← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 110

Sashe 59

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ya sauke, zuwa yanzu sosai Aban Ahmad din ya fara ba shi tausayi, idan ya yi duba da irin damuwar da ya shiga a da ya cancanci a yi masa uzuri a kuma yarda da tubansa, bale abin da ya kwatanta babu lokaci mai hatsari irin wannan, ga shi ba iyaye a gefe bale su kwaba ko su hanna, shi ya godewa Allah ma da ya samu ganin wace ya cutar din da ransa da lafiyarsa ita ma haka.

A nutse ya ce" Ka san damuwa na haifar da mugun yanayi a tare da bawa, bale ita da kannanun shekaru ne abubuwan suka ringa samunta, baban abin da ta gaza gazgatawa rasuwar mahaifiyarta, a lokacin ina ga ai ba ta ma san ciwon kanta ba balle wai ciki, to ka ga da wahala ta iya yarda da cikin kansa."
Mamah ta sauke numfashi ta ce Hakane, in dai za'a samu hanyar da za'a iya taimaka mata lalle haka din shi ya fi, dan a duhu take da lamarin sosai, abun ya daketa sosai"
Ajiyar zuciya kawai yake saukewa, bakinsa ba shi da kalma mai karfi sai addu'a, lalle yana neman taimakon ubangijinsa, wani tsoro da shakun wacce ya bari a baby innocent na shigarsa, uwa uba idan ya yi wani tunani sai ya ga da wahala ta dube shi
MARSHAL ya sake dawo da maganar sanar mata, a tausashe ya ce" Mamah, ai maganar ba za ta kai gobe ba in sha Allah, yau za'a sanar da ita kawai"
Mamah ta kalle shi tana dan zarro ido ta ce" Yau kuma?"
MARSHAL ya gyada kansa ya ce" Mamah mun san ma kai goben?

Idan kana da damar aikata aikin alkhairi komai kankantarsa kawai ka yi shi a lokacin da ya kama a yi shin, ama ina ga ki yi kiranta ta zo nan saboda mutanen cikin gida, kar a ga mun fita harda shi mun shiga bangarenta jin san hakan zai saka a sako ido, a yanzu kuwa ba zan so a zo a saka mu a gaba bayan basu fahimci junna ba, idan ta yafe ta hakura kowama sai ya ji"
Mamah ta gamsu da shawararsa, dan haka ta mike ta karasa wajen wayar tafi da gidanka ta shiga kiran bangaren Aunty amaryar.

A kira na biyu ta daga da salama a bakinta
A tausashe Mamah ta ce" Nana kina wani abu ne?"
Aunty Amarya ta girgiza kai tamkar tana gaban Mamah ta ce" Aa MAMAH bana komai ai dare ya yi"
Mamah ta ce" Yauwa dan zo bangarena ina son ganninki yanzu"
Aunty ta amsa da to gatanan sannan MAMAH ta koma sama ta sake jawa
anta kunnen kar ta ga kowa ko me zasu ji daga falon kasa,
Tana saukowa Aunty amarya na yin salama
Fuskarta a kan Mamahn ta sauka, sai kuma ta kula da BABANGIDA da kuma wani bako dan fuskarsa ba ita yake kallo ba
Dan murmushi ta yi kadan ta karaso tana fadin" Au baba kana nan ashe, barka da warhaka"
Babangida ya amsata yana tambayar gida da yannayin garin da kula da girmamawa
Aunty amarya ta idasa shiga da kyau, tana dora idannuwanta a kan fuskar bakon da ya dago ya kafeta da ido bakinta na fadin" Alhamdulilah Baba, Mamah gani ko abinci zan sama....zan sam....

Da karfi ta dan rintse ganninta, a hankali ta sake budewa tana dauke dubanta a kan bakon, dan a tunaninta ganninta ne ke neman hadewa, ya nuna mata fuskar da ba kudi ba ko me zai zama ba zai bace mata ba ta dauke kan Mamah da muryarta dake dan neman hadewa ta ce" Mamah ko abinci ne zan samawa Babangida?"
Mamah ta hadiye yawu a hankali ta rasa wa zata kalla
"Nanah" ya fada a sanyaye yana kallonta
Maganarta dama ta jima da ajiyewa, sai dai a yanzu numfashinta ne ta tsayar na dakikun lokuta idannuwanta kakafe a fuskarsa tana kallonsa tamkar wace ke son gane shi din dan Adam ne ko aljan, dan kallo ne na kure halittta sosai.

A sanyaye sosai Mamah ta ce" Nanah, baki gane shi ba?"
Idannuwanta, da suke bushewa a hankali ta dauko ta sauke a kan fuskar Mamahn,
Da kyar ta iya kiftawa a hankali sai kuma ta budi bakinta tana mikewa tsaye a dan kagauce ta ce" Ban, ban gane shi ba Mamah, bara na koma."
"Aunty, dan Allah zauna kar ki koma, magana zamu yi" MARSHAL ya fada da kula da kuma girmamawa sosai yana dan sasauto da zamansa yana sauke dubansa shima a fuskar Auntyn.

Sai da ta ja wata irin kasalaliyar sheda, ta sake juyowa ta dora dubanta a fuskar Aban Ahmad dake hawaye ba kakautawa sannan ta sake duban MARSHAL ta kasa zaunawan. amma kuma ta kasa tafiyar.

