← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 110

Sashe 82

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An fada maki hakan daidai ne?

To ki ringa saka sutura sak kina zama da ita a jikinki dan gudun shedanu da kuma masu iya shigo maki, ke yanzu ko kunya bakya ji kina tafe da wannan rigar?

Haba dan Allah!"
Ya karashe yana zabga mata hararar da ta sakata sakw sada kanta tana ta jan numfashi tana rike hijabinta alamu sun nuna kamar zata yi kuka
Kansa ya dafe da hannunsa yana jin cikinsa na neman agaji,
A dole ya sake juyowa wannan karron amon muryar da dan sauki ya ce" Yinwa nake ji "
Dagowa ta yi da sauri ta zuba masa ido, ko tace jajayan leben da Mamah ke aibata kulun
Kai jama'a sai kawai ta ga ya mata kyau , fuskar tasa kanta sai ta ga ta mata kyau...., Da sauro ta dauke kanta tana korar shedan a sanyaye ta ce" Yayanmu ban ga kicin din bane"
Shima ya dan sake kurw fuskarta da ido, sannan ya juya ya fita ya shiga sauka a hankali yana jiyo tafiyarta a bayansa har suka sauko
Wajen ledar ya sake kallo a sanyaye ya ce" Ko zaki zazafa min wancen na ci?

Yinwa nake ji, ga kicin din cen"
Sai ta ji wani irin tausayinsa na neman kamata, bawan Allah haka yake da rashin jimirin yinwa?

Ashe shi yasa Mama bata wasa da harkar abincinsa, tunda ya dawo cin abinci bangarensu Mama a tsaye take kan kaffafuwanta, tunda safe abincinsa a saman table MAMAH ke yi na kari su sunna dakunnansu sunna barcinsu, tara na yi za'a taso mai girki ta shige kicin da wuri a gama abincinsa da wuri a kilace, haka na dare tunda yama an gama, bata san cewa baya hakurin yinwa bane sai yau
Kicin din ta nufa da ledar tana cirowa
Da dan gagawa ta bude ta shiga cicira kajin a baban abin zubawa tana mamakin yadda suka yi laushi, gaskiya sun samu kyakyawan gashi dan duwa du irin kwanan da suka yi haka suke yagewa da kansu, ta cicira su su dukansu ama bata yi anfani da kayan hadinsu ba dan sai ta ji kamar ya fara bugawa , ko dan a leda ya kwana a daure
Wajen ovn ta nufa tana kallon tarin kayan aiki na jone jone
Murmushi ta yi ta dauko fari kal sabo ta ajiye wajen jonawa ta jona shi ta ciro abinsa ta wanke tass ta saka paper na dumamen sannan ta zuba kajin ta karasa wajen ta saka ta kunna shi
Da dan gagawa ta nufi wajen da ta tabata a nan za'a tanadar mata kayayaki na bukata dan tsarin kamar kicin din gidansu ne sai kayan aiki kawai da wannan ta fi ta cen gida
Kayan sharr da su sai daukan ido suke yi, komai a gyare , cikin gagawa ta dibo dukkan abin bukata ta fito ta shiga aikinsu
Tana tsakar yi ta ji karan ya kashe kansa watau naman ya dumama , dan haka ta karra sauki ta hada yar dage dagen miyar da zai ci da shi ta tarugu da koren tatasai da dafafen kwai da Bama ya hadu har haduwa sannan ta dauko baban plate sosai ta juye naman ciki, ta kuma je ta dauko marfinsa da karaminsa ta sauye miyar ta rufe ta dauka da dan sauri ta fice ta nufi table din ta ajiye masa sannan ta je wajen frij ta bude ta zubawa frij din ido da kyar ta iya ciro tataciyar madara da kuma ruwa ta kawo ta ajiye ta sake komawa ta dauko kofi biyu na kwalba saman dab plate dinsu ta kawo ta ajiye masa sannan ta komawarta kicin din dan so take yi ta ga me da me kicin din nata ya dauka ta san komai inda yake ta kuma kimtsa komai yadda take so dan ta kula dole ta saba shiga kicin da wuri, idanma da hali tun yanzu zata dora girkin rana gudun a ringa titsiyota daga dakinta
Abincin yake kallo, lokaci daya wani tunani ya shiga yi masa yawo a cikin kwakwaluwarsa, bayan har ya fara ci cikinsa ya fara dauka ya ringa jin cenje cenjen yannayi a jikinsa kadan kadan hakan ya saka shi tunanin anya a kazar nan ba wani abin aka saka masa ba?

Babu abinda ya gagari aban Ahmad, babu, kuma tabas yana iya yi masa wani abin a kazar nan ko dan a saka mutun a uku
Tsai ya yi da ci ya dauki madarar nan mai sanyi ya bude da sauri ya kafa kansa har sai da ya shanye tasss sannan ya ajiye yana jin ya koshi, dan haka ya mike da sauri ya dan tsaya ya gyara jikinsa da kyau dan har tara ta gota bayan karfe takwas yake da aiki
Bai tsaya nemanta ba, baima tsaya sanar mata ba, dan bai saba hakan ba, ya saba marigayiya na zaune yake ci idan ya gama kuma tana biye da shi har mota, dan haka bai tsaya nemanta ba da dan sauri ya karasa ya bude kofar ya fito yana dan rike wayarsa daya da ya dauko, nan suka yi ido hudu da Luba dake zaune gefenta baban kwondo ne shake da kayan abinci tana whatsup da wayarta
A hankali ya ce" Lafiya, aa yaya kike zaune a nan ne baki shiga ba?"
Luna aka yi wani dan murmushi ta ce" Ai na jima a nan din tun da duku dukuma inaga, na ga baku tashi bane sai kawai na zauna har ku tashi"
Dan kureta ya yi da kallo, wai duku duku, shima bakwai ta wuce ya dawo kuma shi bai ga kowa ba, wai basu tashi ba, hum Luba kya yi ki gama
A bayane kuwa ya ce" Ohk,na tafi"
Da dan sauri ta ce" Aiki kuma yau din?

