Sashe 25
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yake tambayar kansa a cikin ransa, sai dai bashi da damar yin tambayar a dole ya dan risina yana fadin" gaskiya gwara na je, dan walahi yau in ban rike shi ba ba zan iya kwonciya ba, shi marar mutunci"
Yana fita Mar
chal ya lumshe idannuwansa a hankali sannan ya bude ya juyo inda ta yi wani irin tsuru tsuru bakinta na rawa tana rike furucin dake son fitowa daga cikin bakin nata cewar a yi mata rai kar a yi masa komai, domin shi din rayuwarta ne, sai dai wanzuwar Baban gida ya sakata gane cewar ba wajen wargi bane, dole ta kama kanta jikinta na rawa tana fitar da hawaye wani na korar wani ta sada kanta a ranta tana ayanna dama yayah Amir din ya jibgeta, ko yayane ta san ba zai shaketa ya kasheta ba , ama yayansu ai shi kam ta yiwu shine mai idasa aikata lahirar
A hankali ta sake dagowa ta kallo wajen da yake
Idannuwanta ne suka shiga cikin nasa, a hankali ta sada kanta sai hadiye kukanta take yi tana kalmatushh shahada a zuciyarta
Tsayinsa ya rage sosai bayan ya gama nazartarta da mamakin duka duka wannan zara kai shekara nawa ama wai har take irin haka a kan namiji?
Ya karaso daf da ita sosai ya duka daf da ita ta yadda zata iya jin maganarsa dan ihun da suka masa ya ishe shi haka ba kuma zai iya jurar wani ba
A hankali ya shiga magana kamar haka" Kin san dai babu abu mai girma da ake son kiyayewa irin hawayen mahaifiya ko?"
A zabure ta dago rinanun idannuwanta ta zuba a cikin nasa a karro na biyu, shi kuma ya sake saka nasa masu launin jajajaja kadan a cikin natan ya dora da fadin" koda musulunci bai zo da maganar cewa a kiyaye ni haka kawai nake jin ina son kiyayewa kuma ina son wani ya kiyaye koda baya sonta....bale a tunanina ai mamanki ce kina sonta ko????............"
Wani dunkulalen yawu ta hadiye tana sake son gane wai hausa yake yi ko yaya?
Ko a gaba zai ciro bindiga ya harbeta bayan ya mata nasiha?
"Ko bata haifeki ba tana son ki, kyma Allah na iya kama ki a kan haka ko?" Ya fada a dan dake yana dan fito da idannuwansa a kanta, a dole ta ringa gyada kan tamkar yar kadangaruwa
Ya sake dan dakatarwa , kasa kasa sosai ya ce" Ke din bakya jin magana kwata kwata......., ita kuma tana son ki a haka....., Sai na rasa shin na dauke ki na watsar da ke jeji ta yadda zata daina shiga damuwa saboda ke ko na ci gaba da kallonki kina kokarin saka mai son ki hawaye??????"
Ya ajiye tambayar a tausashe yana zubawa fuskarta ido, duba irin na tsanakin nan, duba irin na sosai din nan sai ya zamto itace wannan karron ta sada kanta gabanta na faduwa, hankalinta na matukar neman tashi bakinta na dan bari ta ce" Dan Allah babanmu kar ka watsar da ni ka ji?"
Idannuwansa yake dan lumshewa ganni yana kallon gashin kanta dake kwonce lumbuk a gaban goshinta, kasa kasa ya ce" To zan yi nazari...., Ama da sharadi....."
Da sauri ta sake dagowa dan jin sharadin
Shi kuma ya ce" Kina son sa ai ko?"
A hankali ta sada kanta
Hakan ya saka shi fadin" Kin ga kar ki yi wani munafurci, kina son sa?"
Kai ta gyada tana kallonsa, shi kuma ya tsura mata ido kadan, a hankali ya ce" Kinma san menene so din?"
Da mamaki take kallon Yayan nasu, ita?
Ita din nan ai malamar soyaya ce, gaskiya tana ba soyaya mahinmanci....kai ai ita da so amana ce da amana, sai dai ba zata sanar masa haka ba, hasalima jira take a kai wajen da zai harbeta sai ta ji yana cewa
" Zan aura maki shi ku tafi, kafin nan ki yi kokarin nunawa wace ke sonki soyaya ta hanyar kare mutuncin kanki, ki kare mutuncinta da kuma namu mu y'an uwanki..... sannan ki kiyaye dukkan abinda zai taba lafiyar jikinki, kin ji?
Ai dukan bashi da anfani ko?"
