← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 110

Sashe 96

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zata iya cewa shine mutun na biyu da ko rami ya haka da ido ya mata alamun ta shige zata shige dan ta tabata ramin ne a idannuwanta ama lalausar shinfida zata fada mai sosa baya da saka barcin nishadi.............,
Yayansu, batama san me zata ce ba, ba tsoro ne yake bata ba, wani irin girma ne yake da shi a zuciyarta mai matukar wuyar fasara........, Ita dai ta san cewa ya isa da ita, kuma shi din duniyarta ne
"ZAHRAh, ko tsoron sake kasancewa da mijinki kike yi?" Shirun Zahran ya saka auntynsu sake yi mata tambayar nan a tausashe, wanda hakan ya sakata zarro ido da sauri ta ce" Kai wayo Aunty kuma....."
Luba ta saka yar dariya ta ce" To ni sanar min tsoron me zaki ji kuma?, Ai na zata mata zaki rako ke"
Zahra'u da ta rufe fuskarta tana daria ta bude a hankali ta ce" Aunty, wai fa shi yayanmu ko, sai na ga kowama budurwarsa ce,, to ni ta yaya zan iya magance haka bayan a nan take kwana kina gani fa ita auntyn cen, a nan fa take kwana fa wai yayanmu zata aura, ko batama tausayinsa ne?"
Yanzun kam dariar Luba da karfi ta sakata tana zarro ido ta ce" Kai, y'ar nan anya ba hankali kika raina mana ba muke nan muna rarashi da son mu koya maki son mijinki da kula da shi aje kin jima a cikin kogin soyaya?, ZAHRAN mamanta kishin mijinki kike yi ne yarinya ba yau ba bamu sani ba?

Tlll me an kanwata ita wancen auntyn haushima take baki tana wani son maki miji ko?

Wata hajia Mamah da ita ta wani ce mijinki take so ko?

Watau inma kwontar da hankalina tsaf inaga y'ar MAMAH fa tana sin mijinta ba sai an koya mata kula da abinta ba, da gaskiyarki ZAHRAN Mama inama hadi in ba son kai ba , yar shila da ke ai kece daidai zamanin yayanmu, shafa min na ji kannun labarin nan yaushe ta damu bani da labari?"............

Da dan ihu ZAHRA ta datse kiran ta diro kasa tana haharba kafafuwanta kamar autyn na gefenta tana bata so bata so ita bata so....., Sai kuma ta yi tsai ta saka dariya ta kwonta nan saman cafet tana rungume hannayenta a hankali ta lumshe idannuwanta tana jin wani irin abu na ratsa zuciyarta.......

Tana murmushi ta mike ta nufi wajen dakinta, domin yanzun karfe uku ne zata yi idan ta irga da kyau yamar ta kusa yi, ita kuwa ta sha barci har ta gode Allah abinda yake gabanta yanzun shine zata je ta sakawa gashinta abin nade gashi ne ta kuma gyara kaffafuwanta da akaifunta ta kunsa masu lalle ja..........., A zuciyarta take ji dolema ta shiga nutsuwar yayansu.........., A cikin ranta take ji dolema tsakanin mata da maza a bambance waye mai rarashin, waye mai neman so........, Zata nemi so cikin hikima ba tare da ta roka ko ta barata ba, a bata a kuma rarasheta.......

Kwarin gwuiwa ne ta samu mai karfin gaske, tana kula da kanta tana murmurshi har ta gabatar da sallar la'asar
Tana shirin fita daga dakin dan sauka kasa Mama ta sake shigowa da waya a hannunta fuskarta na wani irin nuni wani alamu da suka saka Zahra tsatsare fuskar na Mama da ido
Zama ta yi ta mika mata wayar tana kallonta a hankali ta ce" Ki amsa kiran ana son a yi magana da ke"
Wayar ta kara a kunnenta, jin muryar mahaifinta ya sakata sauke murmurshi da farin ciki tana gaishe shi da inda yake komai da komai, sai dai a muryarsa ta ji abu mai kama da rauni a tatare da shi, sosai ta ringa tambayar ko lafiyarsa?

Ama amsar daya ce Alhamdulilah, sai kuma yace da ita ga wata zasu yi magana
Itace ta fara yin salama dan a tunanintama ko matarsa ce, sai dai muryar da ta amsata ta sakata zabura daga zaunen da take ta mike tsaye da wayar a hannunta ta kasa cewa komai
Daga cen dinma, shirun ya fi komai yawa, da kyar ta iya budar bakinta muryarta na rawa sosai ta ce" FATIMAH "
Muryar nan tana tunanin ko a cikin kabari ta kwana ta fito ba zata bace mata ba,.....jikinta ne ya dauki rawa ta saki wayar daga tsayen da take ta fada jikin Mamah da ta miken itama ta fashe da kuks mai sautin gaske
Da sauri Mama ke bubuga bayanta ta samu ta dauko wayar ta kara a kunnenta ta ce" Na'am ina ji Mama ce"
Aban ZAHRAh da hankalinsa ya tashi ya ce" Mamah, kuka take yi ne Zahran?"
Mamah ta yi murmushi a sanyaye ta ce" Kar ka damu, kuka dole zata yi, ama zata daina in sha Allah"
Aban Zahra a sanyaye ya ce" To MAMAH, dan Allah Mama a rarasheta, a rarasheta sosai, kin ga sauki ya fara samuwa, dukda nima bata kulani ba ko kadan ama ta yi ba zatan da ta tambayi ZAHRAN, kin ga kuwa ai sauki ya fara samuwa ko MAMAH?

