← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 110

Sashe 40

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hannunta ta ji an rike a tausashe Rukaya ta ce" Kula mana zaki taka dutse fa ZAHRA......"
Da mamaki ta zuba mata ido tana kallonta ta duka ta dauke dutsen ta je ta kaishi cen jikin garu ta yadda wani ba zai taka ba bale ya masa lahani sannan ta dawo ta ce"
*23* D5
Da mamaki ta zuba mata ido tana kallonta a lokacin da ta duka ta dauke dutsen ta je ta kaishi cen jikin garu ta yar saboda kar wani ya taka ta dawo ta ce" Kamar yadda kuka sani idan an yi zama muna iya fuskantar abinda bai yi mana ba, tsankwale tsankwalan fada daga yan uwanmu wasu lokutan magangannun da suka zarce misali daga iyayensu zuwa Mama, duda da wahala a yi zama da manyanmu mu ga irin hakan dan ana jin tsoronsu, abinda zan fada maku gaba dayanku a nan shine kar na ji kar na ga wace ta yi yinkurin mayar da wata magana a zaman da za'a yi a falon cen, ba dan muna jin tsoron kowa ba, sai dan zuwa ne zamu yi dan yiwa mahaifinmu salama, ba adalci bane mu barshi da tunanin baya da tunanin ta yiwu muna nan muna kashe kawunnanmu, ina fata kun fahimta?"
Su biyun ne suka iya amsawa, ita kuwa ZAHRA kallonsu take daya bayan daya irin abu yana bako a garekan nan dan bata taba sannin abinda suke yi kennan ba idan sun kadaice, wato nasiha a tsakaninsu har sai da Rukaya ta sake dubanta ta ce" Ke tunanin me kike ina magana ban ji kin amsani ba?"
Da sauri ta kalleta har tana sakin ajiyar zuciyar da bata san ko ta meye ba kafin a hankali ta furta irin abinda sauran suka ce watau " In sha Allah aunty Rukaya zan kiyaye" sannan suka ci gaba da tafia sunna hangen daidaiku na shigewa tana tare da su hannunta cikin na Auta har suka shige Falon summa da salamarsu a bakunnansu sannan suka yi dan turus dan gannin a zaman harda YAYA AMIR, idan kuwa yana cikin zaman to fa babu wai yan wadinnan dakin sunna wancen barin yan wadincen sunna wancen barin gaba daya ake zaunawa waje daya banda Zahra da mamanta ke yafitarta ta je jikinta ta zauna, domin du irin tsoron da suke masa idan ta je cikinsun nan kafin a tashi sai an guma mata abinda zata kwana tana kuka a boye har sai da ta sani ita kuwa ta murje ido take wareta daga cikinsu dan ta kula su din basu da kunya bakinsu kuwa baya tsoron jazawa kai masifa
Wurin zama suka nufa su ukun, a lokacin ne ita kuma ta dan janye hannunta da nufin nufar Mamah wace ta mata alamun ta zo kusa da kafarta ta zauna
Ja Rukaya ta yi ta tsaya ta juyo da hannunta ta mata nuni da wajen da zata zauna a kausashe sannan kasa kasa ta ce" Wuce mu je"
Yanzun kam ido kawai ta iya kiftawa tana kallonta ta kasa motsawar
Walahi har a cikin ranta take jin tsoron haduwarta daga su sai ita
Tana matukar jin tsoron hakan fiye da tunaninsu
Bata san yaya zata kwatanta tashin hankalinta ba, dan a cikinsu akoy masu yi mata kisan mumuke akoy kuma wadinda kallon idannuwansuma bata son yi a rayuwa dan sai ta ga sun bar mata kallon dake tuna mata wacece ita a kowani second, irin mugun kallon kyankyamin nan
Adawiya ce ta dawo ta ja hannunta ta kaita wajen nasu ama tsakiyarsu ita da Rukaya domin sunna zuwa sai ta nuna mata wajen da zata zauna ya zamto sun sakata a tsakiya, Auta kuwa daga gabansu a zaune sun yi zaman nan na tarbiya haka kuma kunnayensu a kan kowa, yau a shirye suke du wace ta yaba mata magana zasu tare mata sai dai yaya ya hade kawunansu ya yi ta jibga
Mamah kuwa tana binsu da kallo a idannuwanta tana nuna dan alamun mamakin yannayinsu na yau, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta sake kallon ABAH wanda yake jurewa iya jurewa dan kar ya nuna cewa kafar na damunsa a gaban ya'yansa da matansa bayan ciwo take tun zamansa sai gumi yake yana karawa du irin sanyin falon, tana yi tana duba agogon dakin, a kala ta fi minti ashirin da wani abu da Baban gida yace kar a yiwa kafar komai zai zo da wanda zai masa allura a kuma daura masa abinda likitan da zasu je gani ya fada, abin aikin ne da likitan ya tura bayan ya siya ya sauka a filin jirgi sun tafi su dauko su wuce dan kafar ba zata juri doguwar tafia babu abin nan na magani
Ajiyar zuciya ta sauke ta sada kanta tana jin zuciyarta na yi mata rauni, ciwon mijinta shine abu mafi girma dake dagargazarta a wannan lokaci, ta jima rabonta da yin sanyi a kowani lamari irin haka, tsoro take ji a cen kasan zuciyarta, tsoron mai karfin gaske ne
A hankali ta sake dagowa tana bin matansa da kallo kafin ta maida kan tarin
ansu baki daya da kallo
Subahanalah mazan basu fi a irga ba dan sauran du wasu na makaranta, wasu nemansu a wani garin ne basu samu shigowa ba sun ce sai sun dawo zasu samu shigowa....., matan sun fi yawa, banda wa'inda suke dakunnan aurensu suma Doctern ne ya hanna a sanar masu dan baya so kulun sunna hanyar zuwa gida......

