← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 110

Sashe 52

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwansa ya zo lumshewa a hankali sai ya rage masu girma ya ringa kallon kannen nasa, kallon da suke masa du sai ya ji wani iri, gaba daya sai ya ji wani iri walahi, a hankali idannuwansa suka sauka a kan hannayensu ita da Rukaya, a jimke hannayensu suke kanta kuwa a hade da kirjin Rukayar ita kuma Rukayar ta zuba masa ido tana kallonsa
A hankali ya idasa lumshe idannuwan nasa ya saki maganar inda muryar Abah ta ci gaba da magana kamar haka
" Sai dai ni da kaina na san rigima ce ba yar karama ba, idan na yi duba da ra'ayi, akida irin ta dan Adam Babana na da nasa shima wa'inda ya tsaya a kansu, su kuma manyan abubuwa ne masu hatsarin dake iya hanna bawa aikata aikin alkhairi, .......ama da zan samu Babanah ka zamo mai gidanta , hakan zai idasa cika min ladana............, Sai kuma maganar matana dan Allah hajia ku basu kular da ta dace, bama irin mahaifiyar Zahra, ki zamo mata yaya ki kuma jajirce ta fitar da miji ta yi aure, kin san damuwarta sai an bita a hankali, shi yasa nake mata uzuri, dan Allah a kula da ita ga yarinta ga kuma halin rayuwa da ta fada kin ji?......., Mu ci gaba da zayano sunnayen dan kowa inada sakon da zan bashi......"
Haka suka ci gaba da fada masa sunna yana barin sako da umartar yiwa Baban gida biyaya har ya gama ya ringa yar dariya ya ce" Allah mai alheri iyalan Docter kennan masha Allah da mu, to kunna jina, idan na dawo zam sanar maku da kaina, zaton in kuwa ban dawo ba wannan din itace muryata, sakona ne wanda na yi da kaina, babu wanda ya doran bindiga a saman kaina , ni na yi niya na fada, idan kun fuskanci son kai ko wani abin ku gafarceni, abinda zan sake fada shine Gidan da muke ciki Baba ne ya gina mana, ya barshi matsayin gida na iyali, na umarceshi ci gana da wanzar da iko dan ya isa da ku,ku kuma ina umartarku ku masa biyaya, idan kun ki ya bi dukkan hanyar da ta dace dan ku saurareshi, dukkan abinda ya dace zai zartar da izinin Allah, Allah ya taya shi riko...
................."
Sanyin da muryar Abah ta yi,da kuma shashekar kukan Mama da na Marshal ya saka ya sake katse wayar ya sada kansa yana jin sabon kukan rashi da suka dora, har suka yi suka gaji dan kansu sannan suka sake fuskantar junna
Mamah ta idasa share hawayenta tana kallonsu
A tausashe ta ce" Bi izinillah ba zaku rasa ci, sha, sutura ba, in sha Allah ba zaku kawo bukata a gagara dubawa ba, ban maku karyar komai zaku samu na rayuwa ba, ama gwargwadon karfin ikona zan kamanta , ba zan gajiya da hidimarku ba tunda ku din ahalina ne, sai dai ku sani ba zamu rayu tamkar tinkiyoyi ba watau ba mai tsawatarwa ba mai tarowa, kun san ko a gidan giya akoy baba , a nanma dole a bi baba a yi masa biyaya, ba zamu yi rayuwar rashin yanci ba, aa, ko daya, ama fa zamu yi ta kwaba da sakawa a hanya, idan ka yi gardama dukkan hanyar da ta dace a bi dan a nuna maka daidai za'a kamanta, babu yan wancen dakin ko yan uba, na fi gane gaba dayanmu abu daya ya yi mu dan a zauna lafiya, Aure auren yayanmu bakwai dake gabanmu zamu ci gaba da shiryawa hakan a tsanake, dukkan abinda kuke bukata ku zo mu zauna mu zanta mu tsaya a mafita guda, idan ranar ta zo nan da sati uku kamar yadda aka karra wata daya a taru a yi a kai kowa dakinsa............, Iyayenku babu ruwanku da tsakaninmu, ko me zaku gani ido ne naku wace ke son zaman lafiya mu zauna, idan kun ga sabanin hankalinku ku bamu waje ku mana fatan shiriya kun fahimceni?" Mama ta karashe a kausashen da ya saka baki daya yaren amsawa shi kuma MARSHAL kawai ya zuba mata ido har ta dasa aya, sannan ya sauke ajiyar zuciya
Amir ya kalla ya masa umarnin su tafi baki dayansu
Tatarawa suka yi kowa ya fita a falon yana zuru zuru na ciki na ciki ba damar amayarwa, ba damar tambaya daga manyansu har kannanunsu, bama irin maganar wannan bare gurbin wa da yayansu, ai da sun shiga uku da zama sai ya gagaresu, idan wannan yarinyar da suka takurawa ta zama wace zasu dawo yiwa biyaya?, Yiwa biyaya mana kowa ya san a yanzu komai nasu na hannun Yayansu, hakan na nufin matarsa tana cikin hurumin dukkan wani motsi nasu?, Kai ina gwarama ya auro koma wacece da wannan banzar!

