← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 110

Sashe 61

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana uku
A tsakanin kwanakin nan, Aban Ahmad jinya yake yi sosai, domin hawan jini ne da shi irin mai hadasa ciwon kan nan, baban tashin hankalin da ya fahimci yana tunkaro shi ko yace yana ciki tsundum ya daga masa hankali fiye da tunanin bawa har ya gaza hadiyewa ya kwonta rashin lafiya mai zafi wace ta daga hankalin Matarsa har suka koma asibiti ya yi kwana biyu sannan ya ki zaman asibitin suka dawo gida yake shan maganinsa yana fatan samun lafiya ya koma bakin abinda ya gigita shi
Su Mama sun yi kira, dan ba halin fita yanzu, basu fita daga takaba ba, ama MARSHAL koda yaushe yana gidan kafin ya wuce gida, wani lokacin yakan kwana a gidansa ne dan ya cika dare sosai
Yau da ya cika kwana hudu da jinya, ya kasance ya samu ya fito filin gidansa yana zaune yana dan shan Lipton din larabawa da matarsa ta dafa ta kawo masa
Waje daya ya kurawa ido, tunanin fuskarta, da magangannunta, da kalaman nan biyu na yadda take neman tsari da shedan haka take nema da shi, da kuma kalmar nan na...na y'arsa sunna neman kaishi kabarinsa ne suka hadasa masa zubar kwallah har bai san cewa matarsa ta fito dauke da ruwa ruwan dahuwar anta da ta sha kayan hadi ba magi ko diss dan lafiyarsa tana ta kama sunnansa a sanyaye ama shiru har sai da ta dan taba hannun nasa ne ya dago a dan zabure ya kalleta, lokaci guda ya shiga share fuskarsa yana son nuna ba komai dan a kan damuwar nan shi kadai ya san irin halin da matar tasa take shiga a kulun
Zama ta yi tana dafe kanta da hannunta guda
A sanyaye, muryarta da rauni sosai ta ce" Ya dace ka sanyayawa kanka haka Aban Ahmad, Hawan jini fa cuta ce mai karya garkuwar jiki, ya dace dukkan abinda aka hanna ka kwatanta kiyayewa Aban Ahmad"
Idannuwansa kawai ya dan lumshe, a hankali ya ce" In sha Allah zan kiyaye "
Ajiyar zuciya ta sauke du bata gamsu da fadar tasa ba , dan bashi da alamun aikata abinda ya fadan, ta ce" Ai inaga wahalar da sauki ko Aban AHMAD?

Allah ya takaita tunda aka ganta a kusa, dama dole ta yi fushi Aban AHMAD, ama na tabata zata yafe maka ka ji?"
Idannuwansa ya sake budewa yana kallonta, yana matukar son jin kalamanta cewar zata yafe masa, sai dai jim dadin baya yin tsayi sai ya katse, dan sai ya ga ta yaya?

A sanyaye ya ce" Ba fushi bane ta yi da ni, tsanata ne ta yi ai Ummu Ahmad, kuma kin ga da wahala ta yarda yarinyata ta san da ni......."
Kakafeshi kawai ta yi da ido, sai take son yi masa tambaya tana kuma jin tsoro, da kyar dai ta iya fadin" Aban Ahmad, na tambayeka mana?"
Idannuwansa ya dan mata alaamun ta tambaye shi, dan haka ta ce" Abaan Ahmad, damuwarka yafiyar tata ne kadai, ko tsanar da ta maka na taba maka zuciya?"
Ido ya tsureta da shi, bai san me zai ce mata ba, kwarai ya san zafin kishinta a kansa, ama kuma yana tunanin zata fi kowa sannin me yake ciki, idanma akoy maganar da take hasashe zai iya cewa ba its ta fi daga masa hankali a yanzu ba
Kai kawai ya girgiza ya dauke kansa, dan baya cikin yannayi na fitina ko daya
Ajiyar zuciya ta sauke ta mike dan zuwa ta idasa aiyukan dake gabanta
Tana shiga ta dauki wayarta ta zauna bakin gado ta shiga lalubar numbar MARSHAL
Ta taki Sa'a a ranar ya taho da kansa gida dan cin abincin rana, domin Amir ya tafi aiki tunda safe , shi kuwa bai cika saka ma'aikatansa a harkar abincinsa ba
A nutse ta gaishe shi bayan ya amsa salamarta
A tausashe ta ce" Baban Docter, dama cewa na yi dan Allah idan da hali tunda ina nan a samu a kawo y'ar ta wajen Abu Docter ta gaishe shi, ko zai dan sake kwontar da hankalinsa, ka san abin na damunsa sosai baya sauraron komai a yanzu sai maganar, likita kuwa yace a ringa kamanta kwontar masa da hankali ta haka jinninsa zai dawo normal"
Motar ya rufe bayan ya fita ya dan tsaya dan ya gama wayar
Da kula ya ce" Jikin nasa ne Maman Docter?"
Kai ta girgiza tana fadin" Aa da sauki, sai dai ka san maganar yake yawan tunani a kai, dan sai a yi ta hiratarsa baima sani ba yana tunani"
Agogon hannunsa ya dan duba, da kula ya ce" in sha Allah, idan na zo yau ma gani abinda ya dace, a gaishe shi"
Daga haka ya katse kiran hankali kwonce ya nufi bangaren Mamah yana yawan gaisawa da du wanda ya hadu da shi a hanya har ya saka hannunsa ya bude falon ya shiga yana kai dubansa inda yake jin ihu da daria
Ihu Auta ke yi tana saukowa a guje, itama tana buye da ita tana fadin" Allah baki isa ba, Aunty adawiya, Aunty Adawiya kin ga Auta ko?

