← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 110

Sashe 69

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mu ci gaba da addu'a mu kuma ci gaba da shiri in sha Allah Allah zai dafa mana"
Uwa kennan, shi kam zai iya cewa bashi da mafaka, wajen jin dukkan damuwarsa ta yaye, du wani tashin hankalinsa ya yi kasa, kamar idan ya tunkaro mahaifiyarsa, ta waya ko a gabanta ya sanar mata damuwarsa
A dazu fa ji yake yi hijirama zai yi kawai, guduwa zai yima ya bar kasar baki daya ya huta, ama a yanzu da ta yi masa nasiha da sansanyar muryarta sai ya ji Hajia babu abinda zata yi, in sha Allah zai ci gaba da neman aurwen Zahransa, shi ya san ya yi zabe kuma yana fatan ya sameta dan idan ya rasata ya san ya tafka asara
Kwonci tashi asarar mai rai in ji yan magana
A cikin gidan docter kwanaki na tafia ne shirye shirye na kankama, domin a yau aka tara iyaye dan basu abubuwan da aka ware domin siyayar
ansu mata, hakan ya sa suka hadu da shi da Amir da kuma khamis din a falon MAMAH harda Aunty Amarya da ta wuni nan aka hannata tafia ta zauna za'a bayar da kudaden wa kowace uwa na y'arta, hakan ya sa yan matan wasu ke sama sunna sha'anin su, wasu kuwa suke waje sunna dan dafe dafe dai da sauransu tunda yama ce dare bai yi bale a shige daka
Amir ne yake kaiwa kowace uwa bayan an sanar
anta mata kaza zata aurar a bata kudin bukatar na adadin
an harda Maman su FURERA da kuma Mamah wace a nata kason na ya'ya uku reras aka bata aka sanar cewa da ZAHRA, hakan ya sa Maman Abul ta ce" Au , Zahran ta yi miji ne?"
Mamah ta yi murmushi ta ce" Baki san tana da manemi ba?"
Maman Abul ta dan tabe baki ta ce" Ina zaka sani, samarin masu zuwa ai da yawa wajen nata"
A hankali ya zubawa Maman Abul ido, sai kuma ya dauke yana ji Mama na bata amsa, Amir ya mike ya leka sakamakon Sergent da yake magana a kofar falon
Sanar masa ya yi wai wata mata ce ke son magana da Maman Zahra, tana cen kofa ba'a barta shigowa ba
Dan tsai ya yi yana tunani, sai kuma ya bada damar a shigo da matar, koma wacece ya san bakuwar Mamah ce ko kuma ta Aunty amarya, duda ya fi yarda cewar bakuwar Maman ce
Karasa salamar iyayen nasu suka yi, Khamis ya mike ya wuce dan daga wajen aiki ya taho saboda MARSHAL yace sai ya zo,
Suma sunna shirin wucewa wajen nasu aikin Hajia Baba ta shigo, ita da
anta biyu yan mata
Du irin abinda ta shawo dan ta zo ta yi magana da babar murya sai ta ringa jin tsoron hakan a zuciyarta, tun daga bakin get jikinta ya ringa yin sanyi, har ta shigo falon nan wanda ya idasa kakabe mata du wani jiji da kai da isarta, uwa uba da Amir ya sanar cewa baki ne akace na Maman Zahrah, yana murmurshi dan ana fadin haka Aunty amarya ta dauke kanta dabma karma wanda ya kalleta
Mamah na murmushi ta ce" Bismillah, baki na yi?

Bismillanku ku shigo"
Maman Furera ta tabe baki a ranta tana ayana' Allah mai iko, wannan shine abin gudu ya zama abin ado'
Zama suka yi a kujera, Amir ya wuce, sauran matanma suka fara kokarin tashi , MARSHAL kuwa ya nufi cen wajen frij dan ya dauki madara mai sanyi
Gaisawa suka sake yi a mutunce, Mamah take sheda masu bata gane fuskokin ba, fuskarta cike da fara'a da tarba irin ta mutunci
Ajiyar zuciya Hajia Baba ta sauke ta ce" Eh, hakane Hajia ai bamu taba haduwa ba, dama ni yayar Mahaifin Hasan ce, wadinnan kuwa Y'ayana ne"
Fara'arta ce ta sake fadada, Maman Abul kuwa har ta kama kofa ta saki ta dawo ko kunya bata ji ta zauna tana sakale jakar kudinta ta yi kamar bata tashi tafia ba, kunnenta a wajensu tana sauraro
Fitowar MARSHAL MAMAH ta nuna masa, tana ta murmushi ta sanar masa ko su wanene, sannan ta gabatar da shi matsayin yayan yaren baki daya kuma madaurin aurensu, sannan ta dora da fadin" Ai bamu san da zuwanku ba Hajia da mun shirya tarba, bata ce zaku zo ba Zahran ai da mun shirya tarba mai kyau"
Du irin yadda ta zo da wuta wutarta, sai ta ringa neman kalaman ta rasa, dama Maman Furera bata tashi ba, dan ita Allah ya yi mata dan banzan tsegumin tsiya, ga maman Abul, ga aunty amarya dake zaune ta yi kamar bata san me suke yi ba, uwa uba ga Marshal.........

