← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 110

Sashe 84

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uhum ke dai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya Luba"
Luba ta amsa da amen jiki ba karfi itama, Auta kuwa da ta je bangaren Mutuniyarta kilewa suka yi suka wuni sunna shashancinsu, tare suka ringa zagayen bangaren sunna gannin dukkan abinda aka zuba kafin su yada zango gaban TV su jona da wayar ZAHRA su shiga kallo dan Aunty luba harda su fina finan hausa ta zuba mata dan debe kewa, duda ta ringa jin jikinta wani iri, sai ta dauka ko al'adarta ke hanya dan mararta ta yi mata nauyi duda ba lokacin yin bane, ama kuma al'adarta kawai ke hadasa mata haka, da Auta kuwa ta zo sai ta jure kawai ta basar suka shiga washale wale dinsu
_____________________________________
A gidan su Hasan
Baban Hasan din ne ke fada, fada ba da karfi da hargagi ba, aa, fada ne yake yi dan so yake yi ya tankwasa dan nasa da kuma mahaifiyarsa a irin wannan lokacin da Hajia baba yayarsa ke zaune da y'arta wace ke kuka kanta a saman cinyarta har tana jan hanci
Mahaifiyar Hasan ta dan cije bakinta a nutse ta ce" Elhaji, maganar fa ta riga ta wuce ai, Hasan ai yanzu yarinyar ta haramta gareshi tunda an daura mata aure yau kwana biyu cif, kennan kawai a bashi dama dai ya je hankali kwonce ya kawo wata idan ta yin ita sai a aura masa, idan ita dinma bata yi ba sai a sake bincikawa, shi dai cewa ya yi baya son Hamdiya ne, a yi kokari a yi hakuri kawai"
Hajia Baba na kada kafa ta ce" Kennan yau har mun zo lokaci, ko nace zamanin da zamu zoma y'ayanmu da magana su nuna bamu isa ba?"
Elhajin ya kalli Hamdiyar ya ce" Hamda ki yi shiru mana kukan haka, ai zai yi hakuri a yi auren kin ji?"
Hasan dale murmushi yana gyada kansa ya ce" Abah, ai ba kukan nace bana aurenta ta fashe da shi ba, kukan ta ji wa aka aurawa wace suka je suka wulakanta take yi, kukan son MARSHAL take yi, bata san MARSHAL ko bai auri Zahra ba ya fi karfinta saboda ko a ranar da suka hadu da shi har suka baza hali ai Sa'a suka ci a gaban mahaifiyarsa ne har suka yi suka gama suka tafi, gwara ki yi hakuri yarinya ki nemi wani, dan na rantse da Allah ni a kankin kaina ba zan aureki ba, ba ke ba ko wata cikin dangi na haramta sai dai na karaci rayuwata a haka, in kuwa aura min za'a yi to ba damuwa a auran!"
Daga haka ya mike ya yi tafiyarsa cikin dakinsa, Mahaifinsa tamkar idannuwansa zasu fito su fado dan al'ajabin wannan lamari
Hasbunnalah, yanzu Hasan dinsa da baya cewa komai ne ya yi irin wannan rashin kunyar, subahanalah, subahanalah subahanalah ga mahaifiyarsa tamkar bata ji me yace ba, ta yiwu da daurin kugunta a lamarin nan, hakan ya sa ya dubeta ya ce" Yanzu kina kallo yaron nan zai yi mana rashin kunya kika kyale shi?"
Gaban goshinta ta dafe da yake sara mata, har ga Allah itama ta tsorata da rashin kunyar nan da ya yi kuma sai ta tarda shi ta wankeshi tassss, ama maganar a aura masa yar dangi zabin hajia walahi ba zai yiwu ba, koda kuwa sakinta ubansa zai yi ta shirya, rashin mutuncin ya isa hakanan, mulkin malakar ya isa hakanan, an jima ba'a yadasu cewar sun yiwa hajia rashin kunya ba,
A tausashe tana mikewa ta ce" Allah ya baku hakuri"
Daga haka ta yi tafiyarta ciki
Hajia Baba rai bace ta dago y'arta ta
Hajia Baba rai bace ta dago y'arta ta wanka mata mari ta kwashi fada tana fadin" Idan baki kama min bakinki ba zan tatakaki a gidan nan, Hamda ni kika wulakanta ko?

Ni kika saka har dana ya fada min magana ko?

Ashe katse maki maganar MARSHAL da na yi baki barta ba?, To kuwa sai dai ki yi abinda zaki yi dan kema kin san abu ne da ba zai yiwu ba, kuma kin ga Hasan ko?

Hasanma ba zaki sameshi ba dan walahi na rantse maki ni da na shiga harkar auren yayan Baraka sai dai in ana yi a kiyama, tashi mu tafi shashashar banza da wofi!"
Sosai Hankalin Elhaji ya tashi ya ringa bata hakuri yana rarashi har ta je motarta ta shige yana ta bata hakuri shi dai suka tayar suka tafi, hakan ya sa ya koma rai bace ya rufe maman Hasan da fada, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya yi mata sumul da fadace fadacen ba zata shiga tsakaninsa da danginsa ba, ita kuma kanta a kasa har ya gama ta dago tana share hawayenta a nutsenta dai ta ce" Ba damuwa, in sha Allah du yadda ka yanke ina maraba da shi, ama tunda aka yi cin zarafin nan ina tsaye kan kafata kan ba zaka aurawa yarona yaronta ba, inace nima ita ta min miji?

