← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 110

Sashe 110

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hakan itama cikin salama ta samu daidaito da nata malamuncin kuma uba ga y'arta wanda du duniya babu wanda zai dauketa ya san darajarta fiye da shi a irin wannan lokacin da yake cike da muradin son ganninta muradin faranta mata, muradin sake goge laifinsa da ya dauka har yake tsoron haduwarsa da ubangijinsa da kaya irin wannan a saman kansa.........mm, Lalle shima jin dadi na
AKIKA
IYAR ya haifar masa da tashin hankali na shekara da shekaru, domin sakamakon abinda ya fitar a jikin y'ar yarinya dan ya kawar da kwadayin da shedan ke kawata masa ya saka shi a ha'ula'in rayuwa har ya bar garinsa inda ya haramta a gareshi domin ba zai kuma iya rayuwar ciki ba du kuwa da nasa iyayen kushewarsu a cen, sai dai idan wani sanadi na kasa zai mayar da shi, ama a yanzu kam shi ba zai yi wannan gigin ba....Matan da yake rike da su da Allah ne ya bashi ya san ba halayansa ne suka bashi ba yana kaunarsu yana kuma iya yinsa dan kamanta adalci a tsakaninsu....., Ya'yansa kuwa kwaya uku yana tsaye a kan dukkan wata bukata da ya dace ace uba ya tsayawa d'ansa, ZAHRAh itace baba sai docter da kanninsa ua zamto dukkan wata kula yana iya yinsa a kansu kuma bukatunsu sunne bukatunsa
Kwonci tshi a hankali Zahra'u ke rainon cikinta, har ya zamto ta fita a wata na takwas ta shige na tara yanzu, yayi daidai da haihuwar Furera wace ta haihu a asibiti kuma mahaifiyarta ce da kanta dole tsaye saman kanta domin an yi daidai da haihuwar Rukaya wace itama nata haihuwar bata cike wata tara da sati biyun ba ya zamto Mama hankalinta na cen domin Aunty Luba ta yi tafia da mai gidanta, Aunty amarya kuwa bata da lafia dan har Zahrah ta je gidanta wunin yau ko zata dan taimaka mata da wani abin ama firr aunty ta ki su zauna domin ciwon nata mai dalili ne, karshema itace ta yi kiran MARSHAL din kan ya zo ya dauki matarsa domin irin yadda Zahran ke dan kukan bayanta da kuma yadda take ta shiga bayi ya fara bata tsoro kar ajr nakuda take yi ta shiga uku ita dinma ba sannin yaya zata yi mata ta yi ba gwara a kaita wajen Mamanta
A lokacin da ya zo gidan Abn Ahmadi na tsakar gida yana ba manyan kwakwa dinsa abinci sunna ta ihu tamkar zasu warto shi dan fadan tsiya ne da su, sunnaa ganninsa ya nufo wace ta fi fadan ta nufo shi tanaa kwakwakwa din nan nasu ya kuwa gyara tsayuwa yana murmushi tana zuwa ya yi raf da wuyanta ya dagata a haka sai da ya yi juyi uku da ita sannan ya bi sauran da ita ya cikata cikinsu suka arta a guje sunna ihun kukan nan nasu shi kuwa ya tsaya yana daria harda rike ciki wanda hakan ya saka Aban Ahmadi zuba masa ido yana dafe kugu ya ce" D'an nan aikin me ka aikata kennan wa dukiyata?"
MARSHAL ya dage kafadu ya karaso inda yake tsaye ya miko masa hannu ya ce" Oya freind bani tissu na goge na shaki wuyanta a jike, wadinan agwagin naka basu da kunya, watau ta bini a guje ta caken idon kallon Baby ko?"
Aban Ahmadi ya girgiza kansa ya ki bashi tissu din ya ce" Kai dai abin kunya baya yi maka kadan, kwata kwata yanzun duniyar abin kunya gaba ka bata ba baya ba Allah ya shiryeka
an nan"
MARSHAL ya tabe baki yana gaba yana biye da shi tamkar gidansa ya dan dakata ya ce" Ai gwara ni babu wanda ya ga na fashe da kuka ranar daurin aurena, summa fa ka kusa yi wai an aura maka wace kake so, abin kunya Freind ai rikeshi ka yi ido da ido kai ka je ka dauko Aunty ka zo da ita gidan nan, to mu me zamu ce?"
Yana kokarin ramawar shima Aunty ta fito da saurisai zarar ido take yi ga waya a hannunta
Takim takim sai da ta zo daf da Aban Ahmad ta ce" Ni fa ina tsoron kar aje dama haihuwa ce, na shiga uku gatacen ta gaza mikewa daga shiga bayi nace kar ta hau WC dn walahi ance ana haihuwa a ciki"
A zabure Ya riketa yana kallonta ya ce" Nana kalleni dakata na ji me kike fadi, waye zai haihun wai?"
A rikicenta ta janye ta yi gaba a guje tana fadin" Zahrah ce mana zahrah ce"
Daga shi din Har Marshal din sai aka rasa waye zai ba dan uwansa dama ya fara shiga dakin
Sai dai sun a shigar Marshal ya wuce bayin da sauri yana kiran sunnanta shi kuwa a rikice ya ce" Nana shekaran Jiya ba mun irga yanzu ne ta shiga wata na tara ba?"
Aunty Amarya dake neman Mama ta samu da kyar a rikice take fada mata wai gashi Zahrah ce ke ciwon ciki da baya Maman ta ce maza su hadu a asibiti bara ta dauki kayan haihuwa idan haihuwar ce toh in ba haihuwar bace sai su dawo gida tana kashewa ta ce da shi" Aban Zahra ni na sani ne, abinda na sani kawai ance haihuwar fari da wahala ake kaiwa watanin da satitikan ana haihuwa da wuri ne...."
Fitowarsa dauke da ita ya saka gaba dayansu mara masa baya, Aunty amarya kuwa ta riketa fa kyau a jikin nasa har syka karasa wajen mota aka sakata ama ta kasa zama tace ba zata iya zama ba wani abu take ji a jikinta, sai zufa take yi mahaifinta kuwa sai numfashi yake da bakinsa yana faman fadin ta yi numfashi haka ta yi meye ta yi meye tamkar shine ke yin nakudar, tukin motar kanta sai MARSHAL ne ya yi domin daga Aban AHMAD din har maman Zahra sun gama rikicewa kowa na fadin abinda yake bakinsa dan ya taimaka mata ne , Aunty amarya na addu'a shi kuwa sai shasheka yake kamar zai summa har suka karasa asibitin da take awo aka karbeta da takardunta domin Mama daga gida direct nan ta yi da kayayakinta aka shigar da ita dakin haihuwa domin kuwa eh lalle haihuwar ce irin mai jinni mai murda cikin nan , sai dai zuwansu asibitin ya taimaka domin an amsheta an shige da ita da gagawa ana kuma kan bata kulawa
Lalle ta samu nakuda mai sauki, domin nakudarta da haihuwarta basu wuce nata awa uku ba Allah ya sauketa lafiya sai karin jinnin da aka jona mata dan ta dan zubar da jinnin ba laifi sannan aka shiga kimtsa baby boy kafin a mikowa Mama wace ita daya ke tsaye kan kafafuwanta sauran du sun rikice MARSHAL da bakinsa ya budu sai balbale Aban Ahmad yake da masifa kan ya daina masa numfashi haka baya so, du laifinsa ne lafiya matarsa ta zo gidansa daga zuwa ace haihuwa ce bayan bata kai lokacin haihuwar ba, shi dai fadan da yake yi kana gani zaka fahimci a rikice yake sosai ba shi din ba uban mai jegon har sai da kukan bakon duniya ya saka su rige rigen zuwa sunna tambayar mai haihuwar, bama irin Marshal wanda rainon cikin nan an yishi ne da fada masa kulun cewar ya fa kwontar da hankalinsa yarinya ta isa ta haihu da kanta wa'inda basu kaita bama sun raini ciki sun haihu bale ita, du hankalinsa bai kwonta ba sai da ya shiga dakin hutun da take kwonce idannuwanta lumshe tana sauke numfashi a hankali a hankali ya zauna a hankali bakin bed din ya saka hannayensa bibiyu yana rike da nata hannun a tausashe sosai ya dora hannun nata kusa da fuskarsa yana dan shafawa har ta bude idannuwanta ta zuba masa ido kasa kasa ta sakar masa murmushin da ya saka shi lumshe idannuwansa a hankali ya yi kasa ya mana mata kisss a goshinta sannan ya sake rike hannayenta da kyau a hankali ya furta" I LOVE YOU SO MUCH BABY"
Idannuwanta ta lumshe a hankali ta mayar masa da sakon kalmar soyayarsa wanda ke tafe da tarin farin cikin da fuskarsa ta kasa boyewa, madaukakin farin cikin da kwallah ke taruwar masa yana gogewa, tarin jin dadin da ya kasa boyuwa a fuskarsa haka itama a lokacin da kunnayenta ke jiyo mata rakadi da murna irin ta dangi har ya zamto kowa na son ganninta dan tayata murna, ita FATIMA ZAHRAH a yau gata ya sameta har ta samu farin cikin rayuwa....., A hankali ta saka hannayenta biyu ta janyo mijinta ta rungume kansa a kirjinta kasa kasa sosai ta ce " ALLAH YA RAYA MANA UBAIDULLAH"
TAMAT.......

