← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 110

Sashe 46

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yaya jikinta ne?"
Jalaluddeen da dan mamakin jin yayansa na masa tambayoyi , duda abinda ya shafe shi yake tambayarsa, ama a sanyaye haka ya dan dago ya kalle shi, yannayin da ya gani a shinfide a saman fuskarsa ya sake saka shi jin wani irin tausayi na yayan nasa a cen kasan zuciyarsa , a hankali ya ce" Eh ta ci, tana tare da ZAHRA tana tausa mata kafafuwanta yanzu haka"
A hankali ya lumshe idannuwansa ya gyada kai yana fadin" To zuba mana mu ci abincin "
Yanzun kam dolema mamakinsa ya kasa boyuwa, ya zubawa yayansa ido sosai, sai kuma ya zuba abincin duk da yana yi a ransa yana jin tsoron kar ya yi ba daidai ba har dai ya gama ya ajiye ya dan duka da nufin tafia Babangida ya idasa kashe masa mamakinsa ta hanyar saka shi zama dan su ci tare
Gaskiya ya yi mamaki, hannunsa hannun yayansu da Aban Ahmad sunna cin abinci hankali kwonce har ya dan tataba ya basu waje suka gama ci ya kwashe ya mayar da sauran bangaren Maman ya tarda yan uwansa suka hade a zuciyarsa maganar na mintsininsa , karshe ya ajiye hakan a mizanin halin da yayansu yake ciki na rasa ABAH ne, babu wanda bai san irin kusancinsa da Abah ba, a yanzu da yake cikin halin nan dole a tausaya masa, ya rasa uba, amini, abokin shawara, idan ka gansu sun taho shi da ABAH sai sun baka sha'awa, ko me zai yi sai ya shawarci mahaifinsa, bashi da wajen hira ko wajen kai kuka sama da Abansa, yau ya wayi gari ya laluba babu, mutuwa kennan mai yanke duk wani launi na jin dadi ko akasinsa, mai mayar da mata zawarawa mai mayar da yaro maraya....Allah ka bamu kyakyawan karshe
Washe gari mahaifiyar marigayiya da kanwarta da
anta biyu wa'inda zata wanke din nan suka iso gidan makokin
Tunda suka zo suka sauka a bangaren na Maman ita ta zagene ta shige cikin yan gida, irin yadda take shige da fice kai kace da igiyoyon auren MARSHAL a wuyanta, tunda ta zo ta ce da Laraba kauce bani waje ke karamar yar bariki ce, domin itama Laraban har kwana ta yi a gidan, amma ita a dari dari take hasalima cakule take da yaran gidan wajen su Furera, amma ita tana zuwa ya zamto a bangaren iyayen ta fi zama sannan ta fi bauta masu, dukkan wani abu da ya dace ace an yi da shishigi da iya damawa da mutane ta ringa sani tana shigewa jikinsu sannu a hankali kafin ake zuwa kwana bakwai har ya zamto idan wani abin ne sai ka ji an ce aunty MINAL kaza ake so, ko kaza aka ce, ita kuma da karfinta zata je ta yi, haka kuma babu dakin da bata shiga kanta tsaye, babu wace bata yiwa shishigi har ta gane wace wa a cikin iyayen MARSHAL din
Su da kansu iyayen tun sunna mamakin ita kuma yaya haka kamar wata sarakuwar gidan bayan yayar matarsa ce har suka harbo jirginya suka kuma zuba ido da tarin mamakin gannin wannan kwabi, to kwabi yake a idannuwansu mana itama mimin da ta rasu ta girmeshi bale yayarta, duk da mutun ce mai karamin jiki ga kuma.iya kula da jikin nata dan kana ganninta zaka fahimci a waye take tass, ama kuma ai abin wani banbarakwai da shi
Mamah kam tana daga gefe, carbinta shi ya fi komai yi mata dadi a hannunta a irin wannan lokacin
Bata kwana a bangaren Abah, takan je dai tunda safe, dare na yi su juya da
anta bangarenta su kwonta
A zaman da take yi a bangaren na Abah hankalce take da kowa, tun ba'aje ko'ina da rasuwar ABAH ba take fuskantar abinda ke iya zuwa ya zo, hakan ya sa ta sake tsananta addu'a sannan ta hanna kanta shiga huruminsu dan kar su matsewa junna waje a zo a yi abinda ba shikenan ba, domin ta kula a tsakanin nan nasu kowace kiris take jira ta dankarawa yar uwarta magana bayan su dukansu sunna cikin hali ne na rufin kai, hakan baya hanna su shagalta da hiraraki da yan uwansu da dai sauransu, shi yasa ta iya kanta ta kuma iya
anta, domin sau daya aka dankarawa Fatima maganar da bata yi mata dadi ba, ya sa ta sake jajircewa kan Y'arta a hakarkarinta, idan me suke nufi su kuma su yi rayuwa ce, dan Maman Abul ce da kanta wai tace da Fatima oh yan matan Mama kuma sai a fara bankwana da Maman ko?, Tunda lokacin a kara gaba ya yi a je a bi wani sarkin........, Wannan magana sam Mama bata ji dadinta ba, ta kuma sake gannin rashin wayonta sannan ta sake kama kanta dan ta tabbata itama dama ake jira , wanda ya hada dinma ya rasu amma ba zasu sasautawa kansu zafin kishi ba
A haka kwanaki suke ta tafiya, MARSHAL dai bai koma bakin aiki dindindin ba sai da aka wayi gari aka yi sadakar Arba'in ta ABAH, a washe gari ya ringa sallamar mutanen da suka masu karra suka zauna har wannan lokacin ciki harda Minal
Da kanta ta same shi a inda yake zaune, watau wajen gerding ta duka har kasa kanta a kasa cike da kisa irin ta wace ta goge tana dan make murya kamar zata yi kuka ta ce" Allah ya taimakeka muma muna so mu juyo ko gobe ma in sha Allah"
Jaridar dake hannunsa ya ninke a hankali yana dan kallon yannayinta,
A katse ya ce" Allah ya nuna mana"
Kai ta dago ta zuba masa ido a ranta tana ayyana shikenan?

