Sashe 32
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wai ko dandani bata ce na taba ba Fatina?"
Fatima ta yi murmushi itama tana jira ne Auta ta ajiye ta idasa ta ajiye din itama a sanyaye ta ce" Abahna na girka maka mana na kawo?"
Murmushi ya yi yana girgiza kai ya dubi Aban Hafeez ya ce" Ka ji yar aljannah ko?
Y'ar nan mijinta ya huta, bata da kiwya ko ta kankanin lokaci, ga iya miya bama idan ta taushe ce da waina kana iya taune yar yatsarka baka kula ba....."
Dariya Aban Hafeez ya saka har yana dan tafawa ya juyo zai yi magana ya ga Baban gida ya mike yana amsa waya ya dan kare masa Fatin Aba
A lokacin ne shi kuma Baban gida ya yi kiran Amir ya mike zai nufi hanyar fita wace dole zai bi ta wajen yaren , da yar yatsarsa ya fara korar Auta dake iya yi an samu hira da ABAH, sannan ya saka yan yatsunsa ya amshi kwondon nan ya ajiye a nan da yatsarsa ya masu nunin su tafi shi kuma ya fice yana amsa wayar, hakan ya saka Aban Hafeez juyowa yana fadin" Ai kuwa Aba zan zo na sha waina na more da miyar taushe in sha Allahu ai wannanma ka ji sai kanshi yake yi sosai"
Aban ya yi murmushi ya ce" Baban Hafeezu kai dai ajiye yawunka har ku karasa gida, ina fada maka zaka ci girki....."
Ire iren hirarsu kennan, sukan yi ta adini, su yi ta raha, sannan su dauko hirar rayuwarmu a yau, a haka ABAH ke karra yi masu nasiha cikin hikima, kuma ta haka yake karra jin dadin wa'inda ke tare da d'ansa, idan har baka yi masa ba, wato tarbiyarka ba mahadin ta yaronsa bace tsaf zai hanna tarayar, dan ya fada ya karra a duniya babu malami mai saurin koyar da darasi irin aboki
Da wuri suka baro wajen da ABAH, sunna fitowa aka amshi kayan abincin aka kai mota su kuwa suka shiga takawa dan nufar motar
A hankali ya dubi Aban Hafeez ya ce" Freind ina zuwa "
Amsawa ya yi yana kallonsa har ya shige bangaren Mamah shi kuma ya nufi motar dan jiransa
A bakin kofar bayan ya hayo saman tare da Mamah dake sake fadin ai gwara kai ka gagaura mata marin ta yiwu ta ji idan kai ka yi, a kan turare babu irin nasihar da banna yiwa yaran nan, ama ka ga ita da Adawiya sai dai idan basu buda ido daga saman gadonsu ba, ina iya cewa tun a nan suke shafa shi kafin su yi wanka su shafo a bayi su kuma fito su yi wanka da shi!"
Maman ya dan zubawa ido har ta dasa aya, ya gyada kansa a hankali ya kwonkwonsa kofar sannan ya dakata
"Ke Auta idan na baki takalmin nan ki ce min ban san ciwon kaina ba, ina ce da aka ce mu dauke shi kiyawa kika yi yanzu kuma daga gani na saka ki ce da ke ya dace ba fa zan bayar ba ki yi tafiyarki kawai malammmmmmmmmmmmm!" Ta bude kofar, bakinta ya yi dif, idannuwanta suka ruko waje, daga ita sai daurin tawul ta yi daurin kirji da shi kanta na tsagon ruwa fitowarta kennan daga bayi wanka ta yi ta fito ta ji bugawar, ta zata Auta ce ta sake zuwa dan amsar takalmin da ta ki bata, shine tun kafin ta bude take masifantar Autar har ta bude hankali kwonce dan su yita ta kare idannuwanta suka sauka a cikin nasa , lokaci daya kirjinta ya yi wata mahaukaciyar yanke ya fadi...........