"Dan Allah zan so ki yi kokari ki fuskanci abin nan da dak sauki kin ji?, Ki dan sanyaya abin ko yayane, a cikin kaso dari na bacin ran da ya dace ki nuna ki dane wasu kasakasan ta hanyar yin hakuri, kara yin hakuri, yin uzuri, saurarawa kafin yanke hukunci kin ji aunty?" Marshal ya sake fada a tausashe yana sake sa da dubansa dan irin barin da jikinta ya kwasa kwarai ya nemi bashi mugun tausayi dan gaba daya jikinta ne ya dauki bari kar kar kar kamar ana girgizata
Da karfi ta sake juyowa, kallo na karshe daya ta masa kunnayenta suka ringa gazgata mata lalle shi din ne, shi ne, DODONTA, shi ne azzalumin da ya wulakantar da yarintarta, shi ne ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyarta, shi ne wannan ya koreta da cikin shege, shi ne ya ce ba cikinsa bane, shi dai ne, shi ne, amma me ya kawo shi n
an?

A irin wannan yanayi?

Me hakan yake nufi?

"Nanah, dan girman Allah ki saurareni kafin ki yanke min hukunci.

Ki..."
"Dan girman Allah ne zan ki sauraronka, na kuma roke ka idan ka ba ce a gannina a yanzu ko kai aljanine kar na kuma ganninka a gabana, dan a cikin launin halitun da nake neman tsari da su kaine na biyu bayan shedan, ka yiwa kan ka adalci ka fita a sabgata tun kafin na aikata abinda ban san in zan iya aikata shi ba a duniya HAMIDU!" Aunty amarya ta fada a kausashen balakin da ya saka shi rintse idannuwansa gabansa na dokawa da mugun karfi.

Da sauri ta juyo wajen MARSHAL tana kallonsa ta ce" Ka ga wannan mutumin, ka yi gagawar yi masa iyaka da gidanka, da ahalinka, domin bai san amana ba, bai san kunya ba, bai san tausayi ba, uwa uba bai san tsoron Allah ba, yana da dukkan fuskokin da ka sani na salihai, sannan yana da dukan karin da ka sani na shedani, Wannan da ka gani babu wacce ba zai fadawa ba idan ya samu hanya....."
"Nana!" Aban Ahmad ya fada da karfi yana kafeta da ido
Da wani mugun tsawa ta tare numfashinsa tana tatara dukan tarin rikicin duniya ta ce"
Da wata muguwar tsawa ta tare shi tana tattara dukkan wani tashin hankali na duniya da rikici tana kallonsa ido cikin ido ta ce," Karya na maka?

Azalumi!

Ma ci amana!

Marar tsoron Allah!

Karya na yi maka ne?

Idan ka samu mace a yanzu da ba taka ba ba zaka fa
ata ba?

Babu wacce na cire a gidan nan idan ta janyo ka za ka sakata a lungu ka bata yar alewa idan ta ki ka gurza mata wuka a daf da wuyanta ka amfane ta sannan ka watsar fa ita!, Sai dai ka kula a cikin gidan docter akwai y'arka, wacce na haramta mata kiran ka uba ko a lahira, garin fya
e-fya
en kar ita ma ka bata ajiya ka kuma ce ba na ka bane, Ko da yake in ma hakan ya faru ai tarihi ne ya maimaita kansa, sai ita ma ta raina ta haif.....

"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Allah ashe zan wayi gari na ga irin ranar nan a cikin rayuwata?

Nanah da wadannan kalaman gwara ki saka min wuka ki daba min ita a kirjina ki kashe ni, Nana ina ma kasheni ki ka yi da Wadannan furucin?

Nana na san ni din azalumi ne, na san dukkan abin da ki ka fada dan kin bi ta kansu ne, amma har ya kai ki ha
a ni da y'ata?

Nana ni na yiwa y'ata me?, Nana kuma ki ce za ki shiga tsakanina da y'ata?" Hamid yake fada yana mai fashewa da kuka mai tsananin gaske, kuka irin na namiji, kuka mai karfi, kukan da kana gani ka san ba da gangan yake yi ba ya haka kuma kasa hana kansa yi.

MARSHAL da gabadaya kansa ya na neman tarwatsewa Ya dafe kan nasa da hannayensa bibiyu yana kallon kasa, shin ina zai kai wannan furuci na Aunty Amarya?

Maganar ta masa tsauri a ransa, me yasa zata ha
a y'arta da wannan maganar?

Lalle dukkan tunanin da yake yi abin ya zarce haka,
Mamah kuwa jikinta rawa yake so take ta zaunar da Aunty amarya ko ta ja ta, ta bar wajen ama tirjewa take tana binsa fa mumunan kallon da ido kadai zai gani ya fahimci kallon tsabar tsagwaron kiyaya ne.

Rai a cinkushe ta ce" Kuka?

Hamidu kuka?, Ai yanzu ka fara kuka, sai mun tsaya a gaban ubangiji da mahaifiyata da kai zaka yi kuka, Hamidu yanzu ka fara zubar da hawaye ban kuma san ranar tsayuwarsu ba, na ha
a cewa ka bi y'arka?

Ai aikin mazinaci kenan, yana da haramun ne?

Tun yana fada ya'yan mutane la'ananiyar zuciyarsa zata fara kawata masa Y'ayansa, Hamidu sai ka fada....."
"Ke dan Allah ki yiwa mutane shiru ko ki fice ki tafi bangarenki !" Marshal ya fada a tsawace yana mikewa hannayensa na wani irin jimkewa yana budewa yana kallonta da idannuwansa da suka yi jajajir.

Da kyar ya sake bude idannuwan nasa yana kallon na ta ya ce," An ce ki zauna ki saurara, an ce ki saurari maganar da ake tafe da ita, an nemi alfarma, an san an cutar da ke cuta mai karfin gaske, an san an wulakanta ki, amma kin ki zama kuma kin ki tafiya kin tsaya kina magana tamkar jahila?
Chapter 59 · 0% Book details