← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 110

Sashe 60

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

An gaya maki bawa na tsallake kadarar rayuwarsa ne ko an gaya maki wa'adin da mahaifiyarki ta dauko zata tsallake ne?

Sanadiya ne ba da hannunki ki ka kasheta ba , ba kuma da hannunsa ya kasheta ba, kin tsaya kina munana kalamai a kan wace kika haifa masu tsaurin da ba zan iya dauka ba, me ta maki?

Me ta kashe maki?

Me ta maki a rayuwa ta fi ki daukan dukan janyo fadanki? , Kin tsane ta, kin hantare ta, kin guje ta, kin bita da zagi, yanzu kuma ki bita da irin haka?

Aunty in sha Allah bakin ki ba zai fadata ba tun da babu abin da ta maki!

Ki shake shi idan kina so ki kashe shi ke ta gano amma dan Allah ki shafa mata lafiya hakanan!

Idan ba za ki taba amsarta matsayin y'a ba ki daina aibatata dan ko a tunaninki kin haifeta ba uba kina da karfin da kowacce uwa take da shi a kanta, magangannunki yan amen na amsa kafin ki rufe baki a kanta! ....................!"
Ya rintse idannuwansa yana girgiza kansa , ya rasa yaya zai yi sai ya fada, ya rasa me zai yi dole ya fada.

A hankali ya ci gaba da fadin" Mema take cewa?, Karfin kir ki bata da shi, kina gani take fadawa wani dan iska sirinta dan tashin hankalin da take ciki da ke yana neman haukatata, haba aunty ki dubeta mana, rauni ne da ita mai karfi......, Ki mata addu'a ko da a boye ne mana?

Ita din mai rufe asirinki ce dan kuwa duk irin halin da take ciki har yanzu dai babu wanda ya yi galaba a kanta, Aunty kina cutar da ita, tana shiga tashin hankali mu kuma zuciyarmu na rasa sukuni."
Ya sake ajiye maganar kamar zai ajiye da rada rada, kamar zai ajiye baya so a ji karshen kalamansa, shi dai ya ajiye wani iri yana kuma son dauke dubansa baki daya, ya dan dora da fadin" Allah ne gatanta, Mamah ce Mamanta, ni kuma Yayanta ne, mu muna so, kuma muna tayawa da Addu'ar Allah ya tsare,Abu Docter tashi mu je."
Mamah dake kallonsa, bakinta ya kasa furta komai, tun da ya dakawa Aunty amarya tsawa ita ma aunty Amaryar sai ta yi tsomomo ta sa da kanta tana rike kukan dake tukota har ya kama hannayen Aban Ahmad ya mikar da shi ya ja shi suka fice a falon ne ta iya sakin kukan dake nukurkusarta ta zube a saman cafet ta hafe kanta da gwuiwoyinta tana kukan ta ce" Laifina za'a gani ko ?

Laifina za'a gani yanzu?

Me yasa ba za'a ga laifinsa ba shi azzlalumin, me na masa da zai nemi wulakanta ni a cikin duniya?

Dawowa rayuwata da nufin ko meye wulakantani ne, ya barni na mutu a haka, ya barni na mutu a haka dan ganninsa tashin hankali ne a wajena, ni na san me ya min, ni na san irin rayuwar dana gani sanadiyarsa, yanzu me zai ce min har da za'a nemi gannin laifina?"
A hankali Mama ta zauna daf da ita tana dafa hijabinta tana neman in da hannunta yake ta ce" Ba laifinki ake so a gani ba Nana, so ake yi a tankwonsa harshenki domin idan rai ya baci a lokacin ake iya aikata aikin dana sani in ba'a kwabi harshe ba, kuma kin ga Zahra y'arki ce ta cikinki, yadda kike jin kaunar mahaifiyarki haka take jin kaunarki, yadda mahaifiyarki take taka tsantsan da ke, duk wani abin da zai iya aibataki haka ya dace ki yi, kin ga fa Uwa aka ce fa, uwa ba abin wasa ba Nanah, ki yi hakuri kin ji?"
A hankali kukanta ya ringa yin kasa har ya tsaya,
A hankali ta dago fuskarta ta zuba dubanta a fuskar Mamah
Irin soyayar da ake yiwa mahaifiyarta haka ZAHRA ke yi mata?, Irin yadda Mamanta take kafa kafa da komai da ya shafeta, take sonta tamkar ranta, ko mene ne in dai ita ya shafa to fa tana daukansa da mahimmanci ta masa riko daya tak da ba mahadi?

Takan iya kin ci ta bata, tana dangana da komai ita ta samu?

Irin haka Mamah ke nufi?

A hankali Ta ce" Mamah, ni mamana fa babu abin da take so sama da ni a duniya, ta sha fada min"
Mamah ta kure fuskarta da kallo, irin expression din fuskar nata na son gaskata mata abinda Babangida ya fada, kamar wace take son sannin abin bayan abu ne da ba boyaye ba?

