← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 110

Sashe 5

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Wa'alaika salam, kai wai yayane tun dazu muke jiranka mu wuce ka wani shanya mu a nan, kar ka ce min ka je wajen wannan banzar yarinyar ne mana!" Abokin nasa ya fada hadi da dan jan tsaki, hakan ya saka shi dan zabura yana waigowa wajenta dan sai a lokacin ya shiga neman wajen da zai datse hakan, ama bai sani ba, hasalima hadawarma sai da aka hada masa, tukin motarma ya iya mota ne irin iyawar nan ta garari , domin a hannun abokansa ya'yan masu da shi yake warta yana dannawa har aka dace.

A dan hargitse ya bude motar ya fice, sai dai bai yi nisa da motar ba kasa kasa sosai ya ce" Kai me yasa baka da hankali ne, amsa amon motar fa a bayane yake kake magana tana jinka meye haka?"
Abokin nasa ya ja tsaki, wanda maganar tasa ne kawai take iya ji, bata iya jin me ma'awiyan yake fada, dan ya rufo motar ama yana daf da motar
Da yannayi na rashin kunya ya ce" Ka katse mana ai laifinka ne malan zaka wani shanya manyan babs ka je wajen da ko lebe ba za'a barka ka darza ba kamar wani an fika tsatson kirki bayan mun san..................."
A lokacin ne kuma maganar ta dauke, dan ba shiri ya yi gaba da sauri yana amsa kiran.

A hankali Ta bude nanauyun idannuwanta da suka cenza launi suka yi wani irin ja ta sake zubawa a kan hanyar da ya mika yana amsa wayar
Wani irin nauyi jikinta ya dauka, nauyi mai zafin gaske, tamkar yau kunnayenta suka fara jiyo mata magana irin ta wulakanci da zagin nasabarta.....ko dan wannan ya fito daga bangaren wanda ta riga ta aminta cewa mutuwa ce kawai zata iya rabata da shi, sannan babu
a namijin da zai iya sonta ya kare hakinta irinsa?

Da kyar ta iya bude motar, bayan ta kasheta ta bar masa makulin a jiki, dan kar wani ya zo ya gane ba kowa ya yi gaba da ita, ta rufe ta shiga tafia jiki a sanyaye tamkar zata kifa kasa dan ciwon da zuciyarta ke yi
Tana karasowa kusa fa gidan abokin hadin bakin nata yana tsaye jikinsa sai bari yake, adu'arsa daya kar Oga ya fito a lokacin da zata dawo, fatansa daya ta dawo ta shige gidan nan tun kafin a san bata cikinsa,
Magana yake yi mata jikinsa na rawa yana nuna mata maza ta shige, Oga fa na nan, hakan ya sa gabanta sake yankewa ya fadi, duda bata gane wane a cikin ogannin nasu ba, abinda ta sani shine su dukka ogannin nasu babu daya da yake wasa da su, daga wansa zai iya saka bulala ya zane masu jiki tas, sai wanda kallonsa ke fasara idan ka yarda ya damkeka sai dai wani ba kai ba
Hakan ya sa ta dan daga kafa, sannan ta shanye abinda ke ranta ta shige gidan a darare ta bi ta cikin shukoki har ta samu ta isa wajen babar bishiyar da take zama lokuta da dama , a lokacin ta ja ta tsaya tana jin tamkar fitsari zai zubo mata sakamakon jin an ce WAYE?

Jikinta ne ya dauki rawa, zufa na neman karyo mata, lokaci daya kuma ta juyo wajen da aka daleta da hasken fitila dan koma waye ya gane wacece din da yake son sani.

A hankali ya sake zuba mata ido, tun daga yannayin tsayuwarta, gumin da take tsatsafawa, idannuwanta dake ta kasa sunna sama, fuskarta da ta d'auki ka, har zuwa hannayenta da ta damk'e hijabinta take wani abu kamar mai jin kashi.

Sake daleta ya yi da hasken nan yana kallonta , muryarsa a dake ya ce" Fitsari kike ji ne?"
Tambayar tasa ta yanzu ta sakata gane wanene a wajen
Shikenan, ashe ogan da ake nufi yana gidan kennan?

Ai su sun zatama an tada shi daga garin an maida shi wani garin har sunna murna da samun yanci a cikin duniyarsu, sai gashi yai ta yi gamo da muryarsa a irin wannan lokacin da ta kwaso tarin tashin hankalinta.

