← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 110

Sashe 39

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko me yake faruwa da wannan mutumen halinsa ya rinjaye shi?, Zahra shin kin taba hanna shi zuwa gidan nan neman izinin zance da ke ta yadda za'a san shi a san waye shi?" Adawiya ta fada tana kallonta
Dan tsai ta yi, sannan ta girgiza kai ta ce" Aa, ba'a taba haka ba, dan a lokacin da nace masa zan gabatar da shi wa manyanmu sai yace na dakata akoy wani shiri da yake yi, ya fi so aa ganshi da kimarsa da darajarsa, wai idan ya zo a haka nemansa bashi da karfim da za'a ji ana iya bashi ni, wai gidanmu gidan manya ne ba zasu dauki y'a su ba kowa ba sai idan mutun ya amsa abubuwan da suke da bukata"
Adawiya ta yi murmushi ta ce" Yana dai nufin sai ya yi kudo zai zo?"
Nuriya sai ta rasa amsar da ya dace ta bata a wannan tambayar, sai ta rasama amsar ita da kanta bayan a da tana da ita
Adawiya ta sake yin wani murmushin ta ce" Ama, idan yace yli fito kin taba nuna masa bakya son kina tarda shi bayan layi da sauransu?

"
ZAHRA ta yi saurin kafeta da ido a ranta tana mamakin yaya aka yi ta sani?

Da dan takaici Adawiya ta ce" Bari ki ji kadan daga cikin take taken samarin shaho kennan, dama ba zasu taba yarda a sansu a gidanku ba, kulun zasu kawo wani uzuri nasu marar tsari su gabatar maki dan su ai dama basu zo dan a sansu ba, sun zo dan au yada manufofinsu su yi tafiyarsu ne..............., Zaki ga su kulun cikin son fitar da ke suke yi bayan kin sanar masu bakya so iyayenki basa so, wasunsu akoy kyauta ta gigita zuciya , wasun kuwa yar kyautarma babu sai yaudararun kalaman dake iya saka budurwa bijirewa kowa sai su......Fatima namiji mai sonka yana da lokacinka, an sanshi a gidanku, shi din mai yi maka fada ne, mai yi maka nasiha ne, uwa uba mai tsananin kishinka ne ta yadda ko kasuwa kace zaka je ko gidan biki hankalinsa a tashe yake har yana iya hannawa idan yana da wannan damar domin shi burinsa ya kilaceka aa wasjen da zai ringa baka kulawar da ta dace da kai ba wai ya ringa fitar da kai a kowani yannayi da kowani lokaci ba............., Ki yi kokari ki yi nazari sosai a kaan lamarinsa, in har kin ga du abin nan da na fada maki baa halayansa bane to sai a neme shi a ji damuwarsa, duda neman nasa wani launi ne na zubar maki da kima a idannuwansa dan ya nuna maki baya yi aka nace, sai a ga yadda ya dace, ama maganar su yaya dan ki ji da kyau basa aurawa y'ar cikin gidan nan mutumen banza, basa yarda da haka, yaya Amir ne ke daukan wannan a hannunsa, dama idan har suarayinki kin san ba na Allah bane ki hakura dan bata lokaci ne, sai dai idan binshi zaki yi dan kina tunanin shi kadai ne masoyinki da Mama a duniya kuma toh shawara ta rage taki......"
Daga haka ta daki hannunta a sanyaye ta mike ta fice a dakin ta janyo mata kofar jiki a mace sosai ta nufi dakinta kwonyarta cike da tunani.............mmm
Dama rashin saka yarinyar nan a jiki abinda yake haifar mata kennan?

Tunanin bata da madafa bata da wurin zuwa?

Anya ba sunna cikin masu laifi a wajen Allah a kan lamarin nan kuwa?

Eh lalle su basaa tsangwamarta, ama kuma ya zamto ne tana rayuwa a ware a cikinsu, sam ba a hade suke da ita ba, ko menene ana yi masu tare ne ama kuma kansu ba a hade ba.........shin dama laifinsu ne?, Har take tunanin wai bata da majingina sai a jikin katon da yake bako a rayuwarta? , In sha Allah daga yau zata yi kokarin gannin tun daga kan yayarta har zuwa Auta karama dun cenza mu'amalarsu da ZAHRA, yau koda ZAHRA ta masu wani laifi ai ba tsangwama ne ya dace s yi mata ba, tabas zasu cenza dan kar aje su jazawa kansu sakamakon da ta fi karfinsu a wajen ubangijinsu
Zahra kuwa tunda Adawiya ta fita waje daya ta zubawa ido magangannunta na dawowa a cikin kwakwaluwarta, du idan ta dauko maganarsa dan ta bata mahinmanci sai kawai maganar Adawiya ta zo ta shiga ciki,
Babu ranar da ba zai ce da ita yana so ta tardo shi inda yake ba, shi fa so ya yi daga makaranta ta ringa tarda shi wajensu wai a cewarsa dan abokanansa su santa sosai........., Idan da zata biyewa Ma'awiya ya sha nuna mata abokinsa na aure ta yi satar fita su je diner ba za'a jima a wajen dinern ba, in an jima karfe biyu na dare........, Ta sani cewa babu yadda bata yi da shi ba kan ya gabattar da kansa wajen ABAH ama sai yace mata ta bashi lokaci akoy lokacin da yake jira.........

Gaba daya sai kanta ya cakule tunaninta ya hade waje daya ta rasa madafa ta rasa abinda zata yi tunani a kansa daya tak sai kale kale take tana kulawa da kuncewa a cikin zuciyarta har kiraye kirayen sallar magariba ta gabato hakan ya sa ta lalaba da kyar ta shige bayi ta tara ruwan dumi sosai ta shige ciki ta lumshe idannuwanta tana jin yadda fatarta ke fitar da hucin zafin ruwan ama kuma jikinta yana saki a hankali a hankali har ta ji dadin jikin nata sannan ta daura alwallah ta fito ta saka suturarta doguwar bak'ar riga budafiya mai dan mayafi ta haye salaya ta shuga gabatar da sallah
A nan har ta yi sallar isha'i sannan ta mike ta dake lalubo turarenta ta zauna tana dashinawa a jikinta tana turo baki cike da jin haushin amshe mata turare da aka yi fu bata jin jikinta normal
Juyowa ta yi jin an murda kofar nata an shigo ta sauke dubanta a fuskar Auta dake aukin murmurshi ta ce" Aunty Fati Mama taxe maza mu sauko mu je bangaran Abah ana masa bankwana zasu daga karfe biyu na dare gannin likitansa"
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani iri a zuciyarta na damuwa da rashin lafiyar Aban, haka ya sa ta dauki carbinta kawai ta biyo bayansu suka jero su hudu suka nufi bangaren na ABAH, a zuciyarta tana cike da tunanin yaya aka yi suka yi jiranta?

Ko mamace tace kar ta ga sun zo babu ita?

To ama duda haka yaya aka yi suka jero da ita bayan ko maman tace kar ta ga sun yi tafia babu ita tafiyarsu suke su barta a baya babu mai jiranta bale ya jera da ita har auta?
Chapter 39 · 0% Book details