← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 110

Sashe 70

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lalle ta yarda da akace yana da kannanun shekaru yana abu kamar baba, bai wani yi hayaniya ba, bai kuma ja zancen ba, baima nuna mata komai ba, saima godiya da ya yi, ya dai nuna sunna iya tafia kawai, dan haka ta mike tana dungurar kan Y'arta dake rike da jakarta tana kallon MARSHAL ta ce" Ku tashi mu je"
Sai da suka ja hannun y'ar tata sannan suka iya ficewa da ita, dan kamar wata mahaukaciya waigensa take yi har kamar zata tuntumba ta fadi
"Haka zaka barsu su tafi su zo har gida su ci mana mutunci su tashi su yi tafiyarsu hankali Kwonce?

Haka zaka barsu su tafi Sulaimana?!"
Da dan murmushi Maman Furera ta ce" Kai maman auta walahi wani lokacin abin rigima baya maki kadan, to ai basuma zo da rainin ba ni sai na ga sunna da mutuncima, sun yi abu a laluma a daka?, Allah dai ya sanyaya ama dama sai an yi ta haduwa da haka ai da wahala wanda yake da mafada ai ya afka haka din kai tsaye, sai dai kuma karfin rabo ko kuma a yi dace da irinta sai ki ga an dace, ai wannan din ba komai bane kawai a yi na yan uwan nata daga baya in an samu mai so a haka sai a bashi, ai gwarama da suka ji tun kafin a yi "
Tana gama fada ta yi gaba abinta, zuciyarta fess, duda ta so masa zancen a kudinta an wawusar mata kudi a gidan nan ama ta bari sai zaman gaba ta fada masa dan ta san tana fada zai bata ne wasu
Maman Abul kuwa mikewarta ta yi ta ce" Allah shi kyauta" ta yi tafiyarta itama, ya rage su su uku ne, dan Mama baki sake take kallon hanyar da matan nan suka bi tamkar zata kama da wuta dan takaici
A tausashe ya ce" Mamah, barin nata ta tafi shine alkhairi, wannan koda an basum ta yiwu wannan matar ta zame masu fitina a zamantakewar yau da kulun, dan kuwa irin matan nan basa barin ya'yan nasu su rayu lafiya fa iyalinsu, komai sai sun yarda komai sai sun amince......"
Mama ta zuba masa ido, a hankali ta dago hijabinta tana share hawayenta, muryarta na rawa ta ce" Kennan shikenan an rabata da shi itama saboda kadararta?, Wannan wani irin cin zali ne da rashin jin tsoron Allah na mutane?, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, yaya maganar nata auren kennan?"
A tausashe ya sake kure Mama da kallo, kuka take yi fa sosai saboda haka, uwa uba wace ta so basu mamaki Aunty amarya dan karara fuskarta ke zubar da hawaye har ta kasa zama ta mike ta nufi sama ta rufe ta fashe da kukan da suka rasa na menene, shin na tausayin y'arta ne ko kuma wani abin ne daban?

A tausashe ya matso kusa da Mama ya rike hannayenta yana kallonta, muryarsa a matukar tausashe ya ce" Ki daina kuka mana, kin san kowani bawa ai da tsanin da yake hawa dan kaiwa ga ci, Aurar da ita kike son yi ko MAMAH?"
Mama ta gyada kanta tana ta jan hanci
MARSHAL ya ce" In sha Allah, za'a daura mata aure irin na kowa, zata je itama ta rayu a gidanta, ki daina kukan haka kin ji Mama?"
MAMAH ta ce" To da wa Abah?

Da wa za'a daura mata auren Abah?

Ni kulun addu'a nake yi Allah ya hadata da miji na gari, wanda ba zai zauna da ita da cutarwa da gori ko makamancin haka ba, ABAH burina na ga yarinyar nan itama ta samu yanci, tana rayuwarta hankali Kwonce, burina na ga ta yi nesa da du wani mai zaginta mai wulakantata, Abah haka kawai nake da burin nan a kan baiwar Allahn nan, shin na nema da yawa ne ABAH?"
MARSHAL zai yi magana Rukaya ta bude tana janye da hannun ZAHRAH tana fadin" Na fada maki kar ki saki ki fadi Zahrah!"
Da sauri Mama ta mike tana fadin" Ke lafiya?"
Zahra na jin maganar MAMAH ta sake hannun Rukaya da gudu ta karaso ta fada jikin Mama tana barkewa da kuka mai raunata zuciya, muryarta na rawa ta ce" Mamah, wai yanzu Maman su aunty tace Maman su Hasan ta zo a kan maganana?

Tace wai wai sun ce sun hakura da ni?"
MAMAH ta lumshe idannuwanta tana fadin" To sai me?, Shine abin yiwa kukan?

Sai me dan sun hakura ZAHRA?

Allahn da ya sa haka shi ya san me ya tanadar maki, Allah ya sa hakan shi ya fi zama alkhairi ki daina kukan haka kin ji?

Share hawayenki Zahrana ai ba shi kadai Allah ya halita a duniya ba bale mu yi kukan ya gujeki, dana cen ba shine alkhairin naki ba kin ji Zahrana?, Maza goge hawayen haka mana kin ji?

