← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 110

Sashe 109

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar suka samu ya sasautawa kansa harma shi din da kansa ya ringa fadin shi kam ya yafe mata fitar da ta yi dan ya bata mata, ya yafe mata komai da komai, yana fata gobe kiyama ya zamto ta yafe masa shima, domin kadarar rayuwarsa ce ta zo a haka bashi da yadda zai yi, ya kuma ga aya sannan ya godewa Allah da ya nuna masa tun a duniya ba sai ya je kiyama ya dauki dakon kayan da kansa ba zai iya nada gamon dauka ba
A tausashe Aunty amarya d
ake rike da hannunsa tana kallonsa bayan ya sasauta ta shiga labarta masa rayuwarta, rayuwarta a dan dunkule, domin ko raping dinta bata nuna masa kai tsaye hakan ne ba dan ita da kanta zuwa yanzu ta ga mahaifinta yana bukatar jin naganar sosai ama kuma lafiyarsa da shekarunsa sunna bukatar kuyaye wasu tashin hankalin....., Ama kuma ta nuna masa ta haihu ba aure ta kuma nuna masa irin rayuwar da ta yi da yarinyar dan ta haifeta hakanan, tana hawaye ta ringa fada masa irin kyamatar yar cikinta da ta yi irin korarta da take da magangannu mararsa dadi, wanda hakan ya saka shi hawayen shima yana girgiza kansa ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Nana kema kin ga rayuwar nan?

Allah ka yafe mana, Allah mun tuba, to Nanata shikenan sai ki tsaneta?

Menene nata laifin a ciki?

Nanata kar ki ce min itana ta rasa ranta ko wata kadarar ta fada mata itama?

Astagfrulah zan kuma yin kuka mai nauyin gaske dan abin ya min yawa a yau din Nanata, ya min yawa"
Kai ta girgiza tana sake dan matsawa kusa da shi dan sai ta gane sake rasa farin cikin da ya kwasa yake shirin yi a hankali ta ci gaba da fada masa irin abinda ta ringa aikatawa kafin haduwarta da DOCTER ta sanadiyar yarinyar, irin abinda ya biyo baya, har zuwa amsheta da Mama ta yi, ta ci gaba da nuna masa ba laifi tsangwama yarinya ta shata ta kowa banda Mama da
anta, ta idasa da fadin daga baya aka gane bata da lafiya ne aka fitar da ita bayan Marshal ya auri yarinyar, ta sake sasauta dubanta hawaye na zuba a sanyaye ta ce" Abah, ina sonta, walahi ina son abina...., Abana ina son Zahrata sosai, ina son Fatina, ka ganta nan jikin Mama fati ya ki yafe min, Abahna jikarka bata rasu ba, ka ga Mama dake zaune ne Allah ne gatanta itace gatanta, itace uwa, uba, danginta, Abahna ta zo ta bata miji gayanan a gabanka wanda sai dai ka fada min wanene shi a waje ni kuma na sanar maka jikarka ta yi dace da miji na gari...., Abahna dan Allah ka yafe min ka ji?

Ka kuma daina kuka ganinan a gefenka in sha Allah mutuwa ce kawai zata rabaki da kai......"
Abin sai ya zame masa a harhade a kuma rarabe, farin cikin y'arsa dake gefensa , rashin matarsa, tashin hankalin jarabawar y'arsa ,farin cikin irin yadda Allah ya zagayeta da masu talafa mata har aka kawo yanzu, baban farin cikin wata mai kama da shi din sak banda wasu yan gurare a tare da ita da suka dan bambanta da nasa da kuma na mahaifiyarta wa'inda ya tabata wajen mahaifinta ta yi su ama farin fatar , yannayin jikin gaba daya nasa ne shi ya sake bukatar ta karaso kusa da shi, wanda hakan ya yi mata banbarakwai duda hawayen da ta zubar da magangannun mahaifiyarta da irin yadfa take sake kallon mahaifiyar tata tana ji kamar ta je ta rukunkumeta ta fada mata ba fa yafe mata ta gaza yi ba, aa tsoro ne take yi kar sai ta sakankance mafarkinta ya zamo karya, tsoro take yi sai ta je din ta tsine matan kamar yadda ta fada karshen zuwa da ta yi bangarenta tace daga yau idan ta kuma zuwa tana mata tambayoyi sai ta tsine mata.........?

Ya saka ta gaza zuwa har sai da Mama ta mikar da ita ta kaita da kanta ta zaunar da ita kasa kusan kaffafuwansa inda ya matsota sosai ya kama hannayenta itama yana kallonta lokaci daya Marshal ya sauke yar ajiyar zuciya yana ji tamkar ya ce kukan nan fa ya isa hakanan domin Zahrar tunda ta fara har wani shasheka take yi gashi ba lafiya ce da ita ba ba'a so hankalinta na tashi jama'a ama ya gaza ya sake zuba mata ido cike da tausayinta da jin farin cikin da ya tabata tana ciki na kalmar nan da ta rasa a rayuwa watau soyayar uwa , gashi yau ta samu har ana kukan ta so itama?