Ko me zata ce ta ce, mulkin malaka ya tsaya a kaina ama ba zai haura kan yarona kwalin kwal da ransa ba, idan me za'a ce aje a ce a dangin a shirye nake tsaf dan babanmuma ya sani ya kuma yarda ko sakin nawa ka yi na je gidan, tunda ai ita ke rike da igiyar aurenmu baki daya tana iya sakinmu yanzu ta yi niya, Hajia dai ba mahaifiyarka bace yayarka ce, biyaya ta gidan duniya muna kwatantawa, idan tura ce ta kai bango kai ko mu kuma Alhamdulilah haka Allah ya so, ai an zauna shekara da shekaru"
Daga haka ta tafiyarta dakinta ta maka ky ta barshi tsaye tamkar wanda ya summa da mamaki da tsoron furucinta, tunda suke ko sa'in'sa basu taba yi da ita ba, hadasu aka yi aure ama a hankali ta gama mamaye dukkan wani sashi na duniyarsa, mace ce da ta san darajar kanta ta san darajar wanda take tare da shi, bata cika kwaramniya ba ta kasance mai hakuri da rungumar dukkan wani abinda ya nufota da danga
na da addu'a, kafma cikin matan yan uwa babu wace ake jinjinawa irinta dan itace ba'a taba jinta da hajiar ba, yau aka yi haka sai ya kasa binta ya zauna ya dafe habarsa ya shiga tunani, shi a kusa kusan nan abinda zai raba aurensa da matarsa ai ba dai hajia da rikicinta ba walahi, in ya saki marar rufin asirinsa uwar dansa mai sonsa domin Allah wa zai samu?

Haihuwar nan tasa ce ta lalace sanadiyar accident da ya yi , wace zata juri zama ba haihuwa a kusa kusan nan?, Kai baya ciki, ba da shi ba gaskiya, zai hada mtng na ahalinsu ya sanar masu shine ya yanke hukuncin nan Allah ya ba kowa hakuri, yarinyama bata so shima haka dan haka a bar maganar kawai kowa Allah ya bashi daidai da burinsa!"
____________________________________
A daren da Marshal ya dawo direct wajen MAMAH ya fara sauka da niyar idan ya ci abinci sai kawai ya je ya kwonta, sai dai yana zuwa ta sanar masa ai abincinsa yana bangarensa,
Ya dan zauna dai sunna dan zantawa Mamah cikin hikima kadan ta yi dan murmushi ta ce" Baban Docter, nace baka samu ka je gidajen kannen naka ka masu nasiha ba ko?"
Marshal ya ce" Eh MAMAH, in sha Allah ina so sai sun kwana biyu sannan"
Mamah ta yi dan murmushi tana gyada kanta , ta ce" Hakane, a yi kokari idan suka kwana biyun a je, ka san yara sai da nasiha , a kwatanta masu sosai hakin dake kansu yanzu, ko yayane suka yi wasa da shi Allah na iya kama su da shi, a cikinsu kar wace ta yarda ta yi wasa da damarta, ko wa take aure dai sunnansa mijinta shi kuwa sunnanta matarsa, du wanda ya dane hakin wani ko menene kuwa shi da Allah ne, Hakkin aure girma ne da shi da daraja, idan har bawa ya ringa takewa dan wani dalili nasa ko menene yana kona kansa ne ba tare da ya sani ba, Allah dai ya basu zaman lafiya baki daya"
Shi dai ya amsa, ama maganar haki kuma sai ya ringa jin maganar kamar ba da su kadai ake ba?

Komai kankantar abin da mama tace ya dn tsaye masa a Rai, hakin mace da hakin namiji ai yawa ne da su a rayuwa, haka dai suka dan yi hirarsu sannan ya mike ya tafi
Yana zuwa bangaren nasu ya ci abincinsa ya yi nakkkkk sannan ya haye sama dan dare ya yi sosai y shiga gabatar da dukkan abinda ya saba kafin ya yi barci
Har ya zo da nufin kwonci ya fasa ya mike ya nufi dakinta
Hannunsa daya a jimke a bayansa, daya ya bude kofar da shi ya dan leka kadan yana nazarin barci ta yi ne ta kashe fitila ?

Gannin fitila a kashe ya saka shi janyo kofar ya rufe ya sake komawa nasa dakin ya kwonta yana dan jan numfashi a hankali ya kai hannunsa sashen jikinsa ya dan shafa lokaci daya yana lumshe idannuwansa, yau kafin ya samu karfi a jikinsa sai da ya yi da gaske, ga RHISA a gefe sai wani murmushi yake masa wai bai zata zai fito yau ba shi mai danyar amarya a hannu, shi dai bai kula shi ba, dan RHISA ya jima da barin hanya sai addu'a
Da kyar ya samu ya yi barci dan sake sake da tunane tunanen da basu da anfani sam, washe gari yana fitowa ya ringa buga mata daki da kyar yarinyar nan ta wani amsa da meye, shi abin da ya rike masa wuya kamar ya shiga ya mikar da ita tsaye ya fafala mata mari, sai dai ya kyaleta yace shine ta tashi ta yi sallah, yana jin karar dirowa ta yiwu da ta ji muryarsa ta fado?
Chapter 84 · 0% Book details