← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 110

Sashe 97

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bai tsaya jin komai ba, ya dan rage tsayinsa ya damki hannun Furera ya mikar da ita tsaye sannan ya juyo da ita yana jan hannunta a lokacin da ta nemi zubewa idannuwanta a waje lokaci daya ta saka wani irin firgitacen kuka tana kiran sunnan mamansu kan ta taimaketa
Da sauri ya juyo ya zuba mata ido, haka mamansu da ta nufo shi hankali tashe tana
kiran BABANGIDA dakata mana ka ji, ba fa wani abu ta yi ba fa ya zuba mata ita dinma
A hankali ya ce" Mamah, idan kika biyo ni, ki tabata hakuri zaki yi ki ga abinda yake faruwa ki kuma iya kawar da kai daga dukkan abinda zan aiwatar wa kanwata, bayan wannan bana son komai, ke kuwa in kika saki gigin shirme ko haukacewar raini ta saka ki summa ko faduwa kina min ihu sai kin yi jinyar kaffaguwanku da hannayenki dan sai na kakaryaki a gidan nan!"
Kitttt kake ji ta daina ihun kukan, sai dai hadiye kukan da take yi kamar zata mutu dan tsoro da tsoron abinda ka je ya dawo
A kofar Mama ya dakatar da ita ya ce" Ke wajen wa zaki kai abinci da kudi?"
Furera na hadiyar maganarta ta ce" Yayanmu, wajen aunty Laraba ne zan je, wajenta ne zan tafi"
Gaba daya maganarta bai yarda ba, hakan ya sa ya saki hannun nata bai yiwa kowa magana ba ya juya ya fice a gidan, inda haka ya sake daga hankalinta ta duke tana rizgar kuka hankalinta gaba faya a tashe
Salama ya yi, ana amsawa ya saka kansa cikin gidan kai tsaye ya nufi inda su Maman Laraba take da Laraba sunna cin abinci
Tunda Laraba ta ganshi fitsarin dake mararta ya fara fitowa, haka kuma lokaci daya jikinta ya dauki rawa hankalinta ya nemi fita daga jikinta da tsoro da firgicin gannin nasa
Tsayinsa ya rage sosai ya gaishe da Mamansu, wace ta mike itama tana ta mamakin ganninsa yau a cikin gidansu haka?

Da kula ya dubi LARABA, a kausashe ya ce" Kece Laraba ko?"
Da inda inda ta amsa tana sake dukawa daga zaunen da take
Kai ya gyada ya ce" Kudin meye Furera zata kawo maki?"
Daga ita har mamanta sai da gabansu ya fadi
A rikice ta ce" Kudi kuma?

Aa walahi ba ni bace, ba wajena take kawo kudadenta ba idan ta samu, wajen Yayansa ne take kawowa yana bayima bara ys fito a tambayeshi ko babarmu?"
Gabansa ne ya dake faduwa, jikinsa ya fara neman rikicewa na bacin rai, wajen yayansu?

Me ya hada FURERAR da yayansu?

Mahaifiyarsu kuwa kai kawai take girgizawa, dama ta san a rina, ta tabata akoy ranar kin dilaci, a tsaye ta fada masa a zaune ta kwatanta masa cewar ya kiyaye , gidan nan da yake kai hari ba wajen wasa bane, ba wajen da zai je ya ringa baza rashin da'a irin nasa bane, waje ne da ya fi karfinsa, waje ne da idan har ya aikata masu aikin da ya saba a cikin gari ya tsira da wahala ya sha, ta yi fadan , ta yi nasihar, ama da yake
anta ba jin maganarta suke yi ba sai yake ci gaba fa yada rashin da'arsa, yau ga ranar, tashin farko MARSHAL din ne ya gani sai ya san inda zai nufa
Jin shiru an ki fitowa daga bayin ya saka BABANGIDA karasawa ya dan tsaya a hankali ya ce" Ka fito, idanma ka haura garu ka san babu inda zaka je"
Cikinsa ne ya sake murdawa, hankalinsa ya sake tashi
Da kyar ya iya budewa jikinsa na rawa ya fito ya duka gaba dayansa tun kafin ya tambayeshi ya ce"Oga walahi walahi yarinyar nan itane ke zuwa tana samuna kulun ta Allah, kuma kudinta ni ko ta kawo nan nake barinsu bana wani abu da su, Oga kuma ni ban taba aikata iskanci da ita bahar ga Allah, a tambayetama a ji"
Kai MARSHAL ya shiga sarawa, idannuwansa suka ringa lumtu na bacin rai
Bai iya yi masa magana ba da hannunsa ya masa alamun ya biyo shi
Tafia ta daf da daf ce suka yi, haka kuma sunna zuwa shiga aka hanna babarsu binsa dan Laraba ita sunna barin gidan ta yi bayi da gudu ta kai sauran zawon da ya daure mata ciki
Tunda Furera ta hango su ta fada dakin Mamah jikinta na rawa tana ihu, a lokacin su Maman su Abul da sauransu du sun ji kuma kowa na nan ana ta mamakin me hakan yake nufi inda mahaifiyarta ta dage tana kwatantawa Mama bafa komai bane dan zata kai abincinta cen su ci ne ai babu wanda bai san tsakaninsu da Laraba ba, akoy zumunci mai karfin gaske
Auta da ZAHRA sai yanzu suka san me yake faruwa shigowar tata da gudu
Bata jima da shigowar ba suka shigo summa da su Maman baki daya, da Amir da MARSHAL sai Sayadi a bayansu sai jan wando yake yi gajeran wando irin na maza da rigarsa ta yadi ta masa mugin yawa sai tsamin bayi yake yi ya yi tsaye tsamo tsamo a gabansu yana ta faman bari da jiki , kana ganninsa ka san bashi da gaskiya
Hankali Tashe Maman Furera ta ce" Babangida wannan kuwa wanene?

