← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 110

Sashe 15

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A yanke kawai menene a ciki kuma?,
Dan murmushi ya yiwa Mama a hankali ya ce" Du abinda kika yanke zan yi biyaya, kuma a nan zan ci abincin rana, na tafi Mamah "
Ya wuce ba tare da ya sake jiran jin wata maganar ba
Mamah rasa me zata fasarta wannan lamari ta yi, jiki ba karfi ta dawo ta zauna a sanyaye ta ce" Hajia, ku yi hakuri dan Allah......"
Hajia bata tsaya ta ji karashen maganar Mama ba murya na rawa ta fashe da kula tana sada kanta irin abu na sukartan nan ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Hajia dan girman Allah kar ku ce mana aa, mun zauna mun yi shawara ya fi a irga, kin ga dai yarinyar nan shekararta tara tana zawarci, run yana da shekara ashirin da shida shida take gida , yayanta biyu yan mata daga su bata sake wani auren ba bale ta haihu, ta kama mutuncin kanta tana sana'arta, a kulun kulanta shine ba zata sake aure ba dan tana tsoron lamarin mazan zamani, tana tsoron ta tashi ta ba wani namiji yarda ya wulakanta ta, a yau da yar uwarta ta rasu na kawo mata maganar nan ta sha kuka, daga karshe ta gane lalle inafa gaskiya babu dan mutuncin da zai riketa irin MAR
CHAL, HAJIA ku taimaka ku mana rai ku amshi tayin nan yar uwarta ta maye gurbinta su yi zamansu lafiya...."
Gaba daya ji Mama ta yi gwuiwarta ta sake sacewa, sosai lamarin take jin shi wani iri
A nutse ta ce" Ba nufina ku yi hakuri hakan ba zai yiwu ba fa Hajia, nufina ku yi hakuri har a raraka, gani na yi yaushema Allah ya amshi Manal? , Bayan wannan kin sani sarai a hausa ba mace take da iko da
anta ba, yaron nan da mahaifinsa mai tsaye a kan ra'ayin kansa, inaga ku bani lokaci na same shi, abinda yace in sha Allah sai na sanar maku ta waya"...........

A gaskiya ba haka suka so ba, so suka yi Mama na jin haka ta hhaye ta zauna kan maganar harma ta fi su nuna farin cikinta, ama a yanzu sai suke jin wata shaka shaka ta afkawa abin kai tsayen da suka yi, da sun sani da sai sun fara samun kansa sannan su kawo maganar
Kuma Allah yana gani maganar bama ta Maman su manal din bace ta yayar tata ce, ta nuna mata cewar idan fa ya kubuce masu shikenan, dukkan wani jin dadi da farin ciki da gata da isa da suke da shi a da zai zama babu tunda wadda ta hada ta mutu
Wannan dalilin ya sa ta zabura ta nemi ganawa da Maman da kuma Mar
chal din, sai gashi ta gani gannin idannuwanta cewa Mama ba kanwar lasa bace kamar yadda y'arta ke ce mata bata so su shigi junna da Mama dan walahi d'anta na yi mata biyaya fiye da tunanin mai karatu, babu wanda ya isa ya saka shi abu kai tsaye komai wahalarsa ya aikata irin iyayensa, baya wasa da su baya hadasu da komai, kimkim dinsa kuwa halita ce ta dan Adam
Jiki a sanyaye suka fito suka nufi bangaren Docter dan yi masa salama domin tafia zasu yi sai kuma sun juyo
A cen suka samu Aunty amarya tana zaune tana karatun Alkur'ani shi kuma yana jan carbi yana kuma sauraronta, dan bashi da abin yi yau, ita kuma girkinta ne
Sosai ya sake yi masu gaisuwa da fatan alkhairi, shima ya karra masu wata kyauta sannan ya masu addu'a suka mike suka fice
Tunda suka fita take son dauko maganar ama ta gaza dan Auntu amarya dake zaune, har dai ta gaji ta ce" Magana nake da ita fa docter"
Murmushi kawai Abah ya yi ya ki ce mata komai, har dai Aunty Amarya ta kilace alku'aninta ta shiga taka matatakala ta haye sama Hajua kuwa na binta da kallo har ta bacewa ganninta sannan ta ja tsaki kasa kasa ta ce" Sai shegiyar dakakiyar zuciya kin sako yarinya a gaba kamar ita ta aikata laifin ko kunya bakya ji kai kamar na saliha ama na tantiriya ne!"
Ido Docter ya dan kankance yana dan saurarawa dan ya ji abinda take fadi,
Ido ya dan wara ya ce" Laifin me ta maki ita kuma?"
Dubanta ta maido kansa da yannayin sunna iya fashewa idan ta kama ta ce" Na taba yar gwal ko Docter?"
Murmushi ya yi bayanane kasa kasa ya ce" Eh gaskiya kusan haka..."
Baki ta tabe tana cire kai hadi da girgiza kafafuwanta, kana dubanta zaka fahimci tsabar rigima ke cinta take kuma nema su yi da wanda ke kusanta a irin wannan lokacin
Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye dan ya kawar da fadan nasu ya ce"
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_10_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye dan ya kawar da fadan nasu ya ce" Allah ya rahamshe da Manal Maman Baban gida"
Da sauri ta kalle shi, sai kuma ta sada kanta, shi kam ya iya saka mutun jin kunya, tsakani da Allah tana matukar jin kunyar cirat a ambaceta da maman Baban gida, Allah ya taimaketa daga ita sai shi da yau ya raba mata abin kunya walahi
Murmushi ya yi yana dan jan kafarsa a hankali da ta masa nauyi ya ce" Kin gani ko Zuwaira?