Ba zaka huta bane yaya?"
Amsa ya bata yana ficewa ya ce" Eh ban gaji ba" a ransa kuwa ya ce" Na ga natatun mutane, wadinnan da gida daya nake da ku tsaf zan kaiku a mana tsakani da ni dan kar ku dameni ku sa na rame!

Luba kuwa murmushi ta yi ta sabi kwondon ta karasa dan bai rufe ba ta shiga ta rufe tana fadin"
Da murmushi Luba ta shiga tana fadin" Asalamu alaikum masu gida ko ana sama?"
Da sauri Fatima ta dago tana sakin murmushi ta ce" auntyna auntyna"
Luba ta yi turus tana kallonta
Kwondon ta ajiye ta karaso da dan sauri tana sake binta da kallo, kamar aiki yar nan take yi?

Ta ayana a zuciyarta
A fili kuwa tana murmushi ta amsa gaisuwar ZAHRA ta ce" Kaji ba aka ci yar mamanta?"
Zahra ta yi dariya ta ce" Aa aunty yayanmu ne ya ci , kwashewa ne zan yi na dafa dan ni na fi so da romo"
Da dan takaici ta ce" Dan zo nan wajen na gani ZAHRA?"
Fatima ta dan kureta da kallo, ta zo nan wajen ta gani?

Ta ga me?

Luba ta karasa da dan sauri ta kama hannunta ta ce" Ke je cen gaba ki dawo kadan?"
Zahra ta je din ta dawo dan ta kasa hane meye
Luba ta shiga tafa hannu da takaici ta ce" Yanzu yar nan na hadaki da kannanen kaya, na ki rako ki, dan a matsayin ki na mace tun jiya ki fara saita wannan mutumen kika zuba masa ido ya kwana ya tashi har kika bashi kari ya ci ya fita ke ga shashasha?"
Ido ta zarro kasa kasa ta ce" Aunty dan Allah ki yi magana a hankali yana nan fa kar ya kamamu muna magangannun nan marrarsa dadi bayan yanzu ya gama min fadan saka kannanun kaya"
Tana dan zarro ido ta ce" Ke bai ce maki zai fita ba?"
Zahra ta dan turo baki tana girgiza kai
Luba ta idasa shaka ta zauna ta janyo ZAHRA ta zauna itama ta ce" Lalle sai kin yi da gaske, walahi kin ga mijinki ko?

Idan baki yi da gaske ba zai mayar da ke yadda ya rayu da wancen, rayuwar cikin gidan aure ba wata shakuwa ba wani abu special wanda kece kawai kika isa da shi, yadda zai yi mana magana mu kannensa kema yana iya yi maki, inda ya fi sannin darajarki wajen abincinsa, nan fa ba zai taba mantawa da ke ba, bayan wannan ya mayar da ke kamar wata bakuwa a duniyarsa, in dai haka zaki rayu da shi to kuwa ba zaki taba morar kuruciyarki da kuma tsufanki idan da ranku da shi ba!, Koda yake cewa kika yi ya yi fadan saka kannanun kaya ko me?"
A hankali ta gyada kanta tana jin kamar magangannun Luba na nema su yi tasiri a kwakwaluwarta, maganar da Luba ta fada fa cewar ta riga ta shigo sai wani ikon Allahn hakane, yau ko ita kanta ai ba zata so ta fita daga gidan nan ba a matsayin iyalinsa ba, ita ta ga abinda ta gani a jiya zuwa yau kuma ta yarda cewa Allah ne ya bata dan ya nunawa masu tunanin bata isa ta samu rahama da ni'imar ubangiji ba cewar ba su suke da duniya da lahira ba, ta yarda cewa da ta wayi gari a sunnan matarsa wani hukunci ne na ubangiji, abinda ke dan riketa ta kasa gannin cencentar abin ta fi gannin abin ya fi karfinta, ama idan Luba na magana sai ta ringa tunanin anya itama bata cencenci rayuwa mai kyau da namiji nagartace irinsa ba?

Itama ai mutun ce, kamar tana da damar samun farin ciki na rayuwa, kamar tana iya samun farin ciki na rayuwa ko?

Hannayenta Luba ta riko tana fuskantarta a hankali ta ce" Ba'a yin biyaya a irin wannan umarnin, ni da kika ganni a nan har nema na yi na san meye abincin da mijina baya so na je wajen manyan da suka iya girki suka koya min sarafawa kala kala, na ringa durfafarsa da shi har sai ya ci ya murle na sanar masa kaza fa ka ci?, Ta yayama zai ce ki daina saka kannanun kaya?

Yanzu kika fara, ZAHRA in dai ba bangaren Mamah zaki je ko anguwa ba ba ke ba atampa ko leshi, kar wani ya tardoki?
Chapter 82 · 0% Book details