Kai ta sada, hawaye ya shiga bin kumatunta, hawayen da ita kanta bata san tana iya zubat da su ba, batama san a kan me zata zubar da su a nan a gaban wannan mutumen da ta san yana cikin masu kyankyaminta.....to wannan tambaya tashi batama san ta mecece ba sam.

A hankali ta sake sada kanta sosai, ta kasa bashi amsa.

Baki ya tabe ya kashe fitilar ya mayar aljihunsa sannan ya yi gaba wajen motarsa ya shige ya tayar ya shiga juyar da ita dan barin gidan.

Da sauri ta dage hijabinta ta kalkala da gudu ta bi ta cen baya , hakan ya saka shi take birki ya zubawa hanyar ido, sannan ya sake dawo da yannayinta a cikin idannuwansa.

A hankali ya ji kansa ya sarra masa, sanadiyar wani tunani da ya shigo cikin kwakwaluwarsa.

Take motar ya yi ya fice a gidan da gudun gaske dan tuni aka bude masa get.

Cikin sand'a ta lek'a falo, gabanta ne ya sake kwonci kwonci ya fad'i sakamakon hangi Hajia na falo bata hau sama ba, duda baban fargabarta ace hajiar ta hau saman ta bi dakunnansu ita bata sameta a nata ba, gaskiya ba zata kuma yarda ta fita a irin wannan lokacin ba, haka kawai salon ya sakata a uku , bama zata kuma fita inda yake ba, domin ba zata zauna rayuwarta a gida a tsangwameta a tare da shi a tsangwameta ba.

Ta jima a tsaye a wajen nan tana addu'a tana zufa, har dai Hajia ta mike ta kakashe fitilu da sauransu sannan ta sahiga hawa sama da carbinta a hannunta da gilashinta na karrin karfin gani.

Da sanda take dan bin bayanta har ta shige dakin farko, ita kuma da sauri ta kama kofarta ta bude ta shige cikin hanzari ta rufo ta cire hijabinta ta yi wurgi da shi cen san bed, tana kiciniyar cire rigar dake jikinta ta ji an bud'e k'ofar an shigo lokaci daya ta idasa sakarwa ta nemi samin fitsarin mararta har abinda ke d'aure da gashin kanta wato Ribom ya fad'o k'as ya daki k'afafuwanta.

K'afafuwan nata Hajia ta bi da kallo, sannan ta sake d'auko kallon ta dawo da shi har zuwa wajen fuskarta.

Tsare fuskarta ta yi da kallo, hakan ya sa ta sake d'aukan yanayi irin na wanda ta d'auka a d'azu da take gaban wancen mutunen.

"Ke zo nan!" Hajia ta fad'a da d'an k'arfi tana nuna mata gabanta bayan ta nunata.
*Alhamdulillah.*
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_4_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
"Ke!

Zo nan." Hajia ta fad'a a dake da d'an k'arfi, sannan tana nuna gabanta, zabure ta duka ta d'auko ribom d'inta da ya fadi ta shiga daura shi jikinta na bari tamkar zata kifa ta nufo wajen hajiar ta nemi dan dukawa dan ba zata tsaya mata k'erere ba, hajia bata d'aukan wannan rainin.

Damkar hannunta hajia ta yi ta janyota sosai ta shiga dube dube a jikinta har zuwa sket dinta da ya saketa sosai bai rike jikinta ba
Sake zuba mata ido ta yi sannan ta saki b'oyayyar yar ajiyar zuciya a hankali ta ce" Kuka kika yi ne?

Me kike yi har karfe goma sha daya na dare ke neman yi baki kwonta kin yi barci ba?"
Bakinta dake bari kad'an ta bud'e a hankali ta ce" Mamah,dama, sallah zan yi ne."
Fuskarta ta sake kurewa da ido, sai kuma ta ja numfashi ta shigo da kyau dakin ta zauna bakin gado ta ce" Je ki yi alwallar ki fito."
Da sauri ta juya ta shige tana zarro ido had'i da dafe gaban kirjinta, da kyar ta iya dauro alwallar ta fito ta nufi salayar da Hajia ta nuna mata still tana binta da kallo.

Hijabinta ta saka ta haye salayar ta tayar da sallah , a hankali a hankali jikinta dake bari ya daina har ta zurfafa ta yi raka'a biyu kadai ta salame ta shiga danna yan yatsunta kanta a kasa.
Chapter 5 · 0% Book details