← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 110

Sashe 33

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mace ai sai da kanshi, yi shiru Zaran Mama zan siya maki da yawan da suka fi su, maza je ki gama shiryawa ki kwonta dare na tsalawa , ki kiyaye gobe idan aka buga maki kofa kafin ki bude ki tabatar kina cikin sutura mai kyau kin ji?"
Amsa Maman ta yi Mamah ta fito ta karasa inda yake tsaye Adawiya na hado gaba daya turarukanta jikinta na rawa tana fatan kar a kula da wayarta dake kunne tana waya da habibi dinta ta idasa hadowar ta kawo ta duka ta miko masa a cikin babar leda itama kanta a kasa ,
Amsa ya yi bai ce komai ba ya juya ya yiwa Mamah salama ya fice, sai Maman ce ta ce" Adawiya ina fata kin fahimci yayanki na nufin idan kika kuma saka turare mai karfi Allah ne kawai zai kwace ki daga hannunsa?"
Adawiya ta gyada kai tana Allah Allah Maman ta tafi, dan idan aka ga wayar yanzu ne zata sha dukan da bata sha ba a kan maganar turare
Bayan motar ya zuba kayan sannan ya shige gaba ya zauna ya kunna yana yar dariyar Aban Hafeez dake waya da matarsa yana cewa tunda ya zo suke dauki ba dadi da Marchal kan dansa wai bai zo masa da yaro ba, itama tana faman fadin ai shima da ya ji cen ya nufa babu irin rikicin da bai yi ba, wai yayama za'a tafi wajen Abansa banda shi, shi walahi a aika shi yana iya zaman jirgi shi kadai har wajen dadynsa
Sunna wannan hirrar har suka karaso
Yana budewa ya bada umarnin a kwaso baki daya kayan dake bayan motar a kai falonsa su kuma suka taho sunna zantawa da Aban Hafeez har suka isa falon
Basu zame ko'ina ba sai wajen cin abincin , da kansu suka zubawa kansu sannan suka ci cikin nutsuwa duka gama
Marshal ne ya kwashe ya kai kicin ya ajiye, a nan ya ga na jiya sunna nan summa , sai ya saka a ransa in sha Allah zai hade su duka da safe a mayar
A falo suka yada zango, dama ba wani dare ne ya tsala ba, bale a wajen maza gashi ba dati ne da su ba su da wanka sai na barci, dan haka ya saka masu tashar labarun duniya suka shiga zantawa hira ta aminai
A nutse Aban Hafeez ya ce" Baban gida, yaushe zaka daina rigima ne?"
Da dan mamaki ya kalle shi, sai kuma ya yi murmushi, dama ya san a rina wai an ari zannin mahaukaciya, tunda ya zo shiga mota ya kula kallon da yake masa bakinsa cike yake da magana ama ya kasa fada har sai da suka dawo, yama yi kokari da ya rike maganar
Yana murmushin ya ce" Fada kuma kamar wani yaro?"
Aban Hafeez ya tare shi yana fadin" Please ka bani aron hankalinka mana, ka ga dai wannan mutumen ai ba yaro bane ko, ya dace ka kyale shi ko me ya maka Freind "
Zamansa ya gyara bayan ya masa kallo daya bai ce komai ba, to me zai ce masa?

Ko me zai ce ba zai fahimta ba, lalle Joe ba yaro bane, a kadan ya bashi shekaru tara ko fi, ama kuma irin halin da yake yi da rayuwarsa yau da gobe ya saka yara kannanama basa jin nauyinsa ko kunyarsa, babu abinda ba'a yi da shi, yaro karami na iya dudura masa ashar, a lokacin da aka yi rigikin nan tsakaninsa da matar wani dan acaba ai sun kwashi kunya, sunne suka kwashi kunyar nan ba kowa ba, shi yana cen yana baza shirme a cikin gari su ya barsu da kayan kunya, fisabililahi a akuyancinsa harta matan aure bai bari ba, matan mutane yake bi dan yana rike da wani dan mukami na gidan duniya?

Matan nema basu da hankali basu san ciwon kansu ba, me zai baki wanda Allah bai baki ba?

Shima dai har ga Allah daga wannan lokacin mutuncin mutumen ya zube tasss a idannuwansa, sai dai yana bashi daraja ta girman da ya masa, ama a dazun ya taka doka ne ta yadda yake son ido rufe sai ya saka sun aikata aikin da zasu shiga dana sani mai karfin gaske, baya ciki, zai kuma yaki du wanda ya yi fito na fito da dokokin Allah
Gannin ba zai amsa shi ba ya saka shi yin dan murmushi yana kawar da maganar cen ta hanyar fadin" Yaya maganar auren nan, wani irin yayar marigayiya zaka sake aura?

Me zaka mora a tare da matar nan?

