← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 110

Sashe 16

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

In wasu nema har sa bari a yi shekara domin a hausa muna daukan rasuwa da mahimmanci sosai, idan muka rasa wani namu abin na taba mu, munna jimawa kafin mu saku sosai, su kuwa gashi tashi daya har sun dubi haka, duda abu ne mai mahinmanci sosai, shi din kansa a yanzu ai zai shiga hali ne na takura na rashin mace a gefensa dan kuwa wanda ya saba da kulawa irin ta mace yakan shiga hali na matsi idan ya wayi gari babu kulawar nan, ko a baka abinci a kan lokaci ai alkhairi ne, bale sauran bukatu nantau da gobe, sai kuma maganar salihi da shi din ya so bashi dariya, wai bawan Allah baya cewa komai wai mu kaishi a ringa cuta masa
....... uhum lalle Zuwaira bata san aljanin danta a zuciyar mararsa jin cikin gari ba, rashin kawo kukan iyalinsa sun masa wani abu kuwa yana jin dadin haka dan hakan zai kawar da wasu rashin jituwa a tsakanin iyayen miji da matarsa
Da kula ya ce" Yaushe suka yi maki maganar?"
Mama ta ce" dazun nan kafin na rako su nan, kuma wai Baban gida ya tashi ya tafi ya barni da su wai abinda muka yanke ya yi daidai"
Da mamaki ya ce" Shi Baban?"
Hajia ta tabatar masa kwarai kuwa
Aba ya sake yin dan tsai , sannan ya ce" Kin gane, in sha Allah lamarin nan zamu tsaya mu fuskance shi yadda za'a ji dadinsa, kin ga idan adini muka yi duba, wanda a cikinsa muke, dokokinsa muke bi dan son samun rabauta, haka din ba laifi bane, domin mace aka ce ta yi takaba ba namiji ba, namiji ko yau iyalinsa ta rasu ana iya aura masa wata yana iya tarewa da ita, sannan amsar da ya baki cewar ko yayane kika yanke dan ke kika haife shi, kai tsaye ba zai aminta ko ya ki aminta da abun bayan gaki a zaune ba, wannan ladabi ne irin na
an docter baban Ahmadu jikan Sulaimana, zamu fara basu lokaci, mu yi bincike a tsanake, mu fadawa Allah, ko yayane muke son mu ganshi da mace ba zamu dauki ko wace kala mu hada su aure ba dan mun haife shi ko dan mun isa da shi, yana da haki a kanmu na yin binciken macen da ya dace ya aura, in har alkhairi ce a gareshi ki kwontar da hankalinki Allah ya tabatar mana, idan kuwa ba alkhairi bace Allah ya hanna"
Da dan damuwar ta ce" Docter yayar matarsa ce fa, itama matar tasa ta girmeshi fa, shekaru kusan biyar tsakani kennan?"
Da mamaki yake kallonta, sai kuma ya ce" Na san dai ba addini kike son ce min ya hanna ko ya yi nuni da yin hakan ana wahala ba, ko so kike ki ce min ta fi karfin yaronki ?"
Kasa kasa ta kalle shi tana soke kai dan yadda ya yi tambayar harda ta neman magana da son sakata fadin abinda bata yi niya ba!

Gwauron numfashi ta ja sannan ta sauke, kwarai kuwa maganar Docter haka ce, Allah shi kadai ya san yaya gobe take, ko menene ka fara kai kukanka gareshi shi zai saka ka a hanyar da ta dace da kai
Zata je ta dukufa ta yi ta fadawa Allah, Adu'ar mahaifiya ba zata taba faduwa kasa ba, gaba daya sai lamarin duniya ya sake fice mata a rai, watau dai wanda ya mutu shi da mutuwarsa ko?

Allah ka rufa mana asiri.

