← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 110

Sashe 20

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Auta ke ce min kun je asibiti na zata ko ciwon nan nata na mara ne dake kaiku lokaci zuwa lokaci?"
Rai bace Hajia ta ce" Babu ciwon mara, abinda ya ainahin faru na san ba zamu taba sani ba sai a lahira, dan ita ba zata fada min takamaiman me aka yi mata ba, abinda na sani shine ta je wajenta ita kuma ta hankadota daga kofa wajen matatakala ta mulmulo ta fado a summe, yanzu haka maganar da nake yi maka likita yace sai mun kwana zuwa gobe dan bugawar zuciyarta ya ki daidaita, a cikin barcima haka take sauke ajiyar zuciya, wannan wani irin masifa ne, a kanki aka fara samun y'a haka ne?

Menene laifinta ita?

Ko menene matsalar ne?

Idan bakya son ganninta ba sai kin wulakantata ba, danma d'a da uwa ne har take duban inda kike, da wata ce ba mahaifiyarta ba na rantse maki ko gawarki ba zata bi ba , haba dan Allah haba jama'a, ku kuma da kuke sakin jiki kunna wasa da kishi saboda uwarta kunna wulakantata ku sani Allah ba ruwansa da kai wanene ko ga dalilinka ita din da ta haifeta sai Allah ya saka mata irin cin zalinta da take yi bale ku, wanda aka zalinta zai sakawa ko ba dade ko ba jima!, Kuma mata ne, kuma kun haifi mata da cikunnanku, ku kiyayi yiwa lamarin ubangiji shishigi, dan Allah ya haliceta a haka ba dan ya tsaneta ba, dan ta kasance haka ba dan ta aikata laifi ba, haka yake son ganninta, tata salon jarabawar kennan, Kasancewarta a tsakaninku kuma wata jarabawarku ce, idan kun dage ku sake dagewa zaku gani a kwaryarku!, Yarinya dai babu inda zata je Docter da ya kawota ya kireta yarsa a gidan ubanta take in kuma akoy wace ke bata kwondala ta daina daga yau na yafe, walahi walahi kun ji na rantse idan har matar nan ta fada a gabanku ta kuma fada a gaban docter a yau cewar eh ta bar min yarinyar cen ni kuma zan sake kilaceta zan kuma sake rungumarta, ko ya'yan da na haifa suka zageta sai na yafe su duniya bale ku kishiyoyi!

A nan zaku san ainahin wacece Zuwaira, shiruna ba tsoro bane ba kuma gabana aka shiga ba!"
Lahaula wala kuwata ila bilah, ai fadanta mai sauki ne a kan wanda ABAH ya dauka
Hankali tashe yake masifantarsu yana karawa, tambaya yake yi haka suke zaune ba tausayi ba jin tsoron Allah?

Tambayarsu yake yi me ta masu?

Tambayarsu yake yi cikinsu akoy wace ta isa ta zagaye idan Allah ya hukunta haka a gareta?

Fadi yake yi bara su ji kar su ga sun dauki shekaru sunna gidan miji, ko haihuwarsu ta tsaya babu ruwan wanda ya halice su in suka kawo lamarin wulakanci a hukuncinsa lalle zai nuna masu shi ya halicesu shine da iko da gaban jikinsu ya dora masu abinda suke zagin halitarsa dominsa ya ga yaya zasu yi?

A hankali ya rike hannun BABAN GIDA da ya mike ya rike nasa yana kallonsa a tausashe da aika masa duban ya rufa masa asiri ya daina magana da karfi kar ya jiwa kansa rauni
A hankali ya ringa sanyayar da muryarsa har ya juyo kan Aunty amarya dake kuka bilhaki
Muryarsa a tausashe ya ce" Ashe zan iya neman alfarma ki kasa yi min?

Kafin na sanki yarinyar nan na sani a masalacin juma'a tana zuwa bara, hankalina ya tashi da aka kawo min maganarta aka nunan cewa samari sun fara shiga sabgarta , a lokacin na saka aka bita aka gano inda kuke na nemi ganninki da karin haske a kan abinda aka fada, a lokacin yaya muka yi da ke?"
Sosai take hawaye, tana sharewa muryarta a sarke sosai ta sake sada kanta ta ce" Dan Allah ka yi hakuri"
"Ba hakuri nake so ba Nana , so nake yi ki sanar min yay muka yi da ke?"
"Ka min nasiha, ka min fada, ka kuma nunan ilar barinta tana yawo, ka nunan ilar hantararta da korarta da hannata kwana a inda nake, ka kuma nunan zaka talafa mana da taimakon muhali da abinci in riketa in bata tarbiya,......." Ta dakatar da maganarta tana zuba masa ido, kukanta na daukan wani irin yannayi mai zafi da kunna tana kallonsa ta ce" YAYA ZAN IYA RAYUWA DA ITA TANA WACE YAYAN MAHAIFINA YA YI MIN FYADE NA SAMETA?"
A haukace kishiyoyinta gaba daya suka zuba mata ido sunna zarro idannuwansu, su dai sun san y'a bata da uba ama basu san haka zancen yake ba
Baban gida kansa sai da ya zuba mata ido na dakikun da suka zarce yadda yake kallon mutumen da ba muharaminsa zuciyarsa na bugawa a tsayen da yake ya juyar da dubansa yana kallon baya gaba dayansa ya lumshe idannuwansa
A sanyaye ta dora da fadin" a lokacin na nuna maka nima abin a rike a bani tarbiyar ce domin nima nawa nake?

