Sashe 44
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan zulumin ya hannata barci, kira kuwa ta yiwa Mamah ya fi a irga har sai da Maman ta kashe wayarta dan gaba dayansu ta sanarwa ama Aunty amarya ta gaza zama waje daya , karshema haka asuba ta risketa garin Allah ya waye tana cikin hali na kuncin zuciya da tashin hankali, har suka fito suka tafi wajen karatun da aka yi kiran kowa aka hadu ana sauke Alkur'ani da sadaka.....jikin Docter kam ya kiya sai fatan samun lafiya ko wace iri ce, hankalin iyalansa gaba daya a tashe yake, basu taba yin wuni tare ba dai a wannan lokacin, abinci zubawa ake ana kaiwa cen bangaren na docter domin a cen suke iyalan nasa baki daya, hankali du ba a jiki ba, babu mai hararar kowa, kowa yana cikin zulumi
A hankali yayansa na nesa suka fara matsowa sanadiyar kiran da suka ringa samu da iyayensu
Mazan ne, da matan masu aure, daidaiku ne basu samu zuwa ba dan mazajensu sun ce su bari ya dawo mana mutumen da ba rasuwa ya yi ba zasu ringa zuwa sunna dagawa junna hankali, aduarsu yake da bukata fiye da komai
A irin wannan hali ahalin gidan Docter suka dauki kwana biyu bayan kiran Mamah sunna cikin hali na zulumi, sunna karatu ba ji ba gani da sauke Alkur'ani, ana sadaka ta launin abinci kala kala da ta suturu da ta kudi, sosai suka ninka alkhairansu , wanda hakan ya zamto baban abu mai daraja, domin har a masalacin Docter abinda ake yi kennan, ana cikin roka masa gafarar ubangijinsa domin su Marshal ya fito masu karara ya sanar masu ne Docter na bukatar addu'a, dan tunda ya shige halin comar nan bai kuma sannin inda kansa yake ba
Tun karfe hudu da rabi Amir ke kai kawo a baban tsakar gidan yana sanye da jalabiya fara hannunsa rike da carbi, idannuwansa sun gaza daina zubar da hawayen da suke tarawa yana kai kawo yana ankare da dukkan wani motsin dake kai kawo sanadiyar abinda ya same su iya mazan suka ji banda matan da suke falon Abah yanzu yake sa ran gannin sun bude dan ya sanar masu domin baya so su ji daga bakin wani
Alamun an fara kukunna wutacen falon ya saka shi sake sauke wani hawayen mai zafin gaske, a hankali ya karasa ya dan dakata dan ya basu damar kimtsa kansu, dan tashi daga barci ai ba kowa ke yi tsaf tsaf a nutse ba
Ya dauki minti kusan goma a tsayen nan ya shiga bubugawa a hankali sannan ya dakata
Ba'a jima ba aka tambayi wanene, dan du sai suka tsayar da abinda suke yi na shirye shiryen daura alwallah da hawa saman salaya, shake falon yake da iyayensu da
ansu a haka ya shigo yana dan cicira ido ya rasa inda zai fara nufa dan a gaskiya bashi da wannan courage din a yanzu a gabansu
Uman Abul ne take saukowa daga saman Abah hankalinta a kan abinda yake faruwa
Jiki babu karfi ta karaso tana fadin" Lafiya du kuka yi tsaye kunna kallonsa?
Yayansu lafiya dai ko wani ne ya aikata laifi?"
A hankali ya ja numfashi ya sada kansa, muryarsa a sanyaye ya ce" Aa, babu wanda ya aikata wani abu, shigowa na yi na sanar maku cewa, yau mun tashi da kyautar Ubangiji"
Da sauri ta sake kureshi da ido, lokaci daya kuma Aunty Amarya dake tsaye saman salaya ta silale ta zauna tana tataro kafafuwanta ta dora gwuiwoyin hannayenta sannan ta kai tafukan wajen kanta tana yamutsar kan nata bskinta ya kasa furta komai
Mahaifiyar Furera ce ta ringa ambaton innalilahi wa inna ilaihi raj'une, domin yannayinsa zai sanar masu kyautar ubangijin me take nufi
"Kana nufin Docter ya rasu?" Maman Abul ta fada muryarta na wani irin rawa, hajan ya sa yan matan da yayunsu masu auren barkewa da kuka kowa na rungumar wanda ya fi kusa da shi, shi kuma ya karaso jikinsa tamkar an zare laka ya zauna a saman kujera a sanyaye ya ce" Allah ya amshi ran Abah, karfe uku na dare da wasu yan mintuna"
A hankali itama ta bi ayarin matansa dake kuka da ya'yansa, muryarta a matukar jigace tana kallon Amir ta ce" Shikenan Amir Abah ya rasu?
Wayo Allah mun shiga uku mun lalace, innalilahi wa inna ilaihi raj'une innalilahi wa inna ilaihi raj'une, dama tafiyarsa ba ta dawowa bace?"
"Amir yanzu shikenan a akwati za'a sako gawar Docter a kawo a wuce da shi makwontai mu ko ganninsa ba zamu yi ba?, Shikenan mun rasa uban y'ayanmu ya tafi da kaffafuwansa a dawo mana da gawarsa a cikin sanduki?
Menene zai saka mu samun nutsuwar zuciya bayan bamu ga gawarsa ba?, Menene zai sanyayar mana da zuciyarmu?