A karro na uku ta sake dagowa ta zubawa sajen dake kwonce a gefen fuskarsa ido, hawayenta bai daina zuba ba, tana ta faman murzar yan yatsunta tamkar tana cire fatar dake jiki, ta kasa bashi amsa har sai da ya dauke idannuwansa daga saman jajayen lebunnanta ya ce"
15 ....*5s*
Ta kasa budar baki ta bashi amsa, dan abin ya zo mata wani iri, har sai da ya kawar da dubansa daga saman jajayan lebunnanta ya ce" Ki buda baki ki yi magana mana"
Muryarta na rawa ta budi baki tana kame kame ta rasa me zata bada amsa har sai da ya sake kureta da kallo ta fashe da kuka tana girgiza kanta ta sada kanta ta ce" Dan Allah, dan Allah Babanmu ka rufa min asiri kar ka zane ni na summa dan Allah, ka yafe min sannan ka fadawa mamana ta yafe min dan Allah, ba zan kuma ba ka ji babanmu?"
Baki ya dan tabe yana kallonta, ya girgiza kansa ya ce" Ni ba dukanki zan yi ba, so nake ki yi kokari ki kamanta adalci a rayuwarki kin ji?"
Gaba daya sai take neman bacewa a cikin tunanin fasarar mutumen da take tunanin tana daya daga cikin wa'inda idan ance masu wanene shi zasu kire shi da dodo mugu mai duka a mutu, ga kuma wanda ke gefenta yana yi mata magana a yanzu.....tamkar ba shi ba
Sanyi a muryarsa, hakuri a muryarsa da sauransu, wane zata dauka ne a cikin mugu da nutsetsen bawa irin wannan?
A hankali ta sake zuba masa ido, a sanyaye ta ce" In sha Allah, daga yau ba zan kuma kamanta irin haka ba Babanmu"
Sake kallonta ya yi da mamaki, to shi a ina ya zama babansu kuma?
Kai da ya tara ya'ya, ya'yan gidan Docter ai duniya guda ne Masha Allah, mikewa ya yi ya dauki Hijabinta ya ajiye mata a gefe ya yi waje yana tunanin wai kar ya doketa, to ita wannan in ba saka bawa a uku ba ina shi ina dukkanta?
Jiki du kamar na dan jariri daga an tabata ta kumbure wannan dan shafa ta Amir du ta dauki ja kamar an kuncin mai beating ina aka hada da dukansa?
Kokari zai yi ya hade daurin aurenta da na yan uwanta a yi a huta tun kafin ta janyo masu magana, fatansa yaron ya zamto na kirki, dan baya tunanin zai dauki y'a ya ba sakarai ba
Da gagawa ta mayar da hijabinta sannan ta mike ta nufi sama gabanta na faduwa har ta karasa kofar Mamah ta tsaya ta rasa shin shiga zata yi ko baya zata koma?
Hankalinta gaba daya a tashe j
ikinta sai bari yake yi
Gwauron numfashi ya sauke bayan ya rakata da ido yana son gane ita kuma me take nema a wajen d'a namiji da har zata hada kaya ta bi shi?
Yarinta ce ko wauta ko kuma dadin namijin ta sani a kannanun shekarunta bata san wahalarsa ba? kai ya sake girgizawa a lokacin da ta gama hayewa sai kuma ya juya a nutse ya nufi wajen ABAH, dan yana son ganawa da shi kafin ya koma gida, ba zai ga yaron ba sai an gama binciko masa waye shi in sha Allah, a lokacin ne zai san ta inda zai bilowa lamarin
__________________________________
Tunda Mamah ta amsa salamarta ta shigo ta tsuguna daf da kafarta ta sada kai take kuka bata iya dagowa ta dubeta ba, har sai da Maman ta gaji a hasale ta ce" ke saurara min haka kin ji, bana son munafurci da rainin hankali, tashi ki je ki samu waje ki yi kukan iya kuka dan ni bana son rainin wayo, ke yanzu Fatima har kece zaki dauki jaka ki zuba kaya ki bi Namiji?
Me kuke tunani a lamarin namiji ne?
Me ya fada maki da ya saka kika yarda cewa ya fi mu a wajenki?
To bari ki ji in fada maki, a yanzu maza sun garwaya ne sun cakule cikin na kirki da na banza, zan iya ce maki na banzan na iya aikata aikin na kirkin idan har ya fito ta hanyar lalatar kika nuna masa ke ta kirki ce bakya ciki da maganar banza, haka kuma na kirkin na iya aikata aikin lalatar idan ya ga ke din banza ce zaki iya sadaukar da mutuncinki kan shirmaman abin da kike kira so!, Wai in ba lalacewar zamani ba uban me ya ha
a budurwa da ba namiji fuskar kawo mata lalata?
Sai dai a yanzu wata budurwar ta dame magidanciyar ta shanye dan fitina da rashin sannin ciwon kai da rashin kunya da rashin jin tsoron Allah da rashin jin tausayin iyaye, ke yanzu Zahra menene dadinki da kato da har zaki tashi ki bi shi ?
So kike yi ki san asalin waye d'a namiji ne tunda kannanun shekarunki?
Kin kama mutuncin kanki kin rikema yaya kika kare da namiji bale kin nuna masa ke shashasha ce baki da wata daraja har zaki iya binsa yawon duniya?
Me kike tunani ga wanda zai iya ce maki zai dauke ki ki bijirewa iyayenki?