Sashe 24
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ga da mun fito mun dan tsaya muna samu a cen gefen?"
A dan daburce Zahra na waigen hagu da dama ta ce" Mu dan tsalaka ta cen baya mana sai mu samu a nan yanzun sunna wahalar samuwa Aisha"
Binta Aishan ta yi tana bin jakar dake cikin hijabinta da kallo har suka karasa inda Zahran ta amsa waya ta yi nesa kadan da Aishan ta yi magana sannan ta dawo ta shiga tsayarwa Aisha dan sahu har suka samu ta shiga suka yi salama Aishan ta tafi ita kuma ta zuba ido tana ta faman boye fuskarta dan kar a ganeta a hanyar
Ta dauki dan lokaci sai gashi da babur dinsa sai hayaki yake yi, yana zuwa ya faka a gabanta cikin gagawa da yannayi irin na munafuki ya ce" Hau yi sauri, kema da nace maki ta cen baya zaki ce wai malaminku na islamiya a nan yake zama kennan harma tsoron wani dan iska kike yi a duniya ko fatina?, hau mu je yi gaggawa mana kin ji?"
Tunanin ta yadda zata dane babur din take yi, da sauri ta ja hijabinta kafarta dauke da safa ta karkace kadan tana shirin hawa idannuwanta suka sauka a gefen titin da ta tsalako a kan fuskar Yah Amir ya harde hannayensa yana yi mata kallon da sai da hanjin cikinta suka cenza wajen zama dan rikicewa
"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, innalilahi wa inna ilaihi raj'une wayo mun shiga uku" ta fada da karfi tana cakumar rigar dake jikinsa hadi da cikinsa ta ja da karfi ta furta " Mun mutu yaya Amir ne mun mutu!"
Shima sai da ya ji dan fitsarin dake kan abinnan dinsa fitowa a jikin wandon jins din dake jikinsa ya bata masa wando, a haukace ya shiga waige waige daidai lokacin da bus din dake dauke da sojojin da zasu cenji wa'inda suka yi wata a gidan ta zo wucewa, hakan ya sakata sauka a haukace ta ce" Walahi ka gudu, ka gudu idan ya rike ka sai ya kusan kasheka ka gudu!"
A haukace ta juya ta shiga falawa da gudun balaki hijabinta na yin sam tana hailala da ambaton sunnan Allah gaba daya ta watsar da takalmin da jakar a hanya, shima ya buga babur din a haukace ya matsa shi ya yi gaba yana wani irin gudu kamar zai tashi sama hankalinsa tashe yana ambaton Allah ya taimake shi kar ya kama shi, domin idan har ya kama shi ya sani ya mutu din da tace ba karya take yi ba
A guje ya so binsa, sai dai gannin ya dan yi nisa shi kuma a kafa yake dama daga gudu ya fito duda ba kayan sport bane a jikinsa haka ya taho a dan guje yana jin dadin yannayin yamacin yana hira fa abar kaunarsa
Da sauri ya ciro karamar wayarsa ya yi kiran sojojin dake gaba da shi ya sheda masu yannayinsa suturar jikinsa, babur dinsa ya bada umarnin a kama masa shi, du su sanarwa na hanyar a rike nasa shi sannan ya juya ya fala da gudu yana cire belt din wandon dake jikinsa ya mara mata baya a lokacin tuni ta shige gida ta durfafi bangarensu kwata kwata ta manta cewar zata kaiwa Zaki ajiyar nama ne
Dakin ta fada a guje, salalaminta da ihunta ya saka Mama mikewa tsaye a haukace tana rikota, da gudu ta fala bayan Maman tana ihu tana kuka jikinta na bari tana nuna hanyar shigowa dan ta sani ne yau sai ta yabawa aya zakinta a hannun yayansu , sai ya yi gunduwa gunduwa da namanta sai dai kawai Allah ya jikanta walahi!
Mama kuwa hankali tashe take tambayarta lafiya?
Har sai da Amir ya shigo da farko da gargagi, gannin yayansu ya saka shi daidaituwa ya yi salama, ya dan matsa gaba kadan dan kar ya yi masa ihu a kai sannan ya shiga bayani rai bace yana tambayar me kennan?
Yana nuno jakar hannunsa da takalmanta
Tabas bata taba gannin bacin ransa irin na yau ba, tunda ya shigo ya zazaga masifa , ya zazage suturar dake cikin jakarta da wayarta yana nunawa Mama wace ta ji tamkar juwa zata kwasheta ta bugata da kasa ta juyo tana kallonta hankali tashe, fuskarta na nuni da tsantsar bacin rai , amon muryarta a sanyaye ainun ta ce" Zahra, kennan dai tunda ba ni na haife ki ba, ba zan taba samun girmamawa da daranjatawa irin na uwa da y'a daga gareki ba?
Zahra dan ban haife ki bane ban isa ki dauki maganana da mahinmanci ba?
Fatima dan ba ni na haife ki bane kike son bacin raina ido rufe?, Me na maki da zafi ne?
