Sashe 43
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Abinda ta fi ganewa shine a yanzu irin yadda take jin dadin kasancewarta a tsakaninsu ya fi mata komai a zuciyarta, wasu abubuwa take koya masu daraja da tsayawa a rai, wasu tunanika ke shiga zuciyarta nasy darajar gaske irin tafiyar mu'amalar soyaya da saurayi da budurwa a tsanake ba a rikice ba irin nata, a zamantakewarsu bata taba gannin dayarsu ta zauna tana faman neman saurayinta ba, a ajiye yake zai yi kira da sasafe sannan da dare da kansa,
Hira ba a boyewa dan ba maganar a shiga uku a ciki
Sai hakan ke bata mangari take kuma auna tata hirar da wanda ta yi ikirarin a kansa tana iya rasa ranta
Duhun kai kennan
Kiran dake sake shigowa a wayarta ya sakata wannan karron kallon auntynsu a nutse ta ce" Aunty ya sake kiran fa, wannan kiran nasa na biyar ne a yanzu dai"
Rukaya ta amshi wayar tana kallo har ta katse sannan ta ajiye a gefenta ta fuskanci Zahra'u sarkin aiki, du irin gajiyar da ta kwaso yanzunma tana ta ninke kayansu da suka wanke ne dan ba wai idasa sakewa da hira da su ta yi ba, ana dai samun abinda ba za'a rasa ba na ci gaban mu'amalar dake tsakani
A tausashe ta ce" Fatima?"
Fatima ta dago da dubanta tana idasa ninke hijabin Auta ta ajiye ta amsa kiran da ta yi mata
Rukaya ta nuna mata gefensu tana fadin" Zauna a nan"
Zama Fatiman ta yi tana kallon su a ranta tana ayana ko menene wata maganar ce mai mahimmanci
Rukaya ta nisa ta ce" Da farko dai Fatima zan sake baki hakuri na irin zamantakewar da muka gabatar a tsakaninmu baki daya, zan kuma sanar maki cewa a yanzu ko me yale damunki ki neme mu kai tsaye domin mu yan uwanki ne, baki da sama da mu, kuma ke ba bare bace a cikinmu, kin fahimta?"
Fatima ta lumshe idannuwanta tana hanna wasu hawaye masu dumi zubowa daga gurbin idannuwan nata
Rukaya ta dora da fadin" Kin ga, idan nace shawara ina nufin ko wace iri ce, ciki harda ta maneman mu'amala da ke ko wace iri ce, kin ga dai yadda lamarin wancen ya kare, a yanzu kuma ga wani HASSAN dake kira ba ji ba gani kan dan Allah a hada ku, bai zo da wasa ba, sonki yake yi da aure idan har za'a bashi........., Allah yana gani babu mai neman kai da ke, babu wanda kika takurawa bale a tashi a mika masa har ya yi tunanin dama ko an gaji da ke ne, Bamu gaji da ke ba muna sonki hakan ya sa muka nuna masa mahinmancinki, ama a yanzu na fuskanci ya dace ki saurareshi dan bamu san da me ya zo ba, ba'a saurin yanke hukunci kuwa sai an zauna dole, ina fata zaki yi wannan kokarin Fatima?"
Tabas bata manta waye Hasan din nan ba, yayama za'a yi ta manta shi ya gwada naci ai a mll din nan
Wayar da ta miko mata ta amsa tana sake bin numbar dake nuni da kuma kukan ringin din
A hankali ta daga tana yin salama da siririyar muryarta sannan ta saurara tana bin Rukaya da kallo wace ta ga kira da numbar Mamah ta mike da sauri tana fadin" Mamah kuma da wannan lokacin?..............."
Magana yake yi, hankalinta na kan yannayin Rukaya
Da sauri ta mike tsaye gannin Rukayar na yarfe hannayenta ta bude baki ta ce"
Ba eddting
*25*.
