← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 110

Sashe 63

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wankan ya yi tamkar mai mace a gefe, yana cike da takaicin hakan ya fito ya gabatar da sallar da ta wuce shi wai yana barcin asara harda aikata aikin ba daidai ba a barcin
Bayan ya gama direct wajen suturarsa ya zarce ya bude ya janyo wani lalausan bakin yadi ya jefa saman bed hadi da belt da dai sauran kayan shiryawa na maza
Shiryawa ya yi cikin yadin yana dan daga hannun rigar yana bi da kallo dan sai ya ji kamar ya rike shi sosai , ama kuma ba kadan bane ya masa kawai dai dan rike shin ne ya yi
Kansa ya caje dan ba hula zai saka ba sannan ya dauki waya daya bayan ya yiwa kansa wanka da turare ya fito ya rufe bangaren nasa ya ba mai gyarawa ya wuce a kafarsa ya fita ya nufi gidan Aban Ahmad hannunsa daya a aljihunsa daya a dan jimke yana bin bishiyoyin gidan da kallo yana jin nutsuwa a jikinsa da rashin nauyin mara, wanda hakan ya dan rike masa ciki a dazu
Direct falonsa ya nufa, yana ka kofar zai bude ya ringa jiyo murya kasa kasa da kuka kuka hakan ya saka shi budewar dan ba kukan abinda bai dace ace ya bude bane gabansa na faduwa dan tashi daya tunanin lafiyar Aban Ahmad din ya fado masa
Da kallo ya bi matarsa dake zaune tana kuka, itama jin an bude din ta dago dan gannin ko waye
Gannin MARSHAL ya sakata mikewa tana share hawayenta ta ce" Gwara da ka zo idannuwanka su gane maka, ka ga Aban docter tun abincin jiya da na kireka bai sake cin komai ba, ga abinci nan na dafa na safe na rana na yanzu ko kallo, shayi kawai yake sha sai sauke ajiyar zuciya yake yi , duba ka ga kaffafuwansa yadda suke sundumewa hakan na nufin cutarsa gaba take yi ba baya ba, in sonta yake yi ya je ya aurota ya kawota kusa da shi mana, zai tsaya yana min kisan mumuke ni ban ji dadinsa ba wani bai ji ba, ba zan iya hakura ya halakani dan kawai ya samu matsala da ita ba, ya dace ya duba ya'yansa in ni sunnana mace wace aka aura ake iya banzatarwa, tunda na zo garin nan bani da wani anfani a wajenshi sai samun bacin rai, ba zan iya zuba masa ido a haka ba in ba zata yafe ba ai shikenan ya wuce mu koma saudiya a duba lafiyarsa dan ni yana da daraja a wajena!

Daga haka ta wuce dakinta tana sake tare kukanta, su kuwa gaba dayansu da ido suka rakata har ta mako kofar sai kuma aka yi katari sun kalli junna
Bai ce komai ba ya karaso ya zauna ya bude abincin yana dubawa, abincin kuwa da zafi ba laifin dan haka sai ya dauki plate ya zubawa kansa sannan ya zuba masa shima ya saka masa cokali ya ajiye masa ya dauki nasa ya fara ci hankali kwonce dan yinwar yake ji sosaima kuma dai ya san maman Ahmad ai ta iya girki
Du idan ya debi a cokali ya nufi bakinsa sai Aban Ahmad ya raka shi da kallo, har dai ya gama shaka ya ce" Yanzu ba zaka yi maganar rashin kunyar da matar cen ta yi mana ba zaka zauna ka ci abincinta?

Kana kallo ta mana rashin kunya ta shige ciki ba zaka taka mata birki ba?"
Baki ya tabe ya sake bude salak ya sake lodawa a saman abincinsa yana kallo ya yi dan murmushi ya ce" Ai gaskiya ta fada"
Da mamaki ya kafe shi da ido ya ce"" Gaskiya kuma?"
Ido ya daga yana kallonsa ya ce" Eh gaskiya, to kai in banda abinka mutuwa ai ba sai ka kai kanka ba Aban Abanah, mutuwar nan fa jira take lokaci ya yi kai da kanka sai ka laluba ka ganka gaka ga ita, me kake gagawa kana wani hanna kanka cin abinci?

Kashe kanka kake son yi ne?

In kashe kanka kake son yi kuma akoy bindiga a daki ka je ka dauka sai ka yi mai sauri dan shinkafar bera likita na iya cetoka in aka ganka da wuri"
"Yanzu me na maka ni kuma?