"
Tana fada tana cirota daga jikinta tana share mata hawaye ne ta dubi Rukaya ta ce" Ke kama kanwarki maza ku je ta yi wanka ta ci abinci ta kwonta , bana son kukan nan idan kuwa ta ci gaba ki fada min, ina zuwa zan je na nanaga keyar matar cen a kas, in na yarda na kyaleta ni ba Matar Docter bace!, Walahi sai na nuna mata ita karamar marar mutunci ce yau a gidan nan, ta kuma tatara ta tafi gidan nasu daga cen ta yi taron bikin y'ar tata dan ba zamu iya zama da husumamiya jarababiya a cikin gida ba!"
Rukaya ta kama ZAHRA suka kama hanyar sama , Zahran sai kukanta take yi,gani take yi shikenan ita kam bama zata kuma kula kowani saurayi ba kuma, ta hakura walahi
Mama ta warci carbinta ta nufi hanyar fita
A zabure ya farka daga kallonsu da yake ya mike a hanzarce ya kamo hannun Mamah yana zarro ido ya ce" Subahanalah, Mama biye mata zaki yi ?

Ki barta da halinta mana ba ita ta sani ba?"
Mama rai bace ta ce" Kai rabani, na ki na barta da halin nata zan je na goga da ita da halin nata, ai ba yau ba nake barinta da halin nata har hakan ya sa take tunanin fin karfina ta yi, matsa min hanya Baba, ita munafuka to an fasa auren ZAHRA sai me?

Allah ai shi ya haliceta zai kuma bata miji in sha Allah!"
"Mamah, *NI ZAN AURETA* " ......,...........,..........,..........,..........,.......,...........Kalmar ta fito daga bakinsa tamkar yana rada, kasa kasa sosai tamkar baya so wani ya ji, idannuwansa na rage girma sosai tamkar wanda zai rufe su ruf, kirjinsa na dikawa da karfi tamkar zai aikata sabo,
Ido Mama ta ringa kiftawa da farko, a hankali ta shiga karkata kunnenta tana kallonsa, kasa kasan itama ta ce"
Ido Mama ta rinha kiftawa da farko, a hankali ta shiga karkata kunnayenta tana kallonsa Dan sai ta ji kamar bata ji da kyau ba, kasa kasa ta ce" Kai zaka aureta?"
Idannuwansa ya dan sada, sai kuma ya dago yana dan yatsina fuskarsa, har ga Allah a ji abinnan baban abin kunya ne a ganninsa, a hankali ya ce" Mama, ba umarnin Docter bane?"
Mama ta ringa kifta ido tana ta tsatsareshi da kallo
A hankali ya sake fadin" Zan yi masa biyaya ne, zuwa gaba ba sai na karra auren ba idan hakan ya kama?"
Mama ta ringa jin wani irin salama a kasan zuciyarta, wani murmushi ya kubuce mata ta yi raf da hannunsa ta ce" ka yi masa biyayar dai, ama kara aurenma ai bashi da wani anfani Babana Abana Ubana na kaina, Allah dai yi maka albarka ya tsare gabanka da bayanka Dan arziki irin albarka, wannan magana ka yi min shiru da ita a bakinka mahaifinta da auntynta kadai zan sanarwa da kaina bayansu barni da rikicin sauran al'umar, yanzu bara na je na gama da wancen"
Ido ya sake zarrowa, abubuwa biyu suka zo masa wani iri, mahaifin ZAHRA aboki a gareshi, amini na cin anani, yanzu da wani ido zai kalle shi?

Sai kuma.maganar tarda Maman Furera, shi baya so, baya son rigima, wannan biye matan da zata yi ai gani yake yi zubar da daraja ne, ta barta da halinta, ta zuba mata ido ai rayuwa ce, duniya ce ko me kake yi kai da Allahnka, sai dai ina hannunta ta janye ta fice ta barshi nan tsaye yana jin ya tarka abin kunya tamkar wanda ya sha giya, jama'a wannan kayan kunyar ina zai kai shi?

Yarinyar nan karama ace ya auri wa?

Shi ya san tunda Abansa ya fada dama da wahala ya kasa yi masa biyaya, bale ya kula Mamama haka take so bama da ta yi kukan nan yanzu sai ya ji meye to dan ya ji kunya?

Sai gashi shi ya dauko wannan tarin abin kunyar?, Ya Allah yaushe zai iya fara shawara da kansa kafin ya fadi magana ne?

Kai kawai ya girgiza ya koma ya dauki abubuwan bukatarsa ya yi ficewarsa , wajen aiki yau zai kwana dan aiki ke da su mai yawan gaske mai kuma mahinmanci
Da kyar Rukaya ta samu ta rarasheta, ta sakata a gaba ta bata dukan bakin da ya dace, ta kuma nuna mata eh haka din ne yadda Mama tace shi din ba alkhairinta bane, ta dauki dangana ta yi hakuri, idan ta yi hakuri sai Allah ya maye mata gurbinsa da wanda ya fi zama alkhairi a gareta
Lalle ta ji sauki sauki, duda hankalinta a tashen yake sosai, duba da yau da safema sun sha hura har sai da ta kashe dan kanta yana jadada mata soyayarsa, ita fa sai yanzuma take jin ashe tana son Hasan sosai din nan?
Chapter 70 · 0% Book details