Sashe 77
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To ni zan dawo da kai kawo gidan nan zan ci uban du wani mai ido a tsakiyar kai............."
Fada take yi tana haki, ranta a matukar bace yake, dama a duniya in akoy wace ta yi MAMAH dari bisa dari to itace, Rukayama ta dan yi Maman ama fa ita wannan karshe ce, ita ke bima Yayansu magidanciya ce ya'yanta bakwai, tana aure ne a wani garin daban tana auren alkali Yusuf Gila, ko da ta yi zaman gidan ABAH kyar ta san kyar ce, ana shayinta kamar yadda ake shayin mamanta, bata daukan raini ne sam , tun dazu kuwa sai da ta ga komai ya daidaita a gidan sannan ta tarkato kannenta ta yiwo baangarensu da su dan tace zaman ya isa haka kowace ta je bangarensu bayan ta wanwankawa Furera mari ta riki wuyanta sosai ta kuma fada mata zata nemeta dan bata gama da ita ba
Dakatarwa ta yi da maganar tana kallon yadda Zahra ke barin jiki
Da dan mamaki ta dafe bakinta ta ce" Ke Asma'u duba min yarinyar nan da kyau ko dai sun ji mata rauni ne?"
Rukaya ta yi murmushi a zaunen da take ta ce" Ba wani rauni, ai tsoro ne da ita da kika ganta a nan , in ba abu ya isheta ba ki ga ta iya ramawa, sai a jima ana ci mata kashi nata ido ne, sai tace kai da ALLAH"
Mikewa ta yi ta karaso inda ZAHRA ke tsaye Asma'u na dudubata ta yi tsaye tana kallonta, gaba daya jikinta rawa yake yi, a hankali ta ce" ZAHRA menene?, Ke dubeni menene?"
ZAHRA ta kalleta jikinta na rawa tana jan numfashi ta ce" Wai, wai, wai yayanmu ne aka aura min fa?"
Lubabatu ta tatare goshi ta ce" So?"
ZAHRA ta zuba mata ido, sai kuma ta fashe da kuka tana warware lafayar gaba daya ta yar a nan ta nufi wajen kujera ta rike kujerar tana kallonsu ta ce" Yayanmu aka ce fa?
Ni kuwa ina ni ina yayanmu?
A hakama ina lalabawa kar na masa laifi sai kawai ace mai gaba dayama wai an aura masa ni?
Ya fi karfina, yayanmu ba na irina bane , Aunty Ni fa shegiya ce, bani da uba, bani d....."
"Ke dilla rufe min baki ko na dauke ki da mari a yi abinda za'a yi!" Aunty Luba ta fada a mugun tsawacen da ya saka ZAHRA yin tsit tana kallonta tana kuma dan matsawa daga gefenta
Rai bace ta ce" Sakarcin banza, in kina da wani dalilin ki fada a duba, in baki da shi ki rike shirmenki tun kafin na yi kasa kasa da ke a wajen nan, wuce maza ki je ki yi wanka ki fito mu dora shiri dan kuwa yau zaki tare a bangarenki in kina so in kin je ki tsaya ya dafaki ya shanye roman, shirme ya'yan nan hala dan muna nesa da ku kuke neman zama wa'inda basu san ciwon kansu ba?
Har akoy namijin d ya fi karfin mace ne?
Wani irin fin karfin?, Mtssss shirme Fatima walahi a kan shirmenki ina iya maki duka yau a gidan nan bani da hakurin shashanci fa, kin wuce din ko na kaiki na maki wankan?, An aura maki SULAIMANA jikan SULAIMANA kuma sai an kaiki dakinsa muna saka ran badi warhakama mu sake taro muna soya hanji a gidan nan in sha Allahu dan yanzu ya yi aure kuma yanzu zai san menene mace, ana kina son nuna min zaman dodo da yaro zaku yi?
Baki isa ba na rantse da Allah sai kin zagine kin gwongwajeshi iya gwongwazuwa, a irin yadda ya raina yaran nan sai kin hanna masa fita office, in baki yi ba kuma na dauko mota na zo na rufe daki na darwaye maki jiki idan yaso ya harbeni!"
Fada take yi kamar zata ari baki, kowa yana kallonta ne, Zahra kuwa dake cikin bayi tana wanka ido take zarrowa rana sauraron auntynsu tamkar zata sume dan kalaman na auntynsu kamar fariya!
Tana fadan ta fita, hakan ya saka su sauke ajiyar zuciya a tare sunna hada ido, sai kuma suka samu kansu da sakin yar dariya sunna yin saman cafet din suka zazauna
Gulmar dake cin rukaya ta tsananin farin ciki ta fara bajewa, tana zarro ido da yarfe hannu, ba ta komai bace ba sai ta daurin auren nan
Aunty Asma'u ta yi gagawar fadin" Wai Rukaya tsaya, wai ko dai soyaya suke yi a boye ba'a sani ba?, Ke yayanmu fa ba'a masa dole, ba irin mutanen da ake yiwa dole bane, kunna tune fa ranar da aka yi zaman nan me yayanmu yace?, Kai nifa koda jikina baki daya kunne ne na ki na yarda cewa babu wata a kasa, ama abin nan ya matukar yi surprss dina, ba sanarwa, ba kwatantawa, daga sama magana ta fado ?
