← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 110

Sashe 73

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maganar fake matsowa da hira ana daria ya saka shi kafe wajen da ido
Wanda ya hango ya saka shi jin dama ya tashi ya bace bat bata irin na aljani wanda za'a neme shi a rasa,
A irgensa yau kusan sati biyu basu hadu ido da ido da wancen mai zuwan ba, tunda MAMAH ta tashi ta kire shi shi bashida labari ta gana da shi ya tsamtsamta, dan ya tabata maganarsa ne za'a yi, bayan ya yi niyar zai je ya same shi ya fada masa maganar nan kar ya wani kalleta da idannuwan da yake iya kallonta, kar ya masa kallon rushesheshen banza, shi dai ya san ko shi waye, lamari ne na shigar sauri da Mamah da Aba sukai masa, ga ita kanta yarinyar takan bashi tausayi sosai, to shine ya ce a gwada haka ba dan za'a gwada aiki na cikin room na, ko daya wannan aiki bama za'a gwada shi ba ai, kawai a taimaki junna ne a matsayinsu na yan uwan junna, bayan wannan babu wani tunanin ko wani kai kawo a kwakwaluwarsa
Ambulop, irin mai ruwan gold din nan, mai mahaukacin kyau wace akan bugata ne idan ana aure ko taron gidan manya ya mikowa RHISA da suka gaisa sunna dariar yaushe gamo sannan ya ja kujera ya zauna yana fadin" Saura kwana hudu rak ina gayatarka auren y'ata ta fari"
Da mamaki yana zarro ido ya ce" Wauh masha Allah masha Allah Elhaji barka barka, toh wannan abu rana daya da bikin gidan Oga ai, kai ina murna ina murna walahi, yaren yanzu ka haifi abinka har aka taso ka wanke ka mika dakin miji ai an yi mai wuyar an riga an gama mai wuyar sai murna"
Yana dariar ya sake rike hannunsa da ya bashi ya ce" Bari, bari , tunda safe ka ganni nan yawon rabawa nake yi, na kuma baza yarana lungu lungu rabo kawai muke yi, sai jiya katinan suka iso ne shi yasa abin bai samu fita da wuri ba, ishirwama nake ji kamar na kifa dan na sha rana,
an nan ko zan samu ruwa?" Ya karashe yana juyawa wajen MARSHAL dake kallon kasa yana sauraron hirarsu tamkar ya buga , kati?

Kati?

Yo wai wace irin kati?

Abinda yanzu anma daina yayin haka?

Dagowa ya yi yana sauke masa kallo, wai D'an nan, ya kuma maze yana kallonsa, dukkan alamu na neman tashin hankali sun bayana a fuskarsa
Bai ce masa komai ba, katin dake hannun RHISA ya warta ya farke ya bude rubutun cikin
Babu wani kwaramniya kawai gayatar aka rubuta sunnayen ma'auratan, watau MARSHAL SULAIMANE AHMAD SULAIMANA, da FATIMA ZAHRAH.....

Dagowa ya yi ya zuba masa ido, shima shi din yake kallo, irin Aban Ahmad zai nuna masa iyakarsa, to menene na bazawarnan fisabililahi shi da ya so sai an tashi daurawa kowama ya ji?

Mikewa ya yi ya masa kikam yace" Tashi mu je"
Aban Ahmad ya dan kalle shi ya ce" Daga zuwana ko ruwa fa ban sha ba"
MARSHAL ya amshi takardun hannunsa ya ce" Mu je na siya maka a hanya"
Aban Ahmad ya mike yana kade babar rigarsa ya ce" To ai shikenan dama ina son cin shawarma, ama dan bani wata dan gaskiya ba zan yi gaya guda ban gayaci RHISA ba "
A hannunsa ya sake jan guda ya mikawa RHISA dake ta son sai ya gane me yake faruwa, dan idan ka ga MARSHAL na haka tabas akoy wata a kasa
Hanya suka kama suka tafi , a motar Aban Ahmad din suka shige bayan motar su biyun bayan ya ba direbansa ky din tasa motar , direban Aban AHMAD ya ja bayan ya sanar masa inda zai kaisu watau gidan Docto
Da farko shiru ne ya dan ratsa motar, daga baya Aban AHMAD ya shiga dodoka waya yana ta sake gayarsa hankali kwonce, muryar nan tasa zaka rantse ba shine ya yi rashin lafia da yar murya ba, har dai ya kaishi bango ya warce wayar yana hararansa ya ce" Wai meye haka?

Du ka bi ka yayatani Fisabililahi meye wai, ka dai san dai umarnin Abah ne ko?

Kuma ka san dai ba da wani niya a raina a kan maganar nan ko?

Kamar wanda kake jirana sai abubuwa kake min, ka san dai ina cikin masu fadan a daina aurar da yara da kannanun shekaru har a gidan redio ko?

Toh sai ka maida hankali"
Aban Ahmad ya yatsina fuska ya ce" Lalle, na ce lalle, kai ka manta ni sirikinka ne?

