← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 110

Sashe 10

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana iya bada fili ku daku kai da shi ne kawai in hakan ka fi so, in tsagera kake kama ce masa sai an kuman mana ko ka kuma maimaita abinda ya hanakan, a nan ne zaka gane me ake nufi da baba baba ne
Zama ya yi yana shan ruwa , sannan ya dubi mahaifiyarsa a tausashe ya ce" Momy, yaushe zaki shirya din ne?"
Sai a lokacin ta sake tunawa da maganar,
Baki ta tabe ta ce" Ba inda zan je Amir, ita wani damuwa ta yi da mutane daga iya har danginta?, Ni babu inda zan je rashin lafiya ne Allah ya bata lafiya!"
Kureta ya yi da kallo yana ta tunanin ta inda zai biyo mata
A sanyaye ya ce" Mamah, ki yi hakuri ki jure ki tafi, ba dan komai ba sai dan yaya, Mamah ki yi dominsa, ki faranta ran danki mai faranta maki wanda baya hadaki da kowa, kar ki manta mamah rai ake gaisarwa, kar kuma ki manta shi ya kawota cikinmu, shi din kuma namu ne, bamu da kamarsa, ko da me ta zo mu mun yarda dan wanda ya isa ya kawota kin ji maman Baban gida?"
Sosai take kumbura tana cika tana batsewa, da kyar dai ya samu ya samu kanta har ta sauke ajiyar zuciya ta yarda zata je din, ama wai sai zuwan rana
Shi dai a haka ya fice yana jiran yan matan har suka sauko suka yiwa Mama salama kowace sanye da nikaf dinta da saffar kafa da zumbula zumbulam hijabansu suka karasa suka shige motar ya dauki hanya yana kallon inda ya saka a kimar masa shegen mai gadin nan dake bata hanya, domin a jiya tana tafe kamar Yar maye yana biye da ita a kafa, dan tunda ta fito daga motar nan shi kuma ya shanyo kwana ya daleta da fitila sai ya labe ya bar motar ya sauko a kafa ya rakota har fitar yayansa a kan idannuwansa, dalilin da ya sa ya kwana a gidanma dan sai da ya yi dan bincikensa a kan masu tsaron kofar gidan
Tukin garari ya yi da su a hanya har ya sada su da kofar makarantarsu mai hade da Islamiya ya ja birki da garaje ya juyo yana nuno su da yatsarsa ya ce" A cikinku wace bata dauki gargadin da na yi mata da kunnen basira ba dan Allah ta sake mayar da hankali wajen aikata laifin da na hannata, in sha Allah zamu baje kolin rashin ji kowa ya dauki kasonsa!"
Su dai basu ce komai ba, Allah Allah suke yi su bar masa wajen kowace ta fice da sauri ta shige ciki
Ajiyar zuciya ya sauke a ransa yana ayyana ' Allah dan girmanka ka kare mana su, ka tsare mana mutuncinsu, ka sa mu yi masu aure mu mika su dakunnansu cikin mutunci, ya ubangiji idan da wata mai mumunar kadara a cikinsu ka cenzata zuwa kyakyawa alfarmar annabi da Alkur'ani.....'
Sai kuma ya tayar da motar ya nufi asibiti, daga cen zai wuce office dan ya san da wahala yau Mar
chal ya samu dogon zama a asibitin
Jiki ba karfi suke tafe daya na bin daya a bayanta har suka karaso wajen da zasu rarabu
Babar cikinsu ce ta ce" Ke Zahrah zo nan"
Dakatawa ta yi da tafiyar da take ta juyo, idannuwanta suka sauka a kan Furera wace yau basu yi mota daya ba, kennan basu dambatu yau ba
A tausashe, sai dai amon muryarta da dan zafi ta ce" Kin ga abinda zan fada maki a kan maganar wannan saurayin naki shine ki raba kanki da wahala, bana son abinda zaki kuma janyo mana ko barcin asubahi bai sake mu ba a ringa kwalo da mu kamar gangunna, ke gaki da taurin rai ko kasheki za'a yi ba zaki yi magana ba, to walahi mu dai bama so kin ji na fada maki, kar na kuma jin wai ya neme ki har kin amsa shi dan miji goma ba uba goma bane, bale kuma saurayi goma ba uba goma bane , ki rufawa kanki asiri Allah ya fitar maki da miji ki yi tafiyarki dakinki salim alim , kar ki ja mana Baban gida ya dube mu a kan rashin jinmu!"
"Wani abu ta aikata ta ja maku duka ne?" Furera ta tambaya tana sake matso su harda rike tsatso tana kallonsu
Da sauri Ummi ta kalleta ta dauke kai, a gaskiya sun kasance basa jituwa a tsakaninsu a cikin bangarensu, ama rashin jin Furera ya yi kamari, irin abinda take yiwa ZAHRAH ya yi yawa sosai
Fuska auntynsu ta hade ta raba ta shige gaba daya makarantar ta dauki hanyar ajinsu ba tare da ta ba Furera amsa ba, dan bata son maganar ta yi tsayi, ita kuma furera kishinta a kan Fatima ya kare, su kam ba zasu wuce gona da iri irin haka ba, Mamah ba zata taba barinsu su aikata abu irin haka ba
Kallon kallo suke yiwa junna ta cikin nikaf din, sai kuma Furera ta yi wani murmushin raini tana fadin" Dan bani hanya mana na shige malama kin wani gajen hanya kamar kina da iko da ita"
Bata ce mata komai ba, sannan bara matsa a lokacin ba sai da ta yi niya dan kanta ta juya ta shige itama ta nufi nasu ajin tana jin irin yadda karamar wayarta ke giiiigiiiii alamun kira na shikowa ama ta yi banza da ita ta shige ta zauna ta sada kai ita daya a cikin aji tun kafin kowa ya shigo
Mintunnanta uku da yan dakiku ta ji an janyo kujera an zauna a gefenta, lokaci daya aka nemi kama nikaf dinta da muryar wace ko bata dago ba dama ta san itace zata yi mata haka ta ce" Yan mata yau kece farkon zuwa ko lafiya?"
A hankali ta saka hannunta tana rike nikaf din da ta so dagawa kasa kasa ta ce"
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_7_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
A hankali ta saka hannunta tana rike nikaf din da ta so dagawa, kasa kasa ta ce" Ke kar ki cire mana, kin zo kuma zaki fara ko?"
Muryarta ta sakata dan zuba mata ido, a hankali ta ce" Kamar kin yi kuka ?"
Idannuwanta da bata son dagowa ta sake kin dagowar, yanzuma ta ce" Wai ina daliban ne?

