← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 110

Sashe 94

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zuwa zan na kula da ita kafin yama ta yi sai a rakota ko baka ga bata da lafiya ba"
Idannuwansa ya dauke a hankali daga kan Maman ya sauke a kan ZAHRAN, kallo ne tun daga sama har kasa...., A hankali ya sauke ajiyar zuciyar yana kokarin son tuhumar kansa da aikata daya daga cikin aikin da ya fi bata masa rai a duniya, wanda ko waye ya yi a da yake iya yinsa dan gannin ya rama mata, watau raunata ZAHRAH!

Mama bata kuma bi ta kansa ba ta ajiye mata slifas dinta tana fadin" saka mu je mana ko ba zaki iya tafia bane wai sai wani hade jiki kike yi?

Ke saki jikinki tun kafin na make ki saka takalmanki mu je yau ga ya!"
Da dan sauri ya mike tsaye ya karaso inda suke yana dan soka wayarsa a aljihun wandonsa a hankali ya ce" Mamah, bara na kawota"
Yanzun kam gaba daya ta dago ta zuba masa ido tana zarro idannuwan nata a tsorace da kuma sauri ta yi baya ta fada zaune saman kujerar tana sake dago kanta dan kallon bakon ikon Allah a gabanta
A dan rikice da yannayinta ya ce" ZAHRA ki kula mana, Mamah, ko asibiti zamu kaita ne?"
MAMAH kam yanzu a dole ta ji wata kunya na neman lulubeta, ya rab, shi wai daukanta zai yi ya ratsa gidajen nan gaba daya da ita har bangarenta?

Kai?

Ya ilahi wai da gaske kuwa abinda zai aikata kennan idan aka barshi?

Mamah ta ce" Baba ka barta mana , ka ga a kawo mota nan sai ta shige mu karasa ka ji?

Je ka dauko mota"
Ajiyar zuciya ya dan sauke, ya sake kallon Zahran da ta sada kanta ta dafe kumatunta da hannayenta bibiyu dan tashin hankalin duniyar kunyar da yaa kumsa mata
Ficewa ya yi , Mama kuwa ta raka shi da ido sannan ta yi murmushi tana girgiza kanta
Tana nan tsaye ya dawo da motar, tun kafin ya shigo ta kama ZAHRAN suka fito ta sakata a motar sannan ya rufe falon ya ja su bangaren Maman
Sunna zuwa yanzun Mama a dole ta saka shi kama Zahra ya kaita ciki dan zata gaisa da yayar Maman su Abul
A hankali ya karasa dakin MAMAH da ita ya zaunar da ita saman bed
Ba zato ba tsamani sai ganninsa ta yi ya zauna daf da ita sosai sannan ya janyo kanta a hankali ya dan juyo ya rungumeta a kirjinsa ya lumshe idannuwansa
Muryarsa cen ciki ya ce" Da za'a bari na kaiki asibiti, kar aje na ji maki rauni sosai?, Shi yasa nake gudun auren wuri ZAHRAH, shin na maki rauni sosai ne?"
Idannuwanta dake lumshe ta fan bude ta zubawa kirjinsa ido sannan tana shakar dadadan turaran dake fita daga jikinsa
Kasa kasa ta iya budar bakinta da kyar bayan ta gama yanke dolema ta bashi amsa, dolema ta dan hankalttar da shi wani abin mai mahimmanci, kar ya je ya yi ta faman tunanin abinda bama haka bane, a tausashe sosai ta ce" Yayanmu, ba fa abin daga hankali, zai daina"
Maganar tata a dan cicire ne, fuskarta kawai ya iya zubawa ido , a cen cikin ransa yana jin inama a dauke ciwon a dawo masa shi jikinsa?

Shi kadai ya san irin abinda ke dawainiya da nutsuwarsa, cutuwa irin tasa itace babar cutuwa, domin bai iya raba damuwarsa da kowa ba sai Allah
Alamun ana nufo dakin ya sakata da dan sauri ta ja baya , sannan ta ringa dan jan hannunta da ya rike taf a nasa ya ki saki
Sai da aka bude ne sannnan ya saketa ya kuma bita da kallo har ta je bakin kujera ta zauna ta sake sada kanta ta dauke dubanta kwata kwata daga inda yake
Mama yi ta yi tamkar bata gane komai ba ta shigo da maganin dake hannunta ta mikawa ZAHRA da ruwa bayan ta balo mata
Ta shanye magannin sannan ta sake bata shayi mai zafin gaske hadi da Madara hadi mai kauri, nanma ta tsaya a kanta sai da ta ga ta sha masha Allah sosai har tana nuna cikinta ya cika sosai sannan ta kyaleta ta ce ta tashi ta kwonta ta huta
Kwonciyar ta yi ta juya bayanta wajen garu, shi kuwa sai a lokacin ya dan dubi Mama sannan ya dan sake sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Na tafi na dawo MAMAH"
MAMAH ta yi masa murmushi sannan ta bi bayansa
Har ya fito kofa ta yi kiransa, hakan ya sa ya dawo ta zubawa fuskarsa ido na yan dakiku,
Eh lalle abinda take gani gaskiyar kennan ba karya a tare da hakan, Allah mai iko, tun yaushe?