To me kake nufi da ba abinda nake tunani bane da me aka ce ka yi?

Malan ka ga kawai ka ringa tausasawa in zaka min magana uban Zahra'u nake a ringa tunawa,, ah to, fadarka ta kar a aurar da yarinya mai shekara ashirin kuma ai fadarka ce kawai, yan gidan redionma dan a sauraresu suke kallonka ka fada su yi murmushi, ama sun san ai ba komai bane karatu ne a waje, nawa mutun mu biya na kaiwa Excelency mana Takardar?"
MARSHAL ya yi masa shiru ya ki bashi wayar kuma yana ta cika yana batsewa har suka karaso anguwar
Tunda suka doso get din Aban AHMAD ya ce da direban ya dakata, nesa da wata bishiya kadan Zahrah ce tsaye nesa kadan da Hasan kanta a kasa Hasan din na ta yin magana ama ita kanta dai a kasa yake dai bata dago ba
Dan muryarsa ya daga kadan ya ce" Fatina?"
Da sauri ta dago kanta, haka shima da bai ganta ba ya juyo barin ya zuba mata ido da wanda yake tsaye a gefenta
Murmushi ne ya subuce mata a saman fuskarta, ba zata iya musalta bakon yannayin nan ba, bama zata iya kwatanta irin yadda yake bako a duniyarta ba,
Ta rasa a wace duniyar take idan tana kallonsa, sai ta rasa me take ji idan ya kireta da sunna fatinsa
Idan yana mata magana yana murmushi kuwa sai ta ji tamkar zata summa dan dadi, wai itama uba ne da ita ba yayan mahaifiyar Aunty bane ashe, kuma yana sonta wai?

Kai rayuwa tana cike da tashin hankali da kuma kwonci hankali
Budewa ya yi ya fita a motar yana ta zuba mata murmushi , itama sai kawai ta doso shin tana ta murmushi bayan ta sanarwa Hasan mahaifinta ne shima ya taho fuskar nan tasa ta yi jajajir na tashin hankalin abinda yake ciki da ita dan gaba daya ta ki shi, ta nuna ba zata iya ja da maganar Mama ba ya yi hakuri, a yanzunma Maman ce ta bata damar fitowa ta masa salamar karshe dan ta sanar mata duk rintsi ta salameshi da dadadan kalamai ta kuma bashi hakuri, shine fa yake ta jan maganar kan ba zai iya hakuri ba zai je ya rarashi mahaifinsa a zo a nema masa aurenta
Gaisawa suka yi sosai, sunna cikin gaisawar Motar ta tashi ta shige ciki, hakan ya saka Aban Ahmad sakin murmushi yana dauke kansa ya fuskanci Hasan sosai ya sake bashi hakuri da baki a kan maganar, yai masa nuni cewar tunda maganar ta fara zuwa da haka a yi hakurin shi ya fi alkhairi
Ba dadin fuska da zuciya Hasan ya tafi, su kuwa suka jero sunna tafe shi da y'arsa yana ta faman mata fira tana daria kamar ba Zahrah ba, yo ita a yanzu duniyar gaskiya tai mata dadi, batama san yaya zata kwatanta ba sai hamdallah kawai
Wajen motarsa suka nufa ya bude bayan ya ringa fitar da ledoji ya sakata kaiwa falo wajen Mama, ta ringa jida tana kaiwa tana dawowa tana sake kwasa har ta gama ta zauna tana sanarwa Mamah ai Abanta ne, MAMAH ta shiga salalami daidai ya shigo ta ce" Kai kuwa Aban docto wannan dawainiya wai ina zaka da ita, yau kusan sati kulun sai la shigo da abubuwa haka ake yi ne wai?

Ledojin nan fa?"
Yana murmushi ya gaishe da Mama ya zauna yana amsar ruwan da ZAHRA ta kawo masa ya ce" Kai Mama, ba fa wani abu bane dan kayan fita biki ne na amso masu ita da yan uwanta, bafa wasu kaya masu yawa bane Mamah"
Ita dai Mama sai fadan hakan yake, sai daga bisani ta ringa saka albarka tana ta Godiya sannan ta saka Zahran kirawo su Rukaya suka bude kayan a nan, dan wanda ya kawi ya ji dadi ya kuma ga an yaba
Shi kuwa murmushi kawai yake yi yana jin idannuwansa sunna ta cika da kwallar farin ciki idan yana gannin dariar ZAHRA, bai san irin nutsuwar da zuciyarsa take ciki a kan lamarin y'ar tasa ba, shi ya sani dole zai sake nin'ninka ibadarsa dan ya yi ta godewa mahalicinsa , dan kuwa ya sani y'arsa ta yi dacen miji, Allah ya wanketa ita ya bata, ina kuma fatan Allah ya yafe masa wannan cin zali da ya yi a rayuwa
Sun dan jima da Maman ya mike ya tafi bangaren Babangida
Yana shiga ya tarda shi yana kallon Ball,
Zama ya yi yana fadin" Allah mai alheri, yara da kyar na raba malan?
Chapter 73 · 0% Book details