Me yasa zaku ringa jin haushina?" Aban Ahmad ya fada a raunane yana sake kallon MARSHAL
MARSHAL ya ajiye abincinsa ba fan ya koshi ba, da takaici ya ce" saurara ka ji, idan sonta kake kamar yadda matarka ta fada sai fa ka mike a kan kafafuwanka ka je ka sha wahala iya wahala kafin ta dubeka, dan gaskiya na kula tana da fushi, in kuwa yafiyar kawai ta wadatar itama sai ka nema sosai da sosai dan bana tunanin zata iya yafewa da wuri, ba kuma wanda zai maka wannan yakin, mu yanzu abubuwan gabanmuma da yawa nawa ka dan murmuje ka dubi matarka , mace na sonka tana maka kuka kana son bayar da maza, gaskiya ka dan duba halinka wannan sam ba hali bane, to kai in banda abinka in ka mutu baka karra auren ba wane aka yi kennan?"
Gaban goshinsa ya dafe, zuciyarsa na dokawa, shi fa da zasu saurareshi tsoronta yake ji fa, har ga Allah da ta fadi magangannun nan tsoronta yake ji sosai har cikin zuciyarsa
A sanyaye ya ce
A sanyaye ya ce" Ina yin iya kokarina fa MARSHAL, jiki idan ya tabu ai sai a hankali ko?

Kuma ita fa wancen kishinta ne kawai da ba zata iya tankwasawa ba, ita dai kawai in dai maganar mace ne yanzu zaka ga ta rikice, bale sosia take rike da kishin maman fati ban san dalili ba"
Marshal ya yi murmushi ya ce" To ai ta san kana sonta ne kaima ka wani zauna kana neman rikicewa saboda mace, kuma dole ai ta yi kishinta, du inda ka zauna zancenka kennan fa"
Da mamaki ya ce" Kai fa MARSHAL kuma koda yaushe?"
MARSHAL ya gyada kai yana sake daukan abincinsa ya ci gaba da ci, da idannuwansa ya masa alamar ya ci mana shima
Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki abincin shima ya shiga ci, duda ba wai dadinsa yake ji ba, ama da MARSHAL din ya yi magangannun nan har ga Allah sai ya ji wani iri, gwara kam ya cin tun kafin a totse shi da ransa
Ajiye plate din ya yi ya dauki jus din dake ajiye na aya sai abin raba yake ya dan zuba masa ido, haka kawai ya shiga tunanin anya ya dace ya sha wannan abun kuwa?, Ajiye ya yi yana daure fuska harda hararan jug din ya dauki ruwa ya sha sannan ya dake gyara zamansa yana jin nutsuwa na ratsa shi
Kamar wanda yake wani tunani ya ce" Wai ka san me Mamah ke so?"
Aban Ahmad ya girgiza kai dan bakinsa ya dauki abinci
Marshal ya sake kallon gefe yana jin takaicin maganar a ransa, Fisabililahi bai san bama da wa zai tatauna maganar, kuma so yake ya samu kwarin gwuiwar kin yin maganar dan haka yake ji a ransa ai ba sai an fadi zancen ba in dai auren ne ake son yi mata, bama wannan ba yaren kwata kwata nawa suke ne jama'a?

Da takaicin maganar , dan a
duniya babu da wanda yake zance hankali Kwonce kai sake, kansa tsaye irin da ABAN AHMAD, zance suke yi harda na mamaki, dan sunna yi sunna shan dariya har su cafe hannu idan abin ya masu dadi, kusan maganarsu na zuwa daya shi yasa suke gannewa junna
Da takaici ya ce" "Ka ji Mama wai za a zauna da manemin auren Zahra, ni abin da ma ban gane ba shine, ita yarinyar nan nawa take ne?

A matse a ke da tayi aure ne?

Shi me ma ya gani a jikin
aramar yarinya ne wai?

Ni fa irin lalacin nan ne bana so, haba."
arashe da kawar da kai da kuma ha
anin gaskiyar abinda yake fa
a iya gaskiyarsa kenan, Abban Ahmad kallonshi yake yanna dan tunnanin maganar
Ajiye abincin ya yi dan ya ishe shi ya dauki jus din ya mauda iya shansa ya ajiye yana fadin" To menene a ciki?

Ai hakan ya dace a yi dan kar yarinyar tala ta hadu da wasu fitintinnun ko?

Ai in za'a zauna dinma ni a zauna da ni sai mu bashi hakuri a nuna ni nine ubanta ya yi hakuri ya rike mana da amana ko?

Kuma da kake cewa yarinya ai Zahra kam ta girma masha Allah shekara ta ashirin fa MARSHAL"
"Dan Allah in tambayeka mana?" MARSHAL ya kaste shi wani haushi na tuko shi
Aban Ahmad ya ce" ina sauraro"
MARSHAL ya ce" Hala likita ya maka allura a cikin kanka ne?"
Aban Ahmad ya dan dage girarakinsa da alamun son karon haske
Marshal ya dauki jug din ayar ya bude ya cika kofin kwalba ya sha, dan kuwa yanzu gani yake ai kowace wace kawai
Da haushi haushi ya ce" Dan muna sakarkaru, dan ya ajiye mu, dan mune bamu da daraja bamu san ciwon kawunnanmu ba, zamu bashi mutun kuma mu bi shi da magiya?
Chapter 63 · 0% Book details