Sashe 41
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Salamarsa dauke da wata katuwar jaka a gefen hannunsa sannan ya ba likitar dama ta shigo ya saka Amir ajiye nasa Alkur'anin ya nufe shi yana masa sannu ya amshi jakar wace keda mugun nauyin tsiya ya kaita gaban ABAH ya ajiye ya sake dawowa ya dauki kayan aikin likitar ya kai ya sake ajiyewa sai kuma ya fita inda aka ce akoy wata likitar dauke da wasu kayan ya mata jagora dan su biyu ne ya je ya mata ya dawo sunna shigowa Marshal na fadin" Zaman inaga ya isa haka kowa ya tafi dakinsa......"
Lokaci daya yaran suka nemi mikewa, Mama ta yi gagawar dakatar da su ta dube shi ta ce" Aban docter ai basu yiwa Abansu a dawo lafiyar ba, kuma bamu yi addu'a ba ai"
Dan dakatawa ya yi,sai kuma kasa kasa sosai ya ce" To su je kofa su dakata a gama duba kafar sai su dawo"
Yanzun kam bata hanna ba, su kuwa kowace da sauri ta fice suka tsaya a kofar kowa da wanda yake shiri sunna zantawa, sai dai babu wanda bai yi mamakin gannin wai yau Zahra ce tare da su Rukaya, babu abinda ke saka masu faduwar gaba kuwa da son sake kallonta sai idan ta dan saki murmushi, yau murmushinta ya fi damuwarta yawa a wajen hakan ya takura kwonciyar hankalin wa'inda ke jin haushinta sosai
An dauki lokaci kafin a gama duba ABAH, a kadan an kwashi sama da awa, tun sunna tsaitsaye har suka zauna sunna jiran tsamani
Amir ne kadai ya yiwa likitocin rakiya fuskarsa babu alamun annuri ko kadan, kamar a yanzu ne wani abin ya taba zuciyarsa, yana dawowa ya saka suka shige gaba dayansu falon suka zauna a wajen da suka saba zama
Idan har zaka bi fuskokin iyayensu da kallo, tabas zaka karanci hali na damuwa a shinfide a sama, ABAH kuwa yana zaune ne hannunsa a cikin na Baban gida idannuwansa a lumshe ba zaka fahimci ainahin halin da yake ciki ba sai dai shi baban gidan kana kure masa kallo zaka ga irin jan da idannuwansa suka yi sannan hankalinsa kacokam a kan mahaifinsa ne yana dan gyara masa zamansa da rigar dake jikinsa jalabiya fara kal
Shiru ne wajen ya dauka na dan lokaci sai kuma Abah ya bude idannuwansa a hankali ya sauke masu duba yana kallonsu
A dabarance ya share yar kwalar da ta tarun masa a idannuwansa a sanyaye ainun ya ce" Baku yi barci ba?"
Babu wanda ya iya amsa masa, dan yannayin sanyinsa ya saka su a halin rudu
Abah ya sake dan gyara zamansa a tausashe ya ce" Alhamdulilah, in sha Allah gobe zamu tafi ni da yayanku da kuma Mamanku, kamar yadda nake fada maku kulun idan wata bukata ce ta taso ga Babana nan ku sanar masa ko wace iri ce kun ji? , Koda bana nan shi yana nan.........., Sannan ina mai umartarku da ku ci gaba da kula da kawunnanku, da tarbiyarku ku yiwa yayunku biyaya sannan ku ji tsoron ALLAH a dukan abinda zaku yi na yau da kulun......, Kamar yadda kuka sani wannan yayanku ne kuma uba a gareku dan baban wa uba ne, ku sani ni da kaina ya isa da ni bale ku da na haifa, da ni ko ba ni ku yiwa umarninsa biyaya kun ji?......."
"Abah" Marshal ya fada a hankali yana kallon fuskar mahaifinsa fuskarsa na sake daukan ja , girarakinsa na harhadewa idannuwansa na bada wani irin kala na raunin dake cikin zuciyarsa
Abah ya yi murmushi ya ce" Ka barni mana na yi magana tun inada karfin yi?
Ba wasiya nake bara masu ba fa ama ai yannayin rayuwa ne ko?
Idan sai lokaci ya kure min ban fadi komai ba kuma fa?, Kun ji ku saurareni baki dayanku, bani da lafia kuma ciwona mai girma ne, ina fatan samun lafiya a wajen ubangijina ko wace iri ce, ba zan yi wasa da yi maku nasiha da fada maku gaskiya ba, ku da kanku kun san kunna wasa da zumunci kawunnanku a rarabe suke daga iyayenku har ku, ku sani ku na haife ku du wanda ya yi watsi da zumunci koda bayan raina ne ba zan taba yafe masa ba, ku girmama yayanku ku girmama iyayenku, du wace ta raban kan Y'ayana ba zan taba yafe mata ba, haka kuma du wace ta bi Aba da wata manufar ita da ubangijinta, babu wanda zai musa adalcinsa a gare mu sai wanda baya son gani, bani da damar gyara maku ko lalata maku sai dai na yi maku nasiha, in sha Allah auren wasu daga cikinku da zarar mun dawo za'a shiga shiri dan ba zamu jima ba, kafin nan ku ci gaba da rike mutuncin kanku ku yiwa adini biyaya kun ji?"