A sanarwa Zahra rashin lafiya ne ya saka mahaifiyarta yi mata irin rikon nan, ta yi hakuri dan Allah"
Mamah ta sake yin murmurshi ta amsa shi sannan suka yi salama
A hankali suka zauna bakin gadon da ZAHRAN wace ta dora kanta saman cinyar ta Mama
Mama ta ce" Meye na kukan kuma?

Ke ba zaki daina saurin kuka bane ko?, Ama ai kin san abinda ake ciki, na sanar maki, kuma abanki ya sanar maki, shin kin kulaci mahaifiyarki ne?

Ina nufin ba zaki iya fuskantarta bane?""
ZAHRAh kam ajiyar zuciya kawai take saukewa, amon muryar na dake dawo mata a cikin kwonyarta, muryar da a da idan har itane zata yiwa magana ba fai da ainahin sunnanta ba sai dai wani mumunan sunna ko magana irin ta zagi?, Muryar dake kayar mata da gaba?

Wace idan har ta jita a kanta ba komai bane zagi ne da kora?

Muryar abinfa ta fi so a duniyarta kuma take tsoro kamar ranta?

Da gaske zata iya samun sauki har ta sota itama?

Kai tana ta karyara haka a rants sosai ta kuma san da wahala ya zama gaskiya........

Zuwan Auta dan shaidawa Maman an yi baki tana ta neman Maman bata samu ba ya sa ta nufo nan dan ta san Maman dai sama ta yi ko dakin na ZAHRAN ta shigo domin yau an wuni ana fitar da kayan Zahran
Ido ta zarro tana dariya ta ce" Lah, Aunty wai dama kina nan?

Mama wai an yi baki ko masu kwaliya suka ce?"
Mama ta yi murmushi ta mike dan da dabara ZAHRAN ta mike tana share hawayenta Mama ta ce" Maza shige ki yi wanka ki fito akoy mai kunshin da zata maki na hannu, shige ki fito maza ki kimtsa su maki kin ga duhun magaribar har ya shigo jama'a lokaci sai gudu yake yi
Da wannan Maman ta fice dan ta shigo da masu kwaliyar, ita kuwa Auta ta yi zamanta sai surutu take yiwa Auntyn nata
Kwaliya aka tsantsara mata ba mai kwashe kwashe ba, ama kuma harta gashin ido sai da aka saka mata mai kyau ya hau dassss saman fatar idannuwanta
Lesh ne tsantsarere aka fitar, ama ba'a daura mata ba sai da suka yi sallar magariba domin abin ya ja su lokaci sai da sallah ta riske su sannan aka gama aka daura mata dan kwali dauri irin na manyan mata ba daya kan daya ba , dauri ne mai kwali daga ciki ya dan yi sama kadan gashinta ya zubu a gadon bayanta ya yi kyau tamkar ba ita ba
Mayafin kayan aka bata bayan ya sha turare , sannan akai mata hotunna da kayansu na hotuna dan sun ce zasu turawa Hajia Luba, sannan suka sauko suka fice a lokacin tsakar gidan ya cika da hayaniyar rikicin tashin hankalin da ake yi da kyar aka barsu suka fita shima sai da MARSHAL ya karaso ne aka barsu suka fita domin Amir ya kafa ya tsare kan babu wanda zai shigo ko ya fita
Da kula MARSHAL ya ce da Amir" Zata fita ne ka kamata ko zata shigo?"
Amir da har jikinsa ke rawa ya ce" Yayanmu, zata shiga gidan tana ta labewa na hangeta na dawo daga gudu, shine na dan tsaya na gani ta shigan kuwa sai na yi kiranta, shine kwano ya fado daga hijabinta a ciki na ga abinci ne da kudi, na tambayeta da daren nan wa ya aiketa?

Ina zata je?

Da farko tace wajen maman gidan cen zata je, daga baya tace wajen Laraba ko wace?, Karshe dai na gane karya ne na janyota wajen mamansu, Mamansu sarai ta yi mamakin kudin dan kuwa a lokacin ta duba ta ga kudinta ne ama sai ta so daure mata ta nuna ta yiwu adana mata ta yi, yayanmu wai dan wani boye gaskiya a nan fa ta sake shiga bincike bincike tana fadin yarinyar da ba lafia gareta ba kusan kwana goma ko zazabi ko meye?

Ni yanzu abinda na fadawa mamansu daya ne ta bani yarinya ta fada min me zata yi da kudi kuma wajen wa ta je , yayanmu shin ta manta kwanaki ana neman mai daukan kudinta a dakinta?

"
Tsai ya yi yana ta nazarin abin
A hankali ya dubi Amir ya ce" Ka salami taron mutanen nan, ba sai an tara su ba, bara na je da kaina"
Daga yaka ya nufi bangaren su Furera
Ba tsaye tsaye ya shige falonsu a lokacin tana tsugune gaban Mamansu tana tambayarta menene zata yi da kudin da ta dauka da abinci?

Ko Laraba zata kaima ne?
Chapter 96 · 0% Book details