Idan kika kawo min kukan kina damuwa da lamarin halayarta ya dace ace ta rungumi dangi a matsayinta na matar baban wansu....... nakan ce maki ki yi hakuri mu yi ta sanarwa Allah, Baban gida ba zai taba tabewa ba domin d'a ne mai biyayar iyaye, albarkarmu na biye da shi du inda ya yi, babu abinda zai ci karfinsa da ikon Allah sai dai idan Allah ya riga ya hukunta kadararsa ce matakin ci gaban rayuwarsa ko samun aljarnarsa ne hakan, sannan mu bai taba kawo mana karar matarsa ta masa wani abin ba, kin ga gaba dayama ashe zaman nasu ba zai jima ba shekara biyar cikin ta shida da aure Allah ya amsheta, Allah ya sa mu cika da kyau da imani"
A sanyaye Mama ta ce" Amen ya Allah "
Sai kuma ta dago, fuskarta ta nuna ainahin alhinin dake cikin zuciyarta
A sanyaye ta ce" yanzunma cikin wata damuwar nake Docter, na rasa a wani gurbi zan ajiye haka, abin kamar an saka son zuciya, rashin sannin ciwon tasu da ta rasu ya mik tsauri ni kam, zuciyata sai take nuna min harda wata manufa a kasa, ko kawai hasashena ne?........gaba dayama ni na rasa me zan kirayi lamarin, ya girmami tunanina, Yaushema yarinyar nan ta rasu?

Y'arsu ce fa kuma, kanwarta ce ita kuma y'arta ce, ama wai suka kawo min maganar yayar tata ta maye gurbin kanwar, yau fa kwana takwas kadai da rasuwar nan, kuma ka san cewa itama Manal din nan ta girmeshi bale yayarta?

Bayan wannan ka sani sarai Baban gida baya magana, koda an kaishi ana cutar da shi ba zai taba sanar mana ba, bawan Allah salihi da shi baya cewa komai, abin tausayi da shi kana gani fa baya cewa komai Docter, kuma shikenan sai mu tashi mu sake daukan wata gyatumar mu maka masa kennan shi a haka zai gama rayuwarsa ne da auren yayunsa?, Gaba daya lamarin nan bai kwonta min ba a raina Docter "
A gaskiya abin shima ya bashi mamaki, idan aka yi duba da rasuwar kanta yaushe aka yi?

Menene na gagawar nan?

Ba maganar gagawa dan kuwa idan haka dinma suke so ai sai su yi hakuri a kalla a yi arba'in din mamaciyar ko?
Chapter 15 · 0% Book details