Ka fa san wacece ita ko?"
Murmushi ya yi yana shafa gaban goshinsa ya ce" Wai in tambayeka, wa ya aiko ka ka titsiyeni ne?"
Aban Hafeez ya ce" Ba titsiyewa bane, ka sani sarai ba zan ga wani abun da bai min ba a tare da kai ban fada ba, a jini ko a kyale ni ni dai ba na san na fada ba, bani da damuwa da hakan"
Murmushi ya yi yana daukan remot ya rage amon muryar TV din yana kallonsa ya ce" Freind, ai ka san ni ba damuwana ne ba abinda mace take ciki, abinda na sani shine daga bakin lokacin da zan kilace ki zaki dawo ne tawa ni kadai, ba hannaki fita zan yi ba, ba kuma CCTV zan hadaki da shi ba......Man bana tunanin zan iya aikata mata aiki da gangar jikina ta ji wani a ranta ba, sai dai idan mata take so ........"
Ya karashe yana dan sosa kunnansa hadi da sakin yar dariya dan dama da gangan ya fadi haka dan ya tabata sai Aban Hafeez ya yi abinda ya saba
Aban Hafeez ya ringa sallalami yana tafa hannu yana sake kure shi da kallo ya ce" Anya kai din nan jarabarka ba ta fi karfina ba?

Man wani lokacin sai na rasa a wani mataki zan ajiyeka, idan ka yi wani abin istazu sak, idan ka yi wani kuma tantiri sakkkk" ya fada yana kyakyacewa da daria, shima dariar yake yi yana dafe kansa yana girgiza kan nasa, yana matukar jin dadin hirantawa da bawan Allan nan, yana jinsa a sake idan yana hira da shi sosai
"Ama ka san wani abu, ina iya tabatar maka cewa, ba zaka san ka mora mace ba sai ka dauketa tun da danyatarta, tun daga sha shidan nan har zuwa talatin dai haka....Man a nan zaka san kana da mace a gefe, ba wai kai ka ringa dauko wa'inda suka girmeka dan tsohon jaraba ba, kai a ganninka sunne zasu iya jurewa rayuwa da kai?

Sun gajiya fa.........!" Ya fada yana mai son tabatar masa da son dole sai ya cire masa son auren matar nan a ransa, haka kawai shi bata yi masa ba walahi, bata kashe masa ba, bata masa komai ba, hasalima bai fi a irga da suka hadu a nan gidan ba, ama irin yadda ta nuna tana sonsa a lokacin ya yi mamaki, bata da kunya sam, ya san ba haramun bane hakan, ama a gaskiya ya dauki hakan da wata fasara daban, sai yake tunanin kowama idan har ta ganshi da dan maiko tana iya jin tana sonsa a ranta
"wannan ra'ayinka kennan Elhaji, ni a gaskiya ban ga mace ba a wajen wace zan zauna ina ihu da bakina, ka ga aikina dama na ihun ne, na yi a waje na yi a gida?, No ni ba zan iya rainon yar kowa ba, gwara idan y'ar taka ta nuna ka bani kawai........, Ni damuwata biyar ce kadai da mace, idan har bata da wadinnan abubuwan gaskiya ba zan iya ba........, Ibadah, Kanshi freind kanshi , tsafta, girki, .......nd.............nd.............

No freind idan bata da wannan experience din gaskiya ba mace bace a wajena, idan har mace bata da experience din nan.............ba zan taba iya zama da ita ba!" Ya fada a hankali yana wani lumshe lumsasun idannuwansa dan kawai ya sake kunna Aban Hafeez, sai dai koda da maganar kunna Aban Hafeez din akoy maganar abinda ke zuciyarsa ne yake amayarwa, a gaskiya yana fitar da ainahin abinda yake tunani ne .....abubuwan nan da ya zana sunne kwonciyar hankalinsa a zama da mace
Aban Hafeez kam sai ya dawo binsa da kallo, sai kuma ya girgiza kai ya sake zuba masa ido, karshe dai a bayane ya ce" Freind, koma wacece, ina fatan Allah ya baka ta gari, domin matan nan na wannan zamanin kwata kwata baka iya masu, sai ka rasa menene damuwarsu ne, ina suka saka gabansu ne?

Sai ka rasa me suke so ne?

Wani lokacin zaka ga sun dubi wanin da bai kama farcen wanda suke tare da shi ba, rudanin zuciya na saurin yin tasiri a kansu, tsakaninmu da su sai addu'a da tunatarwa da kuma yin bakin kokarinmu dan faranta masu"
Komawa ya yi a hankali cikin kujerar yana jin abu a bayansa, a hankali ya janyo dan bai kula da komai ba kafin ya zauna din ko dan Abu Hafeez ya tatare shi da sharhi ne?

Idannuwansa ya dora a kan hijabin yana kallo, tamkar ya ga bakon abu ko yana son gane menene shi a hannunsa?

A hankali ya kai wajen hancinsa dan sosai kanshin ke bashi mamaki irin yadda yake da saurin shiga hanci
Idannuwansa ya lumshe a hankali yana ciro hijabin daga hannunsa, sannan ya kai dubansa wajen da ledar biyu ke ajiye ta turarukan
A hankali ya janye hijabin ya ajiye shi a hannun kujerar sannan ya sake ba Aban Hafeez hankalinsa sunna hirarsu har sai da kusan karfe dayan dare ta gota sannan ya mike zai tafi, shi kuma ya masa rakiya yana ta fadan gaskiya ya kwana a nan, shi kuma ya kiya yace aa ba zai kwana a dakin da matarsa ta sha kwana ba, shi dai zai je gidansa..............................................
Chapter 33 · 0% Book details