Gaba daya taron nan bayan mijinsu itace baba...........

A hankali sai ta shiga tunanin kanta da rayuwarta.........

Shin anya kuwa girman nan dake kanta tana rike da shi a matsayinta na baba da adalci ko tana yin yadda zai gyarata ne da
anta dan ta sab itace mai manyan ya'ya duk tsiya ko menene tana da alfarma?

Ita da kanta ta sani babu ruwanta da abinda ya shafi matansa, a zuciyarta kuwa tana kiyaye haka ne dan gudun rigingimu da raini irin na kishi wanda zaka ga du girmanka an kawo maka yar yarinya karama an hadaka da ita ta zo tana neman nuna maka itama fa mace ce da mijinka take ganawa............., Ta sani ne ita bata da damuwa da maganar aure auren docter, ama kuma idan ya kawo mace babu ruwanta da ita ko
anta tana bangarenta da nata ya'yan tana rayuwarta ne sai idan halin a zaunan ya kama ake yin zaman
Anya idan yau Allah ya amshi Docter ita ta isa ta ja wannan gida nasa kuwa?

Tana tsoron du irin albarkar gidan nan a wayi gari a ga babu kowa sai wa'inda suka gaje shi, tana tsoron kowa ya watse zumunci ya zamto sai idan sun tsaya a gaban Allah su fada masa dalilinsu na kaste shi.......tabas ta yiwu komai ya tsaya kennan tunda wanda ya hada ya tafi?

A hankali ta ringa jin zuciyarta na yi mata rauni ta sake dagowa tana sake binsu da kallo daya bayan daya
A sanyaye ta budi baki tana kallonsu ta ce" Manyanku su tashi su bude dakin litatafai su dauko ku raba a tsakaninku ku yi karatu kasa kasa kun ji yan albarka?"
Sun dan yi jimmmmmmm, dan ba saba gannin irin haka suka yi ba, har sai da ta kama sunnaye daya bayan daya sannan suka mike suka nufi baban dakin dake dauke da kayan karatun suka dadauko sunna rabawa sunna komawa har kowa ya samu sannan suka zauna suka shiga budewa
A tausashe ta sake fadin" In sha Allah, daga yanzu, zamuna yin zaman nan a nan du bayan sallar isha'i mu yi karatu kun ji ?"
Yanzun kam har shi docter dake zaune kansa a sama idannuwansa a rintse sai da ya bude ya dago dubansa ya dora a saman fuskarta, tarin rauni da tsoron da ya karanta a kan fuskar nata ya bashi tausayi
A hankali ya dauke dubansa yana kallon matansa ya ga kowace sai kallon mamaki take yiwa Hajiar , so suke su gane me take nufi yau kuma?

Hajiarsu ce fa?

Hajia dai hajia, ai sai dai su fadawa wani wace hajiarsu ba dai ya fada masu ba, rumbun rigima kennan, hajiar rikici...........................................................
Chapter 40 · 0% Book details