Inada shekara tara na haifeta a lokacin da muka hadu da kai bata wuce shekara takwas ba ni kuma sha bakwai a duniya, ka juya ka tafi dab sama mana salama da mafaka, ni shaida ce irin yadda ka ringa nema min mijin da ya dace ya zauna da ni da zuciya daya, ama a lokacin kowa sai ya kiya dan ya san ni din dati ce ga kuma wani datin, ..................................................

Aban baban gida Sanadiyar cikinta da na samu ta hanyar wayo da akai min, yayan mahaifiyata ya hadani da shi , yayan mahaifiyata fa Docter, yayan mahaifiyata................" Sai kawai ta sarke, ta fashe da wani irin kuka ta ringa fitar da numfashi sama sama kamar zata summa Hajiar ce kuma ta mike ta amshi ruwan da Baban gida ya dauko ya bude ya miko sannan ya juya ya basu baya hannunsa daya a jimke a bayansa dayan kuwa a cikin aljihunsa yana kallon garu har sai da tarin da take yi ya dan tsagaita, cikin muryar kukan ta ce" Sanadiyar fitowar maganar nan fili Mahaifiyata ta fadi ta mutu da ciwon zuciyar da bamu santa da shi ba, dama mahaifina baya raye, dangi suka kore mu dan kar abu ya fito a shiga uku, shi kuma ya karyata ya zauna a garinmu mirsisi aka yarda da fadarsa ba tawa ba........

A dole na baro garinmu na gudo ama abu ya biyoni an san wace ni wa nake riko ama an dauka a matsayin ta yiwuma karya nake ubanta ba daya bane da yawansu dan ai dai sunnanta shegiya ba yar halal ba............., Sai da ya kai aikatau ya gagareni samu dan na ci abincin bakina, saima lalatatun maza dake bibiyata burinsu mu lalace tunda sun ganni rungume da y'a sun gama gannin karuwa............., Ba zan taba yafe masa ba,, ita kuma wace ka ba sunnan nan ba zan iya dubanta a yanzu ba, na koreta na sanar mata ta barni na samu nutsuwa zan sanar mata abinda take son sani ta ki ta fahimta , shin idan na sanar mata cewa Yayan mahaifina ne ya yi min fyade har ta zo duniya ita zata iya daukan wannan maganar a zuciyarta ne ko tana tunanin zata yi darajar da zai dubeta ya watsa mata kwata ne?, na fada a tsaye na fada a zaune ina bukatar lokaci ban shirya fuskantar lamarin nan yanzu ba ama an ki a fahimta?, .................."
"Wannan din ba shine hujarki na wulakantata ba!" Baban gida ya katseta da karfi, ya fada a karro na farko tun wanzuwarsa a wajen , murya a dake, rai a bace, kirjinsa na yin sama yana yin kasa, yana kallonta da idannuwansa rinanu masu dauke da ruwan bacin ran da ya zarta misali
Idannuwansa da suka yi ja ya sake dorawa a kansu baki dayansu ya ce" Maganar nan ta dawo hannuna sannan ta zamo sirri a tsakaninmu, domin idan ta fita ta shiga kunnenta cewar waye mahaifinta a tsakaninmu ne ta fita, idan na san wanda ya fitar da ita sai inda karfina ya kare, zan ja da shi a hanyar kotun musulunci, hanyar iko, hanyar dabanci har sai na yarda cewar dukkan wani burbushin abinda zai iya zamtowa farin ciki a duniyarsa ya kare kaf sannan na barshi koda zamu yi mutuwar kasko ne ni da shi!!" Ya idasa da dan karfin da ya saka gaba dayansu hankalinsu tashi suka ringa kallonsa a tsorace banda Hajia da Aba dake dubansa tsigar jikinsu na tashi, hajia kuwa tana mamakin dama ya iya fada da karfi haka?

Ita kuma Aunty amarya da sauri ta sake shigewa jikin hajiar tana hade jikinta da yake neman sake kwasar rawa
Gefe ya maida dubansa dan kallon da mahaifinsa ke yi masa na son sanyayar da gabansa, a hankali kamar yadda ya saba masu magana a da ya ci gaba da fadin" Ya dace mu iya rike dukkan wani sensation da
motion dinmu a gaban yaran nan, ku sani ko me zaku ringa aikatawa tarbiyantar da su kuke yi a haka, irin halayan nan kuwa ba kowa zai jure zama da mace a haka ba mu kuma ba kwadasu zamu yi mu cinye ba!
Chapter 20 · 0% Book details