A sanninta ta jima tana gannin irin haka, bata taba hada hakan da komai ba sai yanzu take gane me yake nufi, watau yannayin nan na fuskarsa na yanzu a lokuta da dama idan ZAHRAH na kuka, ko ana zane su haka din nan sak take ganni a fuskar BABANGIDA, sannan kallon nan nasa na yanzu shine yake bin ZAHRAN da shi sai kuma ya sada kansa kafin ya fice ya bar gidan, kennan hakan na nufin an jima da damuwar ZAHRAH ke damunsa?

Ya Allah
Da kula Mamah ta ce" Kar fa ka damu, ba dan ciwonta ya daukaka bane na kawota nan, dan kawai na san kana da aiki yauma, ni kuma ba zan tare a cen ba, Haka din ai ba wani abu bane kowama ta nan ya bi ka ji Baba?"
Duda maganar ta dan zo masa da dan hagunce, ama sai ya ji dadinta sosai a ransa har ya gyada kai ya fice din ya dauki kayan abincinsa ya fice bangarensa da su dan shiryawa ya fita wajen aiki, dukkan motsinsa kuwa ita din ce ke masa yawo a kwakwaluwarsa sosai da sosai, yakan yi murmusji ne kawai , ya gaza samun matsayin da zai dora girmamarsa da abin nan ya yi, ya rasa gane me zai ce?

Idan yace din za'a fahimceshi kuwa?, Bakinsa da dumbin magangannu da kuma tarin tambayoyi, ya ga dai ko a kayan marmari wanda ya nuna shi ya fi dadi, to yaya aka yi taste din abinda ya dandana a jiya ya zo masa da tarin abin mamaki?

Malan shi ya san ihun da ya darza , juyewar da idannuwansa suka yi da ace an ji shi da ya shiga ukunsa.........

Kai kawai yake girgizawa ko a office sai ya saki murmurshi, Karshe dai a kan lebensa ya iya ajiye kalmar MATA duniyarsa, dan ya yarda yana kuma cikin yarda, shi da Mace zai iya cewa sai san barka, inama inama..........zuwan ba zai hanna komawa a yau yau ba?

Da babu abinda zai hanna shi iyo har sai karfinsa ya kare..........
........

A bangaren ZAHRAH kuwa barcinta ta sha mai kyau lulube cikin abin rufa har sai da kiraye kirayen sallar azahar ya tasheta ne ta farka
A hankalin ta so ziro kaffafuwanta, sai dai tana motsawa sai ta ji jikinta ba sukar nan ba zafin nan ba azabar nan mai zafi, hakan ya sakata sauke ajiyar zuciya tana dan murza hannayenta a saman cinyarta ra sauka ta nufi bayin Mamah tana ji harta tafiyarta ta ji saukinta sosai
Tana shiga MAMAH ta shigo dakin dauke da abinci, da maganin ta ajiye nata saman table sannan ta dan dakata kasa kasa ta sanar da ita ta kuma tara ruwa mai dumi sosai ta shiga ta jima ciki kafin ta fito, idanma da hali ta yi sau biyu , ga kuma waya nan auntynsu na son yin magana da ita........

Sannan ta sake bata fili, dan harta Auta bata bari ta san tana bangaren ba dan karta dameta da surutu, itama ta bata fili dan ta sake sosai, shiyasama ta sanarwa Luba cewar ta dan yi mata nasiha sosai dan ta saki jikinta ta kuma kula da jikinta sosai, domin ta san bata karu ba tunda ta tsatsareta da kallo a dukan motsinta, wahala ce kawai ta sha ta mamaki, da saukima a irin yadda take tsoron ranar wa y'arta
Hakan kuwa ta yi, kuma ta ji dadin hakan fiye da tunaninta dan saima tace yanzu bata jin komai mai kama da zafi a jikinta, dan haka da karfin jiki ta daura alwallah ta fitowarta ta saka hijabin Mamahnta gabatar da sallarta sannan ta zauna gaban abincin ta tankwashe kafa ta bubude tana jin cikinta tamkar an yi mata sata ne,
Abincin nan ta ci sosai, ta kuma ji dadinsa a harshenta dan kuwa ya yi dadin sannan ta sha maganin nan ta mayar da abincin saman kujera dan bata cinye ba sannan ta koma bakin bed din tana jin tana sin fita falo ko aiki ne ta yi dan kuwa jikinta ya saku sosai ya warware mata sosai.......
Chapter 94 · 0% Book details