← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 110

Sashe 3

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Murmushi ya yi ya dawo ya duka yana balewa ya ajiye a daf da hannun Mahaifinsa a tausashe ya ce" Abah, bata da tsada kuwa, gatanan ina so ka saka , Allah ya karra maka lafiya.....Docter zai zo gobe da sasafe in sha Allah, ka taimaka ya dubaka, kafafuwanka sun tasa....bana so na ga sun tasa ka ji?"
Irin yadda ya tsatsareshi da ido sai da ya ji kwallah na taruwa a tasa,
Murmushi ya yi ya dauki agogon ya mayar masa a hannunsa ya ce" Kai kuwa, abinku na yara me ya hadani da shi, ina dai jin tausayinka ne, kuma ina dan son yin nasiha, lokaci zuwa lokaci a ringa rage siyan tsada sosia, dan nauyin kar ya yi yawa a zo a shiga hurumin gwamnati da kuma harkar talakawa...., Abahna ka san ko me bawa zai yi, idan bai rike bakinsa daa hannunsa da cin haram ba da sauki, ka kiyaye cin zali ko yayane, ka ji tsoron Allah shi shi kadai, bayan wannan ko waye ka barshi ya gwada ikonsa cikin damar da Allah ya bashi ka ji?"
Murmushi ya yi a hankali ya gyada kansa, ya dauki agogon ya mayar a hannunsa,, dan ba zai yi musu da mahaifinsa ba, ba kuma zai ja ya ja ba, haka kuma ba zai tsaya yace masa kar ya masa nasiha ba , dan nasiharsa shine kwarin gwuiwarsa, mahaifinsa shine na biyu a cikin layin abinda ke saka shi kiyaye dokokin Allah, daga Alkur'ani sai shi, ba zai iya duban idannuwan mahaifinsa yace da shi wannan agogo ya siyeta ne dan halin haka ya bashi dama, ba zai kwatanta masa a yanzu yana samun kudin da bai san yaya zai kamanta su ba, kamar wanda ake bashi rabonsa ,......bashi da abin fadi sai hamdallah, kuma in sha Allah zai rage siyan tsadar, dan a gaskiya yana siyan tsada, da wannan ya fice, Mahaifinsa ya bi shi da kallon tausayi da kuma addu'a, cikin ikon Allah sai da ya ringa haihuwar ya'ya har bakwai da matansa biyu sunna komawa ga ubangijinsa , shine na farko da ya zauna, daga shi kuma har yanzu babu wanda ya rasu, bai wani dauki shekaru ba, dan bai fi talatin da biyar ba, ama a haka Allah ya saka masa albarka, bayan dogon karatu ya fito ya damki aiki mai daraja har ya zamo kafada mahutar dangi da jama'ar gari
A muntuce ya ringa bi daki daki, tun daga kan aunty Amarya, har zuwa dakin mahaifiyarsa wato uwar gidan Docter Hajia ZUWAIRIYA ,
Kowance idan ya shiga bangarenta ya gaisheta, yakan saurara ya saurari bukatunta, da kawo kararta da sauransu dai, abinda ba za'a rasa ba , ba zai bar wajen ba har sai ya biya mata dukkaan bukatunta da yake iyawa, wa'inda baya iyawa kuwa yakan yi addu'a ne ya tashi
A dakin Aunty amarya kawai ya shiga ya fito bata ce tana bukatar kudi ba, ko ta kawo karar yar uwarta ba, har ya gama dan zama ya mike ya bar bangarenta ta bishi da addu'a kanta a sade dan fushin mijin bai saketa ba, watau da ya fadi sunnan da bata so, bata kauna ba kuma zata tana so ba!

Irin zaman da ya yi a saman kujera yana dan cakalar dankalin turawan da Hajia ta zuba masa da kanta irin zama ne da akan yi idan an zo gaban mahaifiya, wato ba d'ar ba dari d'ari.