Mikewa ta yi ta masa salama domin ta saka matarsa ta tashi tun dazu babu dadi, in sha Allah gobe idan ta zo zasu karra tataunawa a kan lamarin Baban gidan
A daidai lokacin da suke wannan tataunawa, a irin lokacin ne shi kuma yake zaune a office din abokinsa Docter Habubakar
Hoton cikinta da aka dauka ne a gabansa yana kallo da kuma bayanin da docter ya yi masa
Ajiyar zuciya ya sauke hannunsa daya a jimke a saman takardar hoton ya dago dubansa ya ce" ka san a zamana da ita, ta matukar dauki magungunnan matan nan da mahinmanci, yawancin lokuta kuma yayarta ke aiko mata da su, wasu kuwa ta siya da kanta........., Koma menene ya hadasa mata wannan zubar jinnin har ya yi sanadiyar mutuwarta sai na nemo shi, kuma ko waye ya kawo shi kasar nanma sai na daure shi!"
DOCTER Habubakar cike da jin ba dadi a zuciyarsa na halin da Mar
chal ke ciki ya ce" a gaskiya ko menene idan ba poison bane, toh wani mugun abu ne da aka hada dan ya zubar mata da jinnin !,ko menene yana iya kisa a sha ko a matsawa, irin yadda ya ringa sakata zubar da gudajin jinnin nan baki ba karamin guba ne ba"
Kai ya girgiza yana dafe gabain goshinsa, a nutse ya ce" Na gode docter, Please ka hada min duka kaf takardun gwaje gwaje da magungunnan da kuka yi mata anfani da su da dukkan hasashenku da abinda bincikenku ya baku, zan gabatar da bincike a tsanake bi'izinillah"
Da wannan suka yi salama ya tafi domin sai ya harhada komai zai kawo masa da kansa
Koda ya karasa office ya kasance ne hankalinsa a matukar rabe gida biyu, daya na tunanin lamarin nan, dayan kuwa a kan rigimar da ake yi da shi kan sai ya saka hannu a kan daga yau yan mata sunna da yancin yawo da pant ma idan sunna so , domin yancinsu ne, du wanda ya zage su ko ya nemi shiga hakkinsu sai iko ya kama shi an ja shi an yi shara'a da shi
Takardar ya dauka ya ja waje ya sakata ya rufe sannan ya ci gaba da aikinsa dan yana son abinda zai dan dauke masa kewa da tunanin iyalinsa,
A saman lebensa ya furta" Allah ya maki rahama Manal, Allah ya sa aljanna ta zamto makomarki, ni dai baki yi mun komai ba,koda kin min na yafe maki, ina fatan nima baki tafi da fushina ba Manal" ( Ya Allah ka azurta mu da samun yafiyar abokanan rayuwarmu a kowani Hali )
Bai samu komawa gidan ba, sai kusan karfe hudu Amir ya nemi izinin shiga office dinsa yana dauke da kayan abincin da Mamah ta yi kiransa ta saka ya kawo masa dan ta ji shiru bai zo ba kuma tana kiransa bai daga ba
Abincin yake kallo, Waina ce ta yi hulu hulu ta yi jajir ta yi kyau a ido, ga kanshi dai ya cika wajen, sai miyar taushe ta samu wadatacen naman rago itama sai daukan ido take sannan babu mai a kwonce a cikinta kamar dai yadda baya son abinci da mai din nan
Dan kallon Amir ya yi yana son tambayarsa wa ya girka?

Sai dai yan nauyin bakin suka rufun masa har ya zuba masa a plate ya ajiye ya bude frij dinsa ya dauko jus dinsa da ruwa ya ajiye cikin girmamawa ya sanar masa zai koma office idan an jima kadan zai dawo ya kwashe kayan
Idannuwansa ya lumshe masa alamun godiya yana kallonsa har ya fice sannan ya matso abincin ya yi Bismillah ya fara ci a hankali da tunanin ba zai taba samun dandano irin na hannun Manal ba, yana fara ci ya ji test din wainar ya yi masa sosai a saman harshensa, ko dan yana tare da yinwa ne ko yayane?

Shi dai ya ji ba laifi wainar ta birge shi dan haka ya ci iya cinsa ya koshi ya yi hamdallah sannan ya mayar gefe ya mike dan fita zai yi zagayen cikin gari, dukkan abinda zai dauke masa kewa yake nema ido rufe dan baya son damuwa a rayuwa, rasuwar iyali kuwa babu abinda ya kaishi damuwa, da aka sanar masa babu ita sai da ya ji kamar zai summa a tsaye, kallon gawarta kawai yake yi ya rasa abin fada har sai da Abansu ya zo ya tunasar da shi abu mafi mahimmanci watau ya gafarta mata sannan ya yi mata addu'a shine kawai soyayar da zai iya nuna mata, su Mama kansu haka jikinsu ke rawa cewa suke kennan abin baba ne ya fade shi a nutse babu tashin hankali?

Gaba daya rasuwar ta zo masu a ba zata ksmar yadda mutuwa ta iya aikin zuwar ba zata
Yana tuki yana kallon yannayin gari maganar NIHAL ta fado masa
Dan murmushin yake ya yi kawao ya girgiza kansa
Shi fa ba maganar shekarunta dake saman nasa bane damuwa, meye a su yan shekaru hudu dake tsakaninsu shi ko wace ta girme masa da shekara goma zai zauna su kurewa junna man kai, tassssss, dan ko a yanzu dama bai yi ra'ayin zama da yarinya ba, dan baya son kayan haushi da saka ciwon kai da raini, ..........sai dai irin yadda ta kawo zalamarta a bayane ya matukar bashi mamaki, kamar wace take jiran haka ta faru?

Ya gaza dora abin a matsaya daya, shin Kwadayi ne ko wauta ce?

Ko kuma itace sanadiyar........................................................
Chapter 16 · 0% Book details