dan taba wajen wuyanta tana kiran sunnanta, hakan ya sa ta yi mika ta bude idannuwanta masu shanye da launin ja na abin barci tana kallon Maman da yannayin tambayar me yasa aka tasheta?
Mama ta ce" Ina ky din sif ?"
Dan luuuuu ta yi da idannuwan nata sannan ta mike tana ziro kaffafuwanta kasa, a lokacin suka yi ido hudu da Minal dake binta da wani kallon da bata san ko na meye ba, dama ga abin barci ga bakinta da bata budewa sam idan ta farka a barci har sai ta kuskure sai ta dauke dubanta bayan ta mata alamun gaisheta da hannunta sannan ta karasa wajen jakar Maman ta hannu ta bude ta lalubo key din ta je ta budewa Maman sif din ta wuce bayi
Baki Minal ta dan tabe a ranta tana ayyana ' Lalle kin samu guri yarinya, kece harda saka hannu a jakar Mama kai tsaye abinki kina tafe kina wani bude duwawu ke ga mai lasisin iskanci........., Ba damuwa kin sakan shaku a kanki ni kuma zan yi maganinki in dai na shigo gidan nan, dan in sha Allah sai gannin mamah ya gagareki ki je cen ki karata da uwarki, koda yake ta yiwu kafin na shigo din kun bar gidan ke da uwar taki baki daya dan ai Doctern ya mutu du wata wace aure ya hada sai ta dan harhada tarkacenta ta je gidan uba nata'
Alkhairi irin na su atampopi da turare Mama ta yi mata, kasan cewar dama bata rabo da tara yan atampopi a kayanta, turarurruka kuwa gidan kennan, Mamah sarkin turare, har Zahra ta samu daya itama bayan an ja mata kunnen sauran a jishi kauuuuu a jikinta kamar zata je gasar gwada kanshi ta zuba mata a babbar leda blue tace dan Allah kadan ne ba yawa, ita kuma ta ringa nuna ai ba zata amsa ba su da suka zo ta'aziya kuma sai a masu kyauta?, Da kyar dai Mama ta shawo kanta ta yarda ta amsa din ta dauko kayanta Maman na biye da ita dan ta yiwa mamansu godiya da kuma bankwana
Gashin kanta ta hade ta daure tana ta murmushin turaren nan, bude kwalbar ta yi ta shiga dan fesawa a wajen wuyanta da kuma tafukan hannayenta, sai kuma ta shafo ta sinsina tana wani lumshe ido tana jin farin ciki a cikin zuciyarta da kwanciyar hankali kai ta yi missing din turare, irin sosai din nan wallahi, gashi mai yawa ne ga sansanyan kamshi a tare da shi...............
Wayarta ce ta shiga kuka da kida a hankali na kasida yana tashi mai taken bari mu gaida batula...............
Daukowa ta yi tana kallon sunnan da ta dora masa, BAKONA hade da heart a jiki, ba dan komai ba sai dan ma'anar hakan kennan....bako ne shi a zuciyarta
Dan murmushi ta yi, dabi'unsa baki ne a duniyarta, irin yadda yake ba soyayya dama da lokaci bakin abubuwa ne a rayuwarta......kalamansa kansu baki ne a dduniyarta
Ajiyewa ta yi har sai da ya sake kira sannan ta daga a sanyaye ta yi sallama tana mikewa ta kashe ACn dake kunne dan sauka zata yi kitchen wajen su aunty
A sanyaye ta amsa sallamarsa sannan ta yi shiru tana sauraronsa
Hassan ya yi murmushi ya ce" Gimbiyata, yaushe zan zo na yi gaisuwa ne?
Ina so na zo na yiwa Mama gaisuwa da su yaya please"
Murmushin da take yawaita yi masa ta yi masa yanzunma, a hankali ta buda manyan idannuwanta ta kafe waje daya da kallo, abu daya ke yawan kayar mata da gaba wanda kuma take so duk rintsi kafin ya ga Mamah sai ta sanar masa idan har ya ga zai iya ya mike a haka in kuwa ba zai iya ba tun kafin abu ya fi karfinsu daga ita har shi gwara su hakura ke kayar mata da gaba
Watau ta sanar masa wacece ita a dunkule ba a zayane ba, tunda itama bata san a zayanan wacece ita din ba, ita dai ta san shegiya ce ita kawai, bayan wannan sauran bayanan gaskiya a rufe suke a kwakwaluwarta , inama ace ta san waye baban nata?