A tausashe Mama ta ce" Ai duk uwa hakane Nanah, duk uwa tana son danta fiye da komai a duniya Nanah"
Aunty amarya ta sa da kanta, cen ta dago ta ce" Mamah ita fa shegiya ce, kuma duk inda na je in dai aka ganni da ita sai a guje ni, a yi ta korata, a yi ta zagina ana ce min karuwa, a yi ta tsangwamata, ko aikatau da na kasa samu dan an ganni da cikinta ne, da na haihuma aka ki bani, ko sadaka ce sai a ki bani , komai fa MAMAH, in na fita ni ka dai sai a bani da ita kuma sai a hanna min, kowa ya tsane ni, kowa ya ki taimaka min, sai docter ne ka dai ya taimakeni."
Sai kuma ta yi shiru a hankali ta fashe da kuka tana dafe kirjinta ta ce" Wayo Allahna Docter, wayo na yi rashin uba, ginshiki, bango, wayo na yi rashin mai tausayina mai jana ya hiranceni , wayo na yi rashin mai min nasiha mai yafe kuruciyata, Mamah da yana nan wannan mutumin ya fito sai ya mare shi kamar yadda ya ce min, ya ce in daina kuka duk ranar da aka ga Mutumin nan sai ya mare shi ko ya sa Babangida ya mare shi, kin ga kamarma abokin Babangidan, kin ji Babangidan ya min tas Mamah bayan ni ban yi komai ba"
Hawaye MAMAH ke sharewa, shi ke nan ta yarda yanzun kam a kai Aunty amarya gannin likita, ta yarda ta amince idan ma akwai ciwo na zuciya abin ya shiga jikinta fiye da tunanin bawa, tamkar wata yar yarinya karama?

Abubuwan sai a hankali.

A sanyaye ta ce" Ki yi hakuri Nanah kin ji?

Ba gamu ba?

Ki yiwa docter addu'a sannan ki yi abin da yake so ki yi, watau ki kula da yarinyarki ki kuma kasance mai yafiya, Kin ga idan so ki ke a mare shi zan mare shi da hannuna kin ji?

Zan kuma masa fada, ama ki yi hakuri ki yafewa Zahranki, kin ga ita ma bata san komai ba, idan kina tune bata zabi ta zo duniya ta haka ba fa Nanah, kin ganta bata da kowa sai ke, idan mutane suna so su
i taimakonki ai Allah ya baki, ki rike abin ki sai ki ga Allah ya baki hanya mai daraja ko Nanah?, Amma idan ki na wulakantata kin ga Allah zai kama ki ne, ya ga dan ya baki jarabawa a duniya kin kasa hakuri ki jure ko?"
Wani irin shiru ta yi tana kallon kasa, cen kuma ta ja numfashi a sace ta ringa kallon hanyar hawa sama, kasa-kasa ta ce" Mamah, ina ma sonta bana so ne ace ni na haifeta"
Mamah sai da ta ji kamar zata fashe da kuka na tausayi, a hankali ta ce" Ba za'a ce ba, ni ce nan na haifeta ke yayarta ce, zaki daina hantararta idan ta ce maki Aunty?"
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta dan gyada kanta, sai kuma ta janye hannayenta a hankali tana mikewa hadi da jan hijabinta, a sanyaye ta ce" Mamah bara na tafi dare na yi"
Mamah ta ce" To shi ke nan Nanah Allah ya saka da alkhairi, ki kula kin ji?

Ban da kukan nan da saka damuwa , idan kuwa kin gaza barcin ki taho nan kawai kin ga muma muna tattara kaura cen bangaren cen sai mu hade mu yi tatta yin aikin tare ko?"
Amsawa ta yi ta fice tana ta faman tunanin magangannun nan na su ita da MAMAH, haka kawai maganar wai yadda mamanta ke sonta ke dawo mata a zuciya, ita fa ta san a cen zuciyarta tana son yarinyar, matsalarta daya ne duk wanda ya ji ga yadda aka haifeta sai ya masu kallon yan iska, dalilin yarinyar nan duk ta fada tashin hankali na rayuwa fa, ai dole ta ki jinnin ko da ganninta ne.

Mamah kam ta jima zaune tana jimami sannan ta dauki waya ta danna kiran MARSHAL tana tambayarsa ina suka shiga ne?

A tausashe ya sanar mata ya kawo Aban Ahmad din an auna shi ga su nan zasu je su amshi magani sai ya ajiye shi gida dan yau matarsa ke sauka tana hanya
Mama ta yi masa fatan samun lafiya ta sake jaddada MARSHAL cewa ya yi ta tausarsa dama zai iya fuskantar haka , ya yi hakuri Allah ya sanyaya, sai ya yi hakuri sosai ko da zai samu nasarar ta saurareshi.
______________________________________
Bayan kwana uku
.
Chapter 60 · 0% Book details