Me yake nema a nan?"
Mamah itama hankalinta tashe ta ce" Baba wai meye yake faruwa haka ne dan Allah?"
Da kyar Babangida ya iya zama, ko kwaliyar da aka sheka masa idannuwansa basu hango ba, asalima bai ganta ba kwata kwata a cikin mutanen hankalinsa a tashe yake sosai
Yana zama ya Kalli Amir da shima har bari jikinsa yake yi domin sai yanzu yake jin wasu magangannu a kan maganar
Amir ya kalle shi ya ce" Ka yi bayani ana jinka!"
Jiki na rawa ya ce" Walahi walahi ita ke tardoni kulun gida, ama gatanan a tambayeta idan na taba yin iskanci da ita, kudadenma da take bani kulun sai na mata fadansu sai tace ai akoysu da yawa ne, ni ban taba nemanta ba, ban taba janyota ba, itace ke sona ni na sanar mata bani da kudin aurenta tace ita zata bani, gatanan a tambayeta komai ban taba sakata dole ba na rantse da uwa rah..............................................

Kwashe shin da Amir ya yi da kafarsa ya maku a kasa ne ya dauke furucinsa, lokaci daya sai maganar Maman furera dake salalami hadi da kuka ta kalli wannan ta kalli wancen a rikice hankalinta tashe ta ce" Kai, kai kuwa wanene?

Ka ji tsoron Allah me kake nufi da magangannunka?

Me ya hadaka da y'ata a ina ka santa?

Yarinyar da babu inda take zuwa ta kai maka kudi a yi me?

Wani ya aikoka ka ci zalin marainiyar Allah?

To ko wanene kai kotu ce zata rabani da kai dan ni ba yar iska bace ban kuma haifi yar iska ba, ke Furera dan ubanki zaki daina kukan nan ki sanarwa yayanku ke bakima sanshi ba?

Ki sanarwa yayanku karya yake yi so yake ya maki shari dan a wulakanta ki a zageki, ki min shiru ki daga kanki ki fada dan ke jinnin malamai ce kuma ni mahaifiyarki a mutunce na zo dakina har na gama hayayafata mijina ya rasu ban san hanyar iskanci ba bale ke y'ar da na haifa ki yi!"
Mama kanta hankalinta a matukar tashe ta gaza baban furucin da ya fi salalami ta rasa inda zata shiga, kulan da Furera ke yi kuwa ya tabatar da ko menene akoy kanshin gaskiya a ciki
A kausashe ya ce " Furera ki yi shiru mana, kai ka daina mana ihu mana, , ke Furera zo nan, zo ki fada min tun yaushe kike tarda shi?

Me da me ya taba maki?

Ko bai taba maki komai ba?

"
"Ya yi mata me dan girman Allah?

Wani irin ya mata wani abu innalilahi wa inna ilaihi raj'une me yarnan ta yi je za'a nemi dora mata irin wannan babar maganar a kanta?

Furera ki sanar masu ke babu inda kika je, baki sanshi ba" Mahaifiyarta ta sake fada tana rizgar kukab itama, sai dai ko shiru bata idasa ya yi Furera na kuka ta ce" Yanzu Yah sayadi nece zaka ce nice ke zuwa kai bama ka sona?

Nice zakace ina kawo maka kudi kana min fadan hakan?, Yanzu yah sayadi nice nace zan biya maka sadakina?

Ni dai na san nace zan sama maka jari da na baka kudaden cen kace an sace shine nace toh zan sake nemowa na baka ka rike jarin da yayanmu zai baka ni dan ba zai baka aurena baka da sana'a ba, shikenan dan an kamani yau sai ka nuna bakama sanni ba dan ka ceci kanka?

Yah sayadi kai da kake fadin ko fito na fito zaka yi da yayanmu ka shirya in dai a kaina ne?, Eh gaskiya ne baka yi iskanci da ni ba ama a iskanci menene ya rage?
Chapter 97 · 0% Book details