Ita kuwa, zama suka yi su hudu a saman kujeru, kowa ya yi shiru sunna kalle kalle na ciki na ciki, bama irin Fatima da ta dauki maganar nan kamar saukar almara....ta ajiyeta matsayin tausayinta da Abah yake yi har ya daukota ita wannan marar darajar ya hada da mai daraja irin BABANGIDA, ......in na wannan ba, bata ga hadi ba, dan haka bata dauki abin da mahinmanci ba
Wayarta da ta fara tsuwa ce ta sakata mikewa tana sauke ajiyar zuciya, lokacin da Hasan ke kiranta ne dan ya tambayeta ko ta ci abincin rana?, Dan haka sai ta yi gaba kadan tana dagawa hadi da lumshe idannuwanta ta shiga amsa shi
"Ranar da muka zauna, nace kar a kuma kamanta irin maganar nan, an manta ne aka maimaita ko an daukeni a shashasha ne a gidan nan?" Ya fada a cikin falon a kausashe bayan ya mike daga zaunen da yake ya fuskance su fuskarsa har bari take yi yana kallon Maman Furera da Maman Abul..........

To fah zasu saka shi kyatsawa
Muryarta cen kurya ta ce" Asalamu alaikum wa rahamatullah"
A nutse ya amsa salamarta yana zaunawa da kyai shima sannan a sanyaye ya shiga amsa gaishe shin da take yi sai kuma ya dan katseta ta hanyar fadin" Kin firgitani, na kasa rintsawa, kin kashe waya du na rikice, hankalina a tashe....ina fata kina cikin koshin lafiya ZAHRAH?"
Idannuwanta ta lumshe tana jin wani iri a cen kasan zuciyarta, kai soyaya duniya ce, watau ka samu wanda ya damu da kai kuma babar riba ce
"Kina saka min tsoro idan kika yi shirun nan, sai na rasa launin jan aji irin na mai daraja Fatina ne ko ina cikin damuwa ne?

Kin kuwa san babu abinda ban saka a raina ba jiya?

Baki taba nunan kina son magana da ni mai mahinmanci ba, kuma kika kashe wayar, kin ga har tsoron kar aje cewa aka yi na daina kula ki a gida ne?

Please ki taimakawa mai sonki ki sanar min damuwar kin ji?" Ya fada a sanyaye sosai muryarsa har kamar tana dan rawa, alamu na kwarai fa a damuwar yake
A hankali ta ja numfashi sannan ta bude sansanyar muryarta ta ce" Aa fa, ba wannan, a jiya mamanmu tace zata sanarwa aunty ta sanar maka cewa............, Cewa........." Sai kuma kunya ta sakata hadiye sauran zancen tana jin wani iri a saman harshenta, yaya zata ce masa ance ya fito?

Murmurshi ya yi, a hankali ya ce" An ce na fito ne amaryana?"
Wani irin yar ta ji a cikin kwakwaluwarta , sai kuma ta rufe idannuwanta ruf tana dan murmushin da ya saka shi furya kalmar hamdallah wa ubangijinsa, da zumudi ya ce" Yaushe aka ce na turo?"
Fatima ta bude idannuwanta, kasa kasa ta ce" Zaku yi maganar da aunty Adawiya fa, kafin ku yi maganar ne nake so na sanar maka wani magana mai mahinmancin da ba zan so na sakankance da kai ba tare da ka sani ba......................"
Shiru ya dan dauki wajen, shi yana jira ta ci gaba da maganar ne, ita kuma ta rasa ta inda zata fara
A hankali ya ce" Fatimah?, Fada min mana?"
"Am dama ina so na yi maka magana ne a kan NASABATA......................." FATIMA ta fada a hankali lokaci daya kuma ta kai dubanta wajen kofarta da aka yi bugawa daya a hankali sannan aka shigo da sauri
Ido hudu suka yi da Rukaya dake zarro ido tana dan kallonta da alamu ta yi mata ta katse kiran dan abinda ya kawota gaskiya ba na jira bane
Ido ta dan kikifta, tana jinsa yana faman fadin" Nasabarki?, Kamar yaya Nasabarki?.....,kin san fa ni hausar wani lokacin shige min take yi, ama nasaba nasaba .....to fada min Matana......."
Ido Rukaya ta zubawa wayar, dan ba wani hayaniya a dakin da zai hannata jin maganar da ake fada ta wayar, da yake dakunnansu a sama yake ko dan kukan abin hawa sai mai karfin gaske suke jiyowa bale tagar a rufe kuma ba fanka ce a kunne ba AC ne, sai ya zamto babu wata hayaniya sai ta numfashinsu da suke fitarwa
A hankali Zahra ta ce" Yaya, zan yi kiranka , Mama na min magana"
Jin cewa Mama ke kiranta ya saka shi dakatawa bayan ya jaddada mats cewar yana fa jiranta, yana jiran jin abinda take son sanar masa dan ya dauketa da mahinmanci
Jiki ba karfi ta ajiye wayar tana kallon Rukaya da ta tsareta da ido irin kallon ido cikin idon nan
Rukaya ta ce" Oya ki fada mana ko sai na biki da tambayoyin iya shege ne?"
Idannuwanta ta fan lumshe ta bude ta ce" Aunty, so kike yi sai maganarsa ta shiga jikina na sakankance da shi ya dawo ya gujeni saboda abinda mahaifiyata ta gujeni?"
"Ok ok, kuma sai aka ce za'a tashi a bashi y'a a rufe ne?
Chapter 52 · 0% Book details