"
Rukaya ta ce" Aunty, kin san Allah mu dai muke tafe tare, mu dawo tare, bamu taba ankara da wani abin ba koda wasa, dama ba dai da ita ba dan kuwa ita fa kin ga ta yi samarinta da suka so junna sosai, Allah ne bai yi ba, sai kawai maganar nan ta fado mana daga sama"
Asma'u na daria ta girgiza kai ta ce" Ni ina son hango fuskar Yayanmu daga nesa, imagine yayanmu cikin dokokin da ya rika da karfi harda na yiwa yarinya aure da wuri, kulun sai sun kwasa idan za'a yiwa wasu aure a gidan nan shi da Baba, kin ga yau abu ya fado kanmu yaya ya yi gummmm, ni baban burina ZAHRA ta zagine, ta murje idannuwanta, ta yi like sai me a gabansan nan, kin san me so nake yi irin ta nuna ai itama ba wani ra'ayin mai shekarunsa take yi ba, idonta idonsa ta nuna ita aka cuta, so nake yi saima yayanmu ya samu abu daya tak ya daya a tare da ita ta dawo bakinta ya bude ta juya nata mulkin, so nake yi ta bambance masa aikin yara da na matan da ya saba kwasa!"
Fitowarta a bayi, da shigowar Auta ya saka su yin shiru da maganar
Auta dake dauke da kaya ta kai saman gadon ta ajiye tana kallon yayunta da kuma ZAHRAH dake daure da tawul kanta na digar ruwa dan wanke shi ta yi da ruwa ko ta ji sauki a jikinta baki daya
Murmushi ta yi ta fice, dan ta tabata wani maganar ake zantawa ama da aka ganta aka yi shiru, basu san yau itama bata da lokacin kowa ba gatacen da nata kawayen da ba'a gansu ba ba'a kore su ba sunna baje kolin nasu zumuncin da tataunawa a kan bakon auren da aka daura da Master Man a bazata.........
Shigowa Aunty ta yi itama da kayan a hannunta ta ajiye sannan ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a kasan nan da ta sauka Mamah ce kawai ta fi karfinta, ama ta samu Furera saura dauran, alkawari ne ta yiwa kanta yau ko a wajen kai amare ne sai ta baje rashin mutunci da mutanen nan, in me suke takama daidai take da su!
Tun daga wannan lokacin ya zamto abinda aka shiga yi shirye shiryen kai amaren ne, du wani abinda ya rage ba'a kai ba aka kai, kowace uwa kuwa tana bangarenta tana abinda ya fi gyarata, inda mahaifiyar Furera gaba daya ta shige dakinta take ta kukan takaici da bacin rai da bakin ciki, yayarta sai fada take mata tana fadin wannan dorawa kai har ina, ama ita bata sauraronta sai yayar tata ce ta je take kokarin gannin an gama shirya amaryar dakinsu a kan lokaci dan ita kunshinma yau ne ake yi mata shi
Haka Maman Abul ita kadai sai hadiyar zuciya take yi, lalle abin nan ya zo masu a ba zata ya kuma kona masu rai, kwarai sun ji ciwon abin nan, ama ita ta fi tunanin to yaya makomar zamansu nan gaba da yarinyar kennan?
Yarinya dai ko makaho ya san ta ga takura , tana kuma kan gani, sannan ko ita ko mahaifiyarta babu wanda zai ce ga ranar da suka rama abu a irin abinda take gani, shin kwontan bauna suka yi suka bi hanyar da suka bi suka malaki UBAN GIDAN baki daya yanzu zasu ci uban kowa ko menene hakan yake nufi?
Dudata abinda ya fada din nan ya matukar tsoratasu, irin yadda ya kalle su ido cikin ido ya nuna masu Matarsa ce su dukansu sun hadu da tsoro da bugawar zuciya da tunanin ko eh lalle soyaya suka yi zabinsa ce? sai dai kuma ko menene su sun san shi din ba zai taba kallon yarinya matsayin mata ba, kawai masifar uwarsa ce ta dauki y'a ta hada dan kauna wa y'ar kishiya, wannan bakon al'amari da daure kai yake jama'a,....itama haka ta yi wunin ba a cikin walwala ba, ga y'arta dake kwonce bangaren na Mamah, ga kuma amare gaba daya sai abin ya nemi cakule lisafinta............
Da yama, ko nace kusan sallar magariba Angwayen suka dawo daga gidan Aban Ahmad, sun ci sun yi nak sun kuma yi guzuri dan kuwa sai da aka hada kowa da guzuri
Cikin angwayen harda BABANGIDA da ya cenza tufafinsa zuwa wani danyen yadi mai wartar ido da saka zuciya tsumuwa mai ruwan bayan kwai, yadin ya dauki simple dinki ne domin wuya kadai aka yiwa dan zubi kadan sai dakaken mancheste na mazaje a tsintsiyar hannun nasa, sai hular da Aban Ahmad ya kakaba masa tunda ya ganshi da shigar ya je ya dauko hular ya dora masa kuma ya wani tsareshi da ido, shi dai bai ce masa komai ba, bama zai ce masa ba
Yana tsaye yana gaisawa da abokanan angon fa suka zo da wuri yana dan murmushi Aban AHMAD ya matso ya yi raf da hannunsa kasa kasa ya ce" ka ga mu je mu yi sallah lokaci ya gabato kafin mu fara mi
a ya'yan nan ko?