Me na aikata maki na kiyaya haka ne?, Me yasa ba zaki yi min adalci bane?, So kike karfi da yaji sai kin wulakantar da kanki ne Zahra?
Ko Allah ne ya yi sai kin wulakantar da kan naki dole?, Haba zahra, kaunar da nake nuna maki bata isa ta hannaki bin kato ba?
Me zai baki?
Ko ya riga ya lalata maki rayuwa ne ban sani ba Zahra???????"
A hankali ya rintse idannuwansa da suke dan bude yana kallon kaffafuwanta yana sauraron fadan mamanta, sai kuma ya nemi mikewa dan ya basu waje, ama yannayin maman nata na neman taba masa zuciya, ta yadda a dole ya ji sai ya tsaya ya dan yiwa yarinyar nasiha saboda ta daina, baya son damuwa , babu abinda ya hada shi da ita, ama tana dauke da zuciyar zuciyarsa ne, tana son yin wasa ........
Zai iya rantsewa bai taba gannin Mama a halin tabuwar zuciya irin wannan ba, ga kuma kuka da ihun da yarinyar nan ke yi tamkar zata fasa masa kunne yanzu ta koma wani irin gunjin kuka tana rungumar jikin Mamanta ita kuma maman nata tana tureta hankali tashe
Sake cire hannunta Mamah ta yi ta dauki takardun da Ya kawo mata a sanyaye ta ce" Baba zan shige ciki kaina na yin ciwo, mun gode Baba Allah ubangiji ya saka da alkhairi ya biya, Allah ya rufa asiri ya karra kareka Baban gida mun gode sosai....."
Idannuwansa ya bude ya zubawa Mama har ta gama maganar tana mayar da kwalar idannuwanta ta juya ta nufi sama tana sauri dan walahi yau ba zata hanna jikin y'ar cen ya daku ba, idan ya so kuma ta yi da gaske dan ta kula idan ta yi wasa dan hakin da ta raina na iya tsole mata ido , samarin zamani na iya sakata kuka da idannuwanta
Sosai yake son janta dan su bar gaban Baban gida, sai dai ya kula ba zata bishi ba, hakan ya sa ya zuba mata Belt din nan ta yadda ya lauyo mata ya sha kaffafuwanta da karfi ya bada sauti a jikinta pattt
Ihu ta saka ta tatare hijabin ta cire gaba daya tana kallon Hanyar da Mama ta bi da karfi ta ce" Mamah, mamah dan Allah kar ki barni da shi Mamah, mamahna dan Allah ki saurareni Mamah wayo mamana zai kashe maki ni........."
Wata ya kuma zuba mata, wannan karron a dole ta kai kasa ta karasa ta zube sama kaffafuwan Baban gida dake zaune yana kallon hanyar shigowa gannin sumui sumui sai ficewa sauran yan matan suke yi da saurin gaske dan ba zasu zauna shafi ta shafe su ba harta wace ke kicin ji take kamar zata saki fitsari a sket dinta
Kafarsa ya janye a hankali ya zubawa belt din hannun Amir ido ita kuma ta ja baya tana malolowa kamar zata mutu
A nutse ya mika masa hannu dan ya bashi Belt din, hakan da ta ganni ya sakata zarro ido da rarafe ta koma gefe sai hannu take cusawa cikin zanninta tana susa , kaffafuwanta kuwa har wajen kaurinta ta yaye sket dinta tana ta susa, yau kam da zani ne ta yiwu ta cire shi ta yar
Belt din ya dan lankwasa sannan ya dago ya kalle shi ya ce" Fata ce?"
Amir dake ta cika yana batsewa ya zubawa yayansu ido, har ga Allah sai ya rasa me yasa ya tambayeshi in fata ce ko ba fata ba?
A hankali ya amsa shi cewar fata ce , hakan ya saka shi yin dan jim sannan ya mike ya miko masa Belt din
Hannu ya saka zai amsa sai ya ga ya rike, ya dan ja ya ga bai saki ba hakan ya saka ya zubawa fuskarsa ido
Wani kallo ne da ya kasa gane fasararsa, har sai da suka yi ido cikin idon nan sannan a hankali ya ce" Shi yaron yana ina?"
Amir ya ja numfashin takaicin Zahra, yanzu ta sa jiya ta fito daga asibiti yau zai mayar da ita?
Wannan wani irin hali ne?
Dan ya tabata yau duka zai kwana yana yi mata, wannan ai ba adalci bane, Yaron ko tsari babu tana amsar bulala haka a kansa?
Shirmen banza da wofi
Da respect ya ce" Na saka masu control na hanyar da zai iya bi su tare min shi, du inda yake yanzu yana hannunsu....."
"Idan fa ya bi ta wata hanyar?" Ya fada yana mai tare numfashinsa, hakan ya saka shi yin jim sai kuma ya ciro wayarsa yana fadin" Bara na kirasu na ji Sir......"
"Aa ka je, zai fi" ya sake fada a tausashe yana sake zubawa belt din ido ya dan cire yana dantse lebensa na kasa
Dan shiru Amir ya yi, to yaya dukan kennan?