Sashe 102
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nufinta a maganarta shine, zuwa yanzu tana fama da jin haushi na kiraye kirayen wayarsa da ake yi ba lokaci, da safe ne, da rana ne, ko da dare ne
Eh lalle ta sani bai taba dauka ya yi kiran da kansa ba, ama kuma ba zata boye ba idan an kira zai dauka kuma zai ambaci sunna ya kuma saurara, wannan lamari ya sakata a jiya yin kiran aunty Luba ta dan bata maganar a shara shanye ita kuma ta dorata a kan hanyar da take son fahimtar idan har zai iya damuwa in an biyo ta nan ko ba zai iya ba, domin ta sanar mata tun yanzu take da damar katse wannan bahaguwar rayuwar, namiji dama an san ba na mace daya bane ama kuma idan kana nawa bangaren sunnanka nawa sai dai ka yi hakuri, hakan ya sa a yau da suke juma'a tunfa ya farka ta kula da shi ya kai matakin karshe a bukatar sake ziyartar daular da take tasa, wace idan har wasa ya yi tsayi tsakaninsu har harshensa ya kai nan sai fa yan yatsunsa sun kai dan ya gane zata iya ko ya kara bata lokaci?
Hakan ce a jiyan nan da kyar ya iya sama mata lafiya ama bakinsa ya sanar mata yana daf da gazawa in har bai je ba,
Kayan kari yake diba a hankali yana sababin binta da duba har nataciyar wayar ta dauki kuka
Kafin ya dauka ya ga ta fara mika hannunta ta dauko, sai kuma ya ga ta zubawa sunnan dake sama ido kamar wace take son gane hausa ce, turanci ne, ko larabci ne kafin ta miko masa wayar da wani kallon da zai iya fadin harare ne sak yar nan ta maka masa sannan ta mike ta ajiye plate dinta mai dauke da romon miya mai dandano ta yi kicin bayan babu abinda suka manta a kicin din ko zata dauko masa
Wayar ya latsa ya amsa yana kallon hanyar kicin din, har ya gama amsawar ya katse ya dake zubawa hanyar ido ama shiru kake ji ba ita ba labarinta, hakan ya saka shi dan duban wayar ya sake dagowa ya kalli kicin din yana neman son sannin me hakan yake nufi RHISA ya yi kiransa
A hankali ya daga wayar ya karra a kunnensa , Rhissan ke sanar masa zuwan nasu fa yana nan zasu fito su kawo masu ziyara ya sanarwa masu tsaron kofarsa......hakan ya saka shi amsa shi sannan ya mikr ya ........
A dole ya mike ya nufi wajen kicin din da wayar ya amsa shi sannan ya kashe
Shiga ya yi gaba dayansa, ya sameta tana wanke wanken da bai san lokacin da aka tara kwanonin ba
Kwanonin ya bi da kallo, sannan ya sake duban fuskarta ya ga ko dago kaima ZAHRAh fatinsa mai sanyi hali mai lafiya bata yi ba bale ta kalle shi
Dan gyaran murya ya yi yana kallonta, hakan ya saka ba tare da ta juyo ta kalle shi ido cikin ido ba ta juya ta je ta dauko masa madara a cikin frij bayan ta ajiye a cen dinma fa kuma ta sani sarai fa ko?
Ta karaso ta miko hankalinta na nuni da wanke wanke take yi, bayan a sanninsa ba wanke wanke ba ko menene take yi ifan ya yi tsaye a gabanta takan dago ta zubawa fuskarsa ido har ta fahimci abinda yake da bukata
A hankali sosai ya ce " Dama, su Rhisa ne suka ce gasunnan zuwa shi da matarsa, ko zaki taimaka ki sako hijab?"
Kai ta gyada , ta karasa wajen pampo ta kashe ruwan wanke wanken , dama ba wasu kwanoni masu dati bane ta kwaso, kawai gudun ta zauna ta kula shi ne ya sakata tsirarar hakan, ta mayar da plate plate din sannan ta zo ta ratseshi ta fice a kicin din ta je ta kwashe kayan karin ta kai saman table ta jera ta sake kawata wajen du yana tsaye yana binta da kallo ta sake dawowa ta shiga haurawa sama ta barshi tsaye cike da matsanancin mamakin yannayinta......, Tambayar kansa yake yi menene?
Me ya faru?