D5
Da sauri ta mike gannin Rukayar na yarfe hannayenta ta bude baki muryarta a raunane ta ce" To Mamaj bara na gani ko barci ta yi aunty amaryar?" Ta karashe tana nufar hanyar fita ta nufi dakin Aunty Amarya
Su duka biye suke da ita, dan yannayinta dole zai daga hankalin mai kallo
Jiki ba karfi ta buga dakin aunty Amarya sannan suka ja suka tsaya sunna jira
Jim kadan Auntyn ta bude hannunta da carbi tana ja idannuwanta ya sauka a kan hannun Rukaya da ta miko mata wayar ta ce" Aunty Mama ce tace bata samunki"
Amsa ta yi itama ta juya tana jin gabanta na faduwa ta amsar wayar maman su kuwa sun yi tsuru tsuru an rasa mai iya yin tambayar jikin na Abah ne ko menene?
Kowa tsoron amsar da za'a bashi yake yi, jim kadan ta dawo masu da wayar ta mika masu muryarta na rawa sosai ta ce" Ku je ku daura alwallah, kowa ya gabatar da abinda ya iya wa mahaifinku, Allah ya bashi lafiya"
Adawiya mai saurin kuka ce ta shiga yi tana matsowa kusa da Aunty Amarya ta ce" Aunty, ya rasu ne Aban?"
Idannuwanta da suke dauke da kwallah ta dora a saman fuskar Adawiyar a sanyaye ta girgiza kanta ta ce" Bai rasu ba, ama bashi da lafiya, su Hajia ba gobe zasu juyo ba, dole sai sun sake kwana dan a ga yadda hali zai bada, ku dai ku rike carbi Allah ya tashi kafadunsa"
Da wannan ta salame su ta juya nata dakin ta karasa saman salayarta ta zauna
A hankali ta sada kanta waje daya, sai kuma ta fashe da kuka, kuka mai tsatsanin gaske tana jin tamkar zuciyarta zata bar gangar jikinta......., Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ga abinda suke fada mata.....ga abinda maman Abul ke fada mata da kuma maman Furera, .....a lokacin da suke tunanin itace ta tsiga tsakaninsu da mijinsu ba zuwa ba zowa gan lamarin aurataya sai suka sakota a gaba da yan habaice habaice kamar haka :sukan ce mata ta fa yi aniya a dakan da take saka shi ya bata koda cikin y'a mace daya ne, dan idan tana da hankali zata kula Docter dai shekaru karta ja suke ita kuma a cikinsu itace yarinya futul itace ba d'a ba jika tsakaninta da shi, ta kuma sani sarai cewa wannan gida da ake ciki gida ne da yake malakin MARSHAL, gidan docter wanda suka taso suka dawo wannan ko rabin rabin wannam bai kai ba duda shima gida ne na masu kudi gaskiya, sai dai a lokacin da ya fito ya ringa dauka gaba daya ya raja'a ya maka ginnin nan bulo da bulo hawa da hawa wajajen shakatawa kala daban daban wajen karatun islamiya kai babu ce kawai babu ya zuba mahaifinsa da makarabansa dan karra samun jin dadin rayuwa, ta fa sani idan har Docter ya mutu a lokacin da bata da d'a ba jika tsakaninta da shi tana cikin matsala, dan kuwa cimilin takaba ne kawai zata iya samu, gwara gwara su idan aka dan duduba ta yiwu da yan motoci da gonaki haka jefi jefi sai gidajen nan nasa uku wa'inda ake haya a cikinsu baki daya, idan aka raba ta yiwu su samu matsugunni , ita kam sai dai a koma rayuwar da........watau rayuwa a bakin titi ana neman na abinci , ana bara ana karuwa ................
Wadinnan kalamai su suka fi daga mata hankali, dan ta san wace rayuwa ce ta baro ta bakin titin, lalle bara kam ta yita ama kuma karuwancin bata taba yi bama, sai dai ta fuskanci kalubale da tashin hankali daga wasu mazan azalumai masu son wulakantar da mace, wa'inda idan suka ganki a halin kaka naka yi baban burinsu su ribanceki su idasa wulakantar da darajarki a banza a wofi dan baki da yadda zaki yi........., Magangannu mararsa dadi da sauransu, shi yasa tunda ta samu kilacewar nan sai ta sake kilace kanta, abu biyu kawai ke fitr da ita koyon girki a lokacin da take amarya, sai kuma islamiya....summa tana samun abinda ta samu ta dawo ta kilace kanta, bata da kawa, bata da abokin shawara sama da Docter, bata iya sakin karinta ta yi hira da kowama in ba shi din ba....................