Yau malan ba zai zo da wuri bane?"
"Me yake damunki ne?

Ina magana kina zilewa?

Gashi har kin manta yau bamu da karatu da safe kwata kwata sai da yama na islamiya?, Muma mun zo ne dan yau mune da Shara ko kin manta?" Ta fada mata da dan mamaki tana kallonta
Sai a yanzu ta dago idannuwantada sukai mata nauyi tana kallonta, sai kuma ta dafe gabam goshinta wanda shima ke dauke da shatin bulala, dan Walahi sun daku iya dakuwa ta ce" Ya Allah, kin ga na sha'afa, kwata kwata na manta, islamiyarma kin mamta wa'inda basu kawo harda kadai bane akace su zo?

Mu ai mun kawo malan Habibulah yace kar mu zo yana so ya ware wa'inda basu da niyar sake yin sauka ko?"
Hannunta ta riko da sauri tana jan hijabinta tana zarro ido ta ce" ke menene wannan?

Meye a jikinki haka?"
Sai kuma ta warce nikaf din nata , ai bata shirya ba ta sake mikewa tana magana hadi da fashewa da kuka, dama ita mutun ce mai saurin kuka, bale fuskar Zahrah ta tsoratar da ita ainun, a rikice ta ce" Innalilahi, Fatima menene a fuskarki?

Dukanki aka yi ne?
Chapter 10 · 0% Book details