Me akai mata?, Sai kawai ya samu kansa da ba kansa amsar babu abinda akai mata ta yiwu wani abin ta tuna, dan a kwanakin sau biyu tana irin haka ama idan ya dauko mata maganar mahaifiyarta, wace aka ce karshen watan nan zata samu salama daga likita sai dai su ringa zuwa sunna gannin likitan du karshen wata sunna dawowa, ya kula sau biyu idan ya dauko maganar sai ta yi dif ta dauke wuta ta yi shiru har sai ya gama maganar ya dauko wata ko sa ci gaba da zantawa
Tuna haka ya saka shi dan sauke ajiyar zuciya ya nufi saman shima
Yana shiga ya sanar idan su Rhisa sun karaso a rako su har bangarensa sannan ya fada wanka
Itama tana shiga ba hijab din da akace ta saka ta nufa ba, hasalima bayi ta shige ta yi wanka abinta ta fito ta zauna gaban mirroir ta kimtsa kanta a yar madaidaiciyar kwaliyar fuska sannan ta tufke gashin kanta ta mike ta karasa ta ciro atampa sket da riga dinkin zamani daidai da jiki
Kafin ta gama shirin tana ankare da blu din fitilar dake nuni idan an bude baban kofar falo ta haska sau biyu, hakan ya mata nunin bakinsu sun karaso kennan, dan haka ta idasa hanzartawa ta makala dan kunne sirara sannan ta dauki dan yololon mayafi ta yafa a saman kanta ta saka takalmi kafa ciki karami mai dan tudu fari kal wanda ya hau da shigarta sai turare da ta maka sannan ta rufo dakin nata a lokacin da ya juya da niyar haurawa dan sanar mata bakin sun karaso sai ya dakata jin rufowar dakin nata duda ky din da ya ji ta murda ya dan bashi mamaki, ama sai ya share kawai ya koma ya zauna inda RHISA ke zaune yana ta aukin binshi da kallo yana girgiza kaffafuwa yana sakar masa murmushi
Matar RHISA ta sake gaisar da Marshal, da yar yarsu mai shekara uku sai duguitunta take gaban MARSHAL din shi kuwa sai kallonta yake yana murmushi yarinyar ta sha yar rigarta da ribom masha Allah tsaf tsaf da ita ga wayo Mamanta kuwa da wani tsohon cikin ne a jikinta tana murmushin itama dan bata yi tunanin ogan na RHISA yana da tarban baki haka ba
Saukowar ZAHRAh ya saka su dukansu kallonta
Da mamaki ya zuba mata ido, a lokacin da ta saki wani irin mahaukacin rikitacen murmushi wanda ya kwata ilahirin fuskarta ya haskakata ta nufi matar RHISA ta amshi hannunta da ta miko mata sannan ta karasa inda ya saki daga bakin har hancin yana kallonta kamar idan akace masa kek zai iya sumewa dan kamar numfashinsa ta baki yake ja yana kallonta har dai ta dan duko sosai kusa da shi tana yiwa y'ar wasa wace sam bata da kiywa ta ringa bangalar mata da daria tana karawa ita kuwa hakan ya birgeta ta sungumi yarinyar a jikinta sannan ta sake kallon Matar RHISA ta kuma juya wajen RHISA ta dan rage tsayi tana gaishe shi a mutunce da kula kafin ta nufi wajen kicin da yar tana fadin" Sorry fa, bara na kawo ruwa"
Da idon dai ya rakata har ta idasa hayewa inda Matar RHISA ta ciciba tana fadin" Aa madame bara na kamo maki wannan makaletan tunda ta dirw kanki ai da wahala ta barki ki dauko ruwanma....."
Ta bi bayan ZAHRAh, hakan ya saka RHISA dan matsowa kasa kasa ya tankwali MARSHAL da har yanzu bai dawo duniyar mutane ba , shi a sumen ba, shi ba a farke ba yana kallon hanyar cike da tashin hankalin da yake ji daga cen cen kasan zuciyarsa
Ido cikin ido suka kalli junna shi da RHISA, RHISA ya dage gira daya yana kallonsa kasa kasa ya ce" Abokina wannan kallon fa kamar wanda aka fara baka tsome kana yi bayan na san hakan ba aikinka bane?, Ka ringa dauke kai a kan mata in ba haka ba sai a haukataka mana haba namiji sarai ta gane ita kake kallo fa harta madame sai da ta yada harara irin in kalli yadda ake kallon mata din nan bata san ni idan ta bada baya har dukawa nake na hango dan kampan ba.......
Ama a gabanta dole in ringa basarwa mana lokaci zuwa lokaci kar ta yi tunanin ta fa riga ta gama da maza"
Dif ya yi sakamakon dawowarsu , sai dai kallon da MARSHAL ya zuba masa a zabure dole ya saka shi sake rage murya sosai ya dan ringa nuni kamar yana masa hirar da ta shafe su ne ya ce" Ka sanar min kuwa in ka riga ka gane abinfa muke nuna maka, watau menene Mata sai na fara doraka a kan darusan zama da irinsu, dan ka gansun nan?