Bakin maganarsu kennan?, Shikenan ya kare magana kennan?, Sai kuma ta dan sake sada kanta a tausashe ta ce"
[11/26, 7:31 PM] MAMAN ASLAM: Murmushi minister ya yi ya ce" Masha Allah, ai biyuma gari ne, bale na san ai sun kusa aure, kana aurar da su din sa kawo maka jikoki birjik"
Sake kakalo murmushi ya yi yana doke hannun MARSHAL dake dan tsokanarsa ya ce" rabu da shi Shugaba, wannan kannin nawa ya iya nema, yaran fa kannanu ne , dan karamin wata uku ne da aka yaye shi,, ka san auren bai jima ba "
Haka dai suka dan tatauna, MARSHAL ya masu rakiya wajen motocinsu suka tafi ya dawo yana duba agogon hannunsa ya zauna yana hankalta da yannayin Aban Ahmad
Da kula yace" Friend yaya dai?"
Aban Ahmad ya dago da sauri dan ya afka a duniyar tunani
Idannuwansa da suka dauki ja sosai ya rintse, muryarsa a raunane sosai ya ce" Friend wai sai na ga wata yarinya a gidan nan da ta tuna min..., Da ta tuna min maganar nan da na yi maka, yarinyar kuma Bama zan ce ga kamaninta ba, na dai dan kalleta na dan lokaci ta gudu, ........banma san me ya kawo tunanin nan a raina a irin wannan lokacin ba sam"
MARSHAL ya dan tabe bakinsa, wannan karron da wani yannayi shi ba na halin ko in kula ba, shi ba na damuwar abokin nasa bata shafe shi ba , a wani rashin ba abin mahinmanci ya ce" Ohk "
Aban Ahmad ya zuba masa ido, Amsar sai bata yi masa ba, duda ya san maganar tana kona ran SULAIMANE amma ai ya san babbar nadamar sa ce, sannan babban abinda ya binne, ne, tunda ya shigo garin nan ya samu hanyar samu har yau ya zama abinda ya zama damuwar dake rage masa walwala kenan, ya rasa yaya zai yi, ya rasa ta inda zai billo, ta inda zai fara
"Ka san, a yanzu, bana tunanin zaka tunkaro wani ya kasa sauraronka, ina gannin, ya dace ka ware lokaci, ka je ka binciki inda take, dan kuwa kar ka manta, Allah baya yafe laifin da bawa ya yiwa bawa sai idan bawan ya yafe ne, gashi muna cikin hali na a wuni da kai ba'a tashi da kai ba, wannan din babban laifi ne, yaya take?

Tana raye?

Wani hali ta shiga sanadiyar hakan?
Chapter 46 · 0% Book details