ALHAMDULILAH
ALHAMDULILAH
ALHAMDULILAH
YAU NA KAWO KARSHEN LITAFINA MAI TAKEN
AKIKA
IYAR
TABAS A DAKIKA BIYAR KUN MIN ADALCI KUN KUMA YI MIN HAKURI, INA GODIYA DA YI MAKU FATAN ALKHAIRI DOMIN IN SHA ALLAH ZAN DAUKI DOGON HUTU NA RUBUTU, ALLAH UBANGIJI YA SADA MU DA ALKHAIRI YA KUMA TSAREMU DAGA DUKKAN SHARI, DAN ALLAH INA NEMAN AFUWAR DUKAN Wanda na batawa, INA KUMA GAYATARMU ZUWA GIDAN *GOBARA DAGA KOGI* NA KWATENA WATAU SAMIRA HARUN, KU KUN SAN ZAMU NISHADANTU ZAMU WARWASA.....KU ZO A SHIRYE TSAF DOMIN NA TABATA TEAM ZAI YI YAWAN DA MUNA IYA DAKUWA
love you mutanena
Calibri
Calibri
SimSun
Times New Roman
Times New Roman
Light
Light
DengXian
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
_GoBack
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
Infinix X688B
TECNO LD7
WPS Office
773dc17bd6994f999a0881069cf7e1b4
Chapter 110 · 0% Book details