Shi yasa yake gudun fita wajen nan, fin karfin Docter aka yi aka fitar da shi waje, gayacen ya rasu za'a kunkuma mana shi a cikin samduki a kawo a wuce da shi a turnutse a kabari ba tare da mun yi ban kwana ba?" Maman furera ta fada tana hawaye hankalinta du ba a jikinta ba
Murya a sanyaye Aunty amarya bayan ta bi yan matan da kallo du sun warwatsu kowa yana neman inda zai saka ransa ta ce" A nasihar Abah, yace du inda ransa ya fita a birne shi a nan, kasa ta kai shi"
A zabure Maman Abul ta dubeta ta ce" Kina nufin ba za'a kawo mana uban y'ayanmu kasarsa garinsa inda aka san darajarsa aka san mutincinsa a birne shi ba?, Ai ba zai taba yiwuwa ba, in dan tashi ne ai shi komaima ya yi yadda ba zai wahalar da dan gwal din ba!, Dole a kawo mana mijinmu a birne a garin da muke ko dan ya samu kyakyawar ziyara da addu'a ta kirki "
Uhum, wasa farin girki, Amir sai ya rasa bakin magana , ya ringa bin wani gagarumin rikici da tashin hankali da yake gani a gaban idannuwansa wanda Mahaifinsa ya tafi ya bari, ama ya bar wa da shi?
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une abinda yake kallo a yanzu ya karra daga masa hankali da shiga tashin hankali da tonon asiri irin na mutuwa, wai wadinnan ahalin da Docter ya bari wa ya barawa, ya Allah, wannan lamari ya sake gigita shi, ya sake saka shi shiga a hali na tarin tunanin shin yaya zasu yi?
Da kyar ya iya budar bakinsa ya shiga tunasar da su ya dace a yanzu su fahimci gawa a shinfide take, ya dace su bi
ansu da suka fice sunna kuka su tsawatar masu su saka su daukan carbi su nunawa mahaifinsu soyayyar da ya dace, ya kamata su gane rigimar nan da suke neman balowa a yanzu bata da wani anfani, komai dai na Allah ne, Docter ya rasu a kasar musulmai, yau ko a kasar wa'inda basa sallah ya rasu ai ni'ima ta ubangiji ce, maganar abinda zai sheda maku ya rasu ko bai rasu ba kun san dole za'a basu shaida, ya zama wajibi a gabatar masu da shaidar komai dan rasuwa aka ce ba abin wasa ba, in har basu yarda da fada masun da aka yi ba ya kuma tabatar masu tabas za'a yiwa docter sutura ne a garin da ya rasu, shine ya bukaci haka, karshe dai shine ya mike ya fice ransa na baci dan har an shige masalaci an fara sallah ya karasa da sauri ya kurkure bakinsa ya shige masalaci dan niyarsu idan aka salamce a dora da dukkan abinda ya sawaka dan yiwa docter shinfida
Garin Allah na wayewa gaba daya gari ya dauka
Tururuwar mutane ne kawai kake gani ta ko'ina domin a kafafen yada labarai an sanar cewa za'a yi jana'izarsa a yau din a cen kasar da ya rasu, sai dai ahalinsa zasu mike da amsar gaisuwa, hakan ya sa du wani wanda abin ya shafa da al'umar annabi suka ringa tururuwar zuwa gidan ya dinke da kofar gidan dake dauke da dankara dankaran runfunna wa'inda mazan gidan suka girka shake da jama'a ana ta karatu sama sama idan ka nufo sai ka ji tsigar jikinka na tashi bama a lokacin da Mamah ta sanar an tafi kai Docter gidansa na gaskiya a lokacin kowa ya sake bada hima da dukkan abinda ya samu ana binsa da addu'a har kusan sha biyu na rana sannan aka ringa watsewa wadu kuwa sunna nan dan sai sun tarbi MARSHAL sun masa ta'aziya sannan su tafi hakan ya sa wasu na tafia ne wasu na karuwa gidan na sake daukan al'uma
Tun karfe goma sha daya suka kamo hanya, sai kusan sallar magariba suka karaso garinsu
Mota daya tak ce aka zo daukansu da ita, Amir ne da kansa ya tuko ya zo daukansu
Motar bak'a ce mai bakaken gilas , tunda ya tsayar da ita yake tsaye ta wajen da masu tarban baki suke tsayawa har suka ringa fitowa yana binsu da kallo kafin yake hango Mamah ta dan rabu da jikin MARSHAL sunna tahowa a hankali a hankali kanta a saman damtsen hannunsa nikaf a rufe a fuskarta yana sake talabarta a jikinsa ya nufo motar da Amir ya bude da sauri yana sada kansa dan fuskar MARSHAL ba zata iya kwatantuwar irin yannayinsa ba, danma ya saka bakin gilas ne ba zaka gane halin da idannuwansa suke ciki ba, ama ta yadda fuskar ta dauki ja haka jijiyoyin jikinsa dole zaka fahimci a damuwa yake
A hankali ya sake riketa zai sakata a motar ta dago idannuwanta tana kallonsa, muryarta na hadewa da kyar ta bude bakinta bayan ta shafa sajen dake fuskarsa ta ce"
Muryarta na hadewa da kyar, ta zuba idannuwanta a saman fuskarsa ta dora a gefen fuskar nasa ta shafa a birkice ta ce" Abahn docter....., abahna.....
Shikenan na tafi da docter na dawo ni kadai.....?