Babu wace jikinta bai yi sanyi ba, babu wace bata ji hankalinta na neman tashi ba har ya salami yan matan suka fita kowace hankalinta tashe wata har tana sharar hawaye ya koma kan samarin suma ya yi masu nasiha ya salame su sannan ya dawo kan matansa, wa'inda kowace ke hawaye sunna kallonsa
A tausashe ya yi masu nasiha, harda su tsokanar ashe ana sonsa?
Sannan ya masu nuni da ai cuta ba mutuwa bace nasiha kuwa ba yau ya fara ba, kawai ta yau ta dan bambanta ne dan ya fara ankara da wasu laifuka nasa da sake nasa a tsakaninsu baki daya.........., Sun dan karra jimawa sannan suka tafi kan sai an jima kadan zasu masa rakiya dan tuni lokacin ya kusa
Mamah jiki ba kwari ta mike tana kallonsu ta ce" Bara na leka yan matana na ga wajen wa zan barsu sai na dawo"
Tunda ta fito ta ja ta tsaya a mamakeken gidan ta rasa inda zata nufa
Abubuwa sun yi mata yawa, zuciyarta ta yi nauyi ta rasa me zata yi ina zata dosa me zata rika
Jiki ba kwari ta nufi dakin wace ke bi mata a matsayi a dakunnan matan docter dan a ganninta ya dace ta fara darajata dan itace baba idan bata nan
Zama ta yi a saman kujera bayan sun sake gaisawa a tausashe ta ce"
*24*.
D5
Zama ta yi a saman kujera a tausashe ta ce" Uman abul dama zuwa na yi na maki maganar yara, tunda bana nan zasu dawo nan har na dawo, kin san ba zan tafi na barsu su kadai a cen bangaren ba babu baba"
Ba alamun nuna wata damuwa ta ce" Ai ba damuwa Hajia sunna iya zuwa su hade da yan uwansu"
Murmushi Mamah ta yi tana sauke ajiyar zuciya ta mike zata tafi tana godiya, sai kuma Uman Abul ta dakatar da ita
Cikin halin ko in kula ta ce" Ama hajia ai banda yarinyar nan ko?"
Dan tsura nata ido Hajia ta yi tana son karin bayani
Maman Abul ta dan kawar da kanta ta ce" Kin san ai samari ne da ni da yawa yan matan kalilan ne, ga makaranta ana fita da sauransu gasu du ba wayon kirki, ita kuma ba muharamarsu ba, gaskiya ba zan si ganninta a nan tare da su ba ta je wajen mamanta mana tunda dai tana nan ko?"
Ido kawai hajia ta zuba mata, ta rasa amsar da ta dace ta bata, ta rasa me zata ce sai binta da duba take kamar bakuwar halita har sai da ta dan motsa tana dauke kai sannan ta dawo hayacinta
Idannuwanta ta lumshe ta sake budewa tana kallonta a hankali ta ce" Kina nufin Zahra?"
Uman abul ta gyada kai tana sake cire kanta ta ce" Eh ita fa, maman abul ki fahimceni, ba da wata manufa na fadi haka ba, sai dan na kiyaye tarbiyar Y'ayana"
Mamah ta sada kai ta dan dauki lokaci a haka sannan a sanyaye ta ce" Hakane kuma, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"
Da ido ta rakata har ta bacewa ganninta cike da mamakin amsar da ta samu daga bakin Maman Baban gida,lalle ta fara damuwa da yannayin matar nan
Mama kuwa bangarenta ta nufa direct
Tana zuwa ta same su a falo sunna zazaune kowace jiki a mace sun yi shiru babu mai yiwa yar uwarta magana sunna dai zaunen ne kana ganninsu zaka fahimci sunna cikin damuwa ne
Zama ta yi saman kujera tana amsa sannun da suke yi mata tana binsu da kallo ta ce" Lafiya na ga kun yi zuru zuru da ku?"
Auta ce ta iya budar baki ta ce" Mamah wai Abanmu rasuwa zai yi ne ko menene?"
Mama ta dan kura mata ido sai kuma ta yi murmushi ta ce" Auta dama bawa ya san lokacin mutuwar wani ne?
Ko cuta an fada maki mutuwa ce?