Wani dan karamin ihu ta saka na razana hadi da sake zarro idannuwanta, sannan ta juya a guje ta nufi bayi tana tare tawul din dake neman sauka gaba daya daga jikinta jikin nata na rawa hankalinta tashe ta shige ts maro kofar tana sake rukunkume tawul din jikinta hadi da ambaton yayanmu wayo yayanmu
Mamah da itama ta zarro idon ce kuma abin ya bata daria, dan tunda ta bude ya ga halin da tale ciki ya sada kansa kasa tamkar yana gaban sirikinsa ya cire dubansa daga barin gaba daya yana kallon gefe har yanzun kuwa bai juyo ba, kansa a cen barin yake bai juyo ba
Tana yar daria ta shiga tana fadin" Shiriritar wofi, gobema kya bude dakinki da kin ji an buga baki tabatar ko waye ba, kuma dole ki saka hijab ki fito ya miki shegen duka a kan aiki da turaruka masu karfi dan ba zan zo na maki aure na kaiki gidanki ba abin kunya mijinki ya kawon karar turaran da kike sakawa ya yi yawa idan zaki fita,ke da yar uwarki dama ina neman rana irin ta yau da zai fada maku tunda shi kunna jin tsoronsa, Baba bara na bata hijabinta ta fito ka wanwanka mata mari zata fi ganewa dan Zarah kam ba dai taurin kai ba!"
Mama na mita ta bude wajen hijaban Zahra ta dauko wani lafcece mai nauyin gaske sannan baki ta karasa ta bude bayin ta mika mata sannan ta ja ta tsaya tana jiranta har ta gama sakawa ta fito jiki ba karfi, kanta a kasa , tana tafe gabanta na dukan tara tara na tsoron dukan da Mama tace ya masu saboda turare
A hankali ya kuma juyowa, sai ya samu kansa da shayin sake dago idannuwansa dan bai san me kuma zai iya gani ba
A dan fizge ya iya dagowar yana dan tsayuwa kusa da kofar ya ciro maganar bakinsa da kyar ya ce" Ki dauko min hijabin dazu, da kuma dukkan turarukan saman cen"
A marairaice ta kalli Fuskar Mamah, sai ta ga ta sake daure fuska irin a mata maganintan nan, hakan ya sa da dan sauri ta karasa ta ciro hijabin, sannan ta je wajen turarukanta tana kallonsu idannuwanta na cikowa da kwallah
A sanyaye ta dauki wata yar farar leda mai dauke da kampanin da ake masu siyaya sabuwa dal sai kanshi take yi ta kwashe kayan ta zuba , ama ta bar kwaya daya tak wanda ya figar mata zuciya, kanshinsa mai sanyi ne sosai ta juyo da su ta nufo inda yake ta rage tsayinta sosai tana mika masa kanta a sade
Kayan yake kallo ta kasan ido, a hankali ya ce" Shi dayan fa?"
Idannuwanta ta dago da suke cike taf da kwallah ta juya ta koma ta dauko dayan ta dawo ta saka shi a lokacin hawayenta suka bale a saman kuncinta sunna zuba, shi ya zubawa hawayen ido cike da mamaki, Mamah kuwa ta yi saurin dauke kanta dan so take yi ta koyi jajircewa a gaban Zahranta, idan tace no ya zauna a no din!
Kayan ya amsa, santsin hijabin ya saka shi sake kallon yadin, a cen kasan makoshinsa ya ce" Irin yadin nan shi daya ne?"
Mamah ta juyo tana kallonsa, sai kuma ta ce" Wannan shi daya ne baban gida, irin yadin nan"
Bai ce komai ba ya juya da su a hannunsa ya nufi dakin dayar
Mamah kuwa ta rasa rarashinta zata yi ko me zata ce, domin yana tafia sai ta kifa kanta a hannun Maman bayan ta janyo hannun ta fashe da kuka harda su girgiza kai a hankali tana fadin" Mamah turarena, Mamahna ba zan kuma shafa da yawa ba ama idan aka rabani da turare yaya zan yi rayuwa babu?"
Sosai zuciyar Mamah ta tsinke, ta ringa kikifta ido kirjinta na dokawa, a sanyaye ta shiga rarashinta tana fadin" Yi hakuri zan siya maki wasu ai, in bama abin baban gida ba cewa fa kawai na yi ya maku nasiha ama sai ya zo ya kwashe komai?