Ya tabata ta samu farin ciki da nutsuwar zuciya yau kam dan haka ya sake sada kansa yana sauraronsu Furucin SHEIK yana share hawaye da kuma murmushi ya ce" Na rasa matata ashe ashe amarya ce da ni daleliya haka?

Daga nan sai Dubai mu je mu shige ruwan kasa mu yi ta shawagi tsabar soyaya, jibeni da kyau na maki kuwa?"
Dariar da ta saka duda abin bako ne a duniyarta ya saka mamantama yin dariyar tana rike hannunta a hankali sannan ta dan dago fuskarta ta shiga share mata hawaye , ina kakanta a sanyaye sosai ya ce" ZAHRAh, dan Allah ki yi hakuri kin ji?, Ki sasauta fushinki ki kuma dubi mahaifiyarki kin ji ZAHRAh?"
A hankali Fatima ta dan juyo da dubanta wajen mijinta, ashe shi dinma ita yake kallo da kallon nan nasa na kasa kasa yana talabe da habarsa
A hankali ya lumshe mata ido ya kuma gyada mata kansa, lokaci daya kuma ta kalli Mama wace ta ringa gyada mata kai tana kallonta , hakan ya saka hannunta na rawa itama ta rike na Mamanta sai kuma ta mike a hankali tana kallonta kafin ta karasa jikinta ta shige sakamakon bude mata hannayenta da ta yi dan ta zo din ta rungumeta........, Har sai da suka ringa sakin ajiyar zuciya, a raunane sosai Aunty amarya ke fadin" Ina sonki, ni ina sonki Zahrana, baki da laifin komai Zahrah, idanma da mai magana a kan hakan ya zageni ama ba ke ba, ki yarda da ni Ciwo da kuma kuruciya sun yi tasiri a kaina sosai, ki kuma yafe min , in sha Allah ba zaki kuma gannin muzgunawa a wajena ba"
Lalle bawa gajen hakurinsa ke saka shi aikata aikin gagawa wani lokacin har ya rasa abubuwa masu mahinmanci dan nema ido rufe...., Lalle bawa kan manta menene rayuwa ya damki son sai ya ga ya gyarawa kansa ne tashi tsaye bayan ko me yake yi ya barawa Allah zabi kawai zai ga daidai da haske a duniyarsa mai karkon da ba na yan dakiku bane........, A yau ita FATIMA ZAHRAH HAMAD ta sake yarda cewa a cikin halitun bawa kowane yana da daraja kuma Allah ya san da shi, tunda ta wayi gari yau ita ZAHRAH ta ga duniya mai karfi wace ta bambanta fa dukkan hasashenta sai ta rasa me zata cewa ubangijinta bayan godiya?, Duniyoyin nan hudu dake cikin tata duniyar sun zamto cikashin farin cikinta har a kiyama......., Muryar wace take jira ta ji ta kireta da sunnanta ko dan ta zageta ne ta kirayetan tana saka mata albarka , mijinta abin alfaharinta yana murmushi a gefe yana kallonta da kallon da ta san menene fasararsa dan a motsinsa zata iya cewa a watanin nan kusan uku abinda zai yi da ido ko da hannu daidaiku ne ba zata iya fasarawa ba sunne na fadansa dan har yanzu bai yi ba a gabanta tun na kuruciyarya da ta gani ya sakata sake komawa ta zauna jikin uwa daya tamkar da dubu, uwar goyonta, uwar da bata da shamaki ko dar din ceaa duniyarta ce, a duniya tana cikin masu kaunarta wa'inda suka isa da ita take kuma kyauta zaton in Dai sunna gefe ba zata wulakanta ba, sai bakon duniyarta wanda zuwansa yanzu ne ama yayi wuf da zuciyarta, take ji dama ta sanshi da wuri da ta jima tana tafka shagwaba a duniyarsa yana kuma tarota, domin a yanzu ta fahimci lokaci daya shima ya kamu da soyayarta irin wace hausawa kan cewa ABIN CIKIN KWAN YA FI KWON DADI....

Karshe dai Malan ya dauki awani a gidan nan a falon Mama har sai da ya yi kiran yaransa ya shaida masu su tafi uzuririkan gabansu shi ba yanzu zai fito ba, da kyar dai aka ajiye zance kan Aunty Amarya ta bi shi , Fatima kuwa mijinta zai kawota daga baya ta kwana koda daya ne sai ta dawo gida
MARSHAL din ne ya kaisu da kansa a tasa motar bayan ya sanarwa ZAHRAh ta yi ta koma gida ta huta kafin ya dawo fa, domin yau ko barcin ranar bata taba ba sai kuka da ta sha baya so hakan ya haifar mata da ciwon kai...................

Rayuwar kennan, a
AKIKA
IYAR mahaifiyarta ta fito daga gidan mijinta da ita dan ta hadu da bacin rai na miji wanda ta gaza hakurinsa har ta yi nesa da shi, sanadiyar rabon yar y'ar da take jaye da ita a hannayenta ta je nesa da garin ga kuma kasa ta kirayeta....., A yan dakikun ta hadu da ciwon zuciyar da ya buga zuciyarta, hakan kuma wata hanya ce ta sanadiyar zuwa birni da rayuwar Zahra a matsayin matar MARSHAL..............
Chapter 109 · 0% Book details