Abincin yake ci, bata yi masa magana har sai da ya gama ta yi kiran daya daga cikin yarenta ta umarceta kan ta kwashe , ta kwashe ta mayar kicin ta kimtsa wajen sannan ta dawo sumui sumui ta haye sama numfashinta a makogwaro har ta shige sannan ta ja numfashi tana shigewa dakinta hadi da adu'ar Allah ya sa kar Hajia ta sanar masa cewar yau bata yi wanke wanke ba, wancen bara gurbin ta saka ta yi mata ya ci kakanin babaninta!

Hajia ta sake zubawa fuskarsa ido, sai kuma ta tabe baki tana cire kanta kasa kasa ta ce" wannan ja na lebenka kamar dai ba na lafiya ba......"
Kasancewar yana kallon fuskarta ne, kuma yana jin dukkan abunda take fada, sai ya yi murmushi bai ce komai ba, bai san me yasa kalar lebensa yake saka mahaifiyarsa koda yaushe mita a kai ba, shi dai ko goro baya taunawa bale a kai ga sigari ko giya, hasalima kamaninsa da na mahaifinsa tamkar kaki ya yi ya tofar, itace baka sannan a kaf ya'yan mahaifinsa su uku ne suka yi farinsa, ama Hajia sai tace shi nashi jan ya yi yawa anya na lafiya ne?

"Baban gida, na san abanka ya maka maganar kayan lefen yaren nan ko?" Hajia ta fada tana dubansa
A nutse ya amsata yana sake dubanta
Hajia ta hade fuska sosai ta ce" To bari ka ji abinda zan fada maka, ban lamunce maka kwasar kudi ka je ka kwashi kaya na makudan kudade ka zubawa ya'yan da kwanan duniya iyayensu ke koya masu tsanarka da kiyayarka ba, ka sani ni na haifeka babu wanda zai fi ni sonka ko sannin zafinka a duniya, ka kula Baban gida, idan nace bana so kar ka saki ka yi!"
A hankali ya dago kansa dake sade, shin yaya zai yi da iyayensa ne?

Idan wannan ya ce ga abinda yake so a yi, sai wancen ya ce kar a saki a yi, ya kuma yi aiki da karfinsa da ikonsa a kansa
Bai san me yasa Hajia take yin wasu abubuwan ba wani lokacin, bayan shi ya sani mahaifiyarsa mutun ce mai matukar kyauta da son mutane
"Yaya zaka tsareni da ido kana min wani kallo kamsr sa' arka Baban gida?, So nake ka fada min abinda abanka yace kaf ina saurare" ta sake fada harda harde
afafuwanta, irin jira take ta ji abinda bai yi mata ba a yi wada za'a yi
Ajiyar zuciya ya sauke a tausashe ya ce" ABAH bai ce min komai ba, nine nake so mu yi maganar da ke, sai na ga abinda ya dace a yi, MAMAH kar ki manta nine baba a gidan nan, ko me za'a yi ya zama wajibi na shanye na kuma nuna masu halin girma, da haka ne zasu yi koyi da ni idan kowa ya malaki hankalin kansa ya rike zumunci duk rintsi, Mamah, dukkan abinda suke yi ko giya suka sha babu wanda zai tunkarenk, tun daga kan AMIR har zuwa kan ummi Auta..., Ko a haka aka tsaya da sauki a irin tab'arb'arewar zamani da zumunci..."
Zama ta gyara da kyau tana kallonsa ta katse maganarsa a harzuke ta ce" Ba zai yiwu ba fa, ba zai yiwu ba, su rike zumunci ko kar su rike wannan damuwarsu ne, ba zai yiwu a taru a kashe min
a ba, na tabata abanku ba wani tausayinka yake ji ba, bari ka ji, idan ya ce sai ka yiwa ya'ya mata kayan daki da komai ba laifi ka yi, bayansu idan ka yarda ka yiwa matansa ko maza kayan aure ban yafe ba!
Chapter 3 · 0% Book details