Du irin yadda ta zo da wuta wutarta sai ta ringa neman kalaman ta rasa, dama Maman Furera bata tashi ba, dan ita Allah ya yi mata dan banzan tsegumi, ga Maman Abul, ga Aunty amarya dake zaune bata kula kowa harkarta take yi kamar ba maganar Zahra ake yi ba, ga Mamah, ga uwa uba MARSHAL, Marshal ai idan baka sanshi a ta hado ku ba zaka sanshi a TV ko a jarida ko a gidan redio, akan yi magana ace sako daga shi, uwa uba ita shi ta dauke shi da matukar mahinmanci, dan takan yiwa
anta misali da shi da nagartarsa idan tana magana, hakan ya sa ta dan daburce a yanzu har ta rasa ta inda zata fara, dan murmushi ta yi tana dan shafa gaban goshinta ta ce" Ai kam, ai itama bata san da zuwan namu ba Hajia, ni dinma abu ne mai mahinmanci ya kawo ni, ban sani ba ko kebewa muke yi mu zanta?"
Caraf Maman Furera ta ce" Aa ku kebe ina kuma Hajia, a nan da kika gano iyayen Zahran ne mu baki dayanmu, kin ga mahaifiyarta nan, mu kuma abokanan zamanta kennan, ai komai kina iya fadi gabanmu dan abinda ya yi ZAHRAH ya yi mu"
Da mamaki Mama ta dubeta, sannan ta kalli MARSHAL dake zaune shima yana kallonsu a tausashe, sannan ta maida dubanta kan Hajiar fa
anta, sai ta ga y'arta daya banda kallon MARSHAL babu abinda take yi, kallo irin kazamin kallon nan dan har wani langwabar da kai take yi, dayar kuwa hankalinta a kan Mamansu
Dan numfashi Hajia ta fitar tana jinjina zumuncinsu
Ta ce" To ni ai na shiga rudu, nama fara karyata abinda aka fada min, yau kwana uku kennan da wata yarinya ta nan gida ta same mu a cen gidan su Hadan din take fadin magangannu mararsa dadi, to dai ni da farko nama yarda, yanzu kuma sai nake kokonta, ta yiwu wani abinsu sukeda tsakaninsu ta zo mana da maganar"
Mamaki gaba daya babu wanda bai kama ba, y'ar cikin gidan?

Wace irin mafana ce ta je masu da ita?

Har gidan su Hasan?

Kai wasu a cikinsu har cikinsu ya duri ruwa da tunanin kar dai aje dansu ne ya aikata hakan
A tausashe MARSHAL ya dan yi gyaran murya ya ce" Toh?, Me aka fada haka ne?"
Hajia ta dan ti shiru, sai kuma ta kalle shi tana fadin" Ai kam ni fa kunyama ta kamani MARSHAL, dan dai ka san nice baba a dakinmu, to nakan yi bincike nawa na kaina idan halin aure ya kama a kan
an nawa, ka san kowa zai so ya samu tsatso mai kyau ko dan tarbiyar ya'ya da ginuwar ahali, ina matukar ba hakan mahinmanci, shi yasa da aka sanar da maganar ta tsaya min a rai duba da muna tsaka da shirye shirye yace mana daga gareka yake jira a zo a yi komai zama guda dan yayar yarinyar ta sanar masa za'a hade da basu ne da ya rage yan kwanaki, to ni har na hau zancen na zauna, yanzu kuwa na bar maganarma tunda ga dukkan alamu hade hade ne na magauta"
Idannuwansa ya lumshe, wani irin abu na taso masa daga kasan zuciyarsa, dan a wajen nan babu wanda bai gane me maganar Hajiar nan take nufi ba, sai dai babu wanda yace komai dan shine yake maganar a yanzu, ama karara zaka ga tashin hankali a fuskar Mamah, ka ga wani yannayi marar misaltuwa a fuskar Aunty amarya, ka ga wani yannayi kamar na zakuwa da wani nuna wani zakewa a fuskokin matan biyu da suka rage
Da kyar ya dan iya rike agogon hannunsa yana dan murzawa, ai yanzu kam yana tunanin boye boyen ya kare, babu wani ja da baya sai dai ko wace wace
A hankali ya ce" wace magana ce aka fada din?"
Hajia ta ce" Dangane da nasabarta ne"
Maman Abul ta yi murmushi tana dauke kanta
Mamah kuwa ta sake hade hijabinta tana cimuimuya tana kallon Hajiar nan
MARSHAL ya dan sauke numfashi a hankali ya ce" Haka ne abinda aka sanar maki"
Da mamaki Hajia ta tsare shi da kallo, ya kuwa san me take nufi?, Dan haka ta ce" Aa fa, ina nufin yarinyar ta nuna ba Marigayi bane ya haifi ita ZAHRAN wai bata da u........."
"Hakane, me kika yanke dangane da maganar aurenta da Hasan?" MARSHAL ya katseta, a dake ya kuma yi mata tambayar yana kallonta ido cikin ido
Duda ta girme shi, a haifema zata iya haihuwarsa, sai ta ji wani shayinsa, sai dai abinda ta zo da shi in maganar haka ce ba zata iya cenzawa ba, dan haka cikin yannayi na jimami jimami ta ce" In dai haka ne, sai dai na bada hakuri, dan ba zan iya daukar wannan kasadar ba"
MARSHAL ya gyada kansa yana juyar da kallonsa gefe jin wani dan uban tsaki ya fito daga wajen Zuwai ta Docter, sannan ya sake dubanta a nutse ya ce" ok, Mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Daga haka ya sake juyawa wajen MAMAH yana ta tsatsareta da ido, dan ta fara watsa hannaye ya tabata daf take da nuna hali na fada a wannan lokacin
Hajiar kuwa tana gannin haka ta san me yake nufi kennan sunna iya tafia?
Chapter 69 · 0% Book details