Walahi ba zaki daukar min rigata ba yarinya an fada maki bana so ne?

Dan ta min kadan ai ga yar uwarta nan ina iya sakawa na yi barci, zo maza bani rigata, saima da kika zabi bak'ar bayan kin san na fi son bak'a ?"
Da karfi ya rike kofar da ya shigo yake niyar mayarwa ya rufe
Taga taga ya yi sakamakon kaffafuwansa da suka so daukar rawa su maka shi da kasa
A hankali makoloton wuyansa ya yi sama ya yi kasa daga cikin wuyan nasa ya iya fitar da dan nishi mai hade da kukan kato kadan ya fitar da sauti kamar haka" Huuuuuuummmn"
Idannuwansa ne suka sake zaunawa a kanta, har zuwa suturar dake jikinta watau riga yar karamar da ta dangale ta yi sama har dan cinyoyinta na neman bayana sanadiyar halitar da Allah ya yi mata yar daidai da ajikinta , rigar ruwan madara ce mai sirririn hannaye, sannan mai lafewa a jiki ce dan harta shatin pant dinta ya fito, watau idasa hada kaya suke ita da auta suka fitar da kayan kaya ne na barci da ake saya masu Auta tace ai wadinnan sun ma Zahran kadan yanzu, ita kuma tace aa ta bara mata abinta dama ai ba fita suke yi da su ba na barci ne, shine Auta tace ina ai wannan ko barci sun yi kadan, ita kuma ta kiya karshema ta saka daya dan ta gwada mata ba wani kadan tunda basu ki kaiwa cinyarta ba tana iya barci da kayanta, gardama dai ta sarke, suke kewaye dakin suka yiwo waje, ta biyota a guje dan amshe rigarta ne kuma sun san ba wani kato dake shigowa a irin lokacin nan ai, uwa uba ba zasu taba kawowa Babangida zai zo gidan warhaka ba, Mamah kuwa tana bangaren da zasu kaura ita da Aunty amarya sunna idasa gyara dan tace gobe za'a gama kwashe komai, hakan ya suka nufo falon kasa auta na ihun ba zata bayar ba, Zahra na ihun sai ta bata rigarta gudu irin na garaje da rigar nan jama'a dan rashin kunya?

A lokacin ne kuma Babangida ya samu shigowa dan daukan abincinsa, abincinsa kadai ya kawo shi gidan nan jama'a abinci kawai ya tarar da wannan abu
Ido Auta ta fara zarrowa cin karro da Babangida a falon jikin kofar kamar yana jingine dai kamar yana make, hakan ya sa ta ci birki har Zahra ta karaso ta gwarun mata tana warce rigarta ta budi baki zata yi magana itama ta ga abinda Auta ta gani
A guje Auta ta juya tana sake bin matatakalar hadi da haddawa bibiyu, uku-uku tana gannin kamar an karawa wajen nisa
Rigar ta saki itama, kirjinta ya ringa sama yana kasaa dan firgici sannan ta juya ta auna a guje ta sake juyo bayanta tana hawa maza na tsaye sunna kallonta kamar an dasa su a wajen an kuma saka su kallon haramun dinsu jama'a
Sai da ta bacewa ganninsa yana kallon matatakalar har idannuwansa suka ringa hade masa ganninsa sannan ya iya rufe idannuwansa da alamun lumshewa , lokaci daya ya bude ya ringa lalubawa har ya kama abin budewa ya bude kofar ya fita ba tare da ya dauki abincin nasa ba, baima tuna da yinwar da yake ji ba, har sai da ya sada kansa da motar nan ya bude ya shiga ya rufe ya shiga neman ky din motar wanda yake jikin yar yatsarsa, da kyan kunnayensa suka jiyo masa kukan ky din sanadiyar motsa hannun nasa da yake yi y cire ya saka ya kunna motar sannan ya shiga tunanin inda zai je
Motar ya tayar ya fice a gidan ya karasa wajen cin abinci daga cikin motar ya yi odar pizza da jus Ira sannan ya gyara kujerar ya kai hannunsa wsjyen habarsa ya dan shafa a hankali ya sake kure hanyar kawo masa abincin sai kuma ya dawo da dubansa kawa kawa wajen wandonsa cike da takaici da matsanancin mamakin irin yadda jikinsa ke neman hautsinewa a kan abinda ya ki yarda dan sam lamarin ba wani sence, shirmen banza shirmen wofi ne, kawai an yi wata Sa'a ce an fado a kan lamarinsa ba dai abinda ake tunani bane zai saka shi ciwon mara!

Abokinsa RHISSA ne ya fado a ransa, baki ya sake dantsewa yana ayannawa ransa RHISSA ai dan duniya ne , ba zai yiwu shi da baya saka iskanci a rai , bama hadinsa da abinda ya gannin, a tunaninsa ko tsirara ya ga abin ai bai isa tsinka ba dan ko fure bai yi ba, ama shine zai ga haka?

Baya ciki!
Chapter 61 · 0% Book details