← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 110

Sashe 79

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lah ha ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam
Da daidaya yake kallon cirowar kajin da sakawa a wata ledar har aka gama saka su su hudu jiga jiga da jusss irin na kwalba babar kwalbar nan mai tsadar gaske kwaya biyu ta dauko ta kawo infa yake tsaye ta miko tana ta boye murmushinta
Ledar yake kallo tamkar an miko.masa bom, kasa kasa sosai ya ce" Luba, walahi ba nine na sayi abin nan ba, kin ga ce min ya yi fa ga maganin, ni banma san asalin wai abinda yake cikin ledar nan ba kennan Luba..............."
Haba jama'a, haba a kan me za'a ringa yiwa jikan SULAIMANA haka ne dan Allah?

Me ya yi ne ni jama'a za'a sako shi a gaba haka ne?

Iyi, kaza?

Wani kallo ake so duniya ta masa ya riko kaza ga yarinya a gefe?

Iyi mutun fa da girmansa da komai?
kashhhh sharin uban amarya da yawa yake
Ledar yake kallo tamkar an miko masa bom, kasa kasa sosai ya kalli Luba dake sakar masa wani murmushin da ya rasa a gefen da zai ajiye ya ce" Luba, kin ga walahi ba nu bane na sayi abin nan, kin ga fa ce min ya yi fa maganin, ni kuwa na amsa na yi gaba banma san menene asalin wai abinda yake cikin ledar nan kennan ba Luba......"
Lubabatu ta dan rage girman idannuwanta tana kallonsa, ta dan karkato kadan ta ce" Aya, to gashi ai yaya ko na kai maka?"
Kai ya girgiza , a dole so yake yi ta gane da gaske yake maganarsa ya ce" Aa, ba sai an bani baa to ni na yi me da shi kuma, ki barsu a nan ku ci kin ji?"
Lubabatu ta girgiza kai har tana dan tabe baki ta ce" Aa, ai hakinta ne ita Aunty ZAHRAN ko?"
Shi kam kamar Luba so take ta kure shi, yaya sun saba irin haka da ita magana a siri su daidaita damuwar daya yau zai ringa yi tana neman raina masa wayo?

Da tace aunty Zahra inda Zahran ke tsaye tana kallon mamanta fuska a shagwabe alamu na nuni daf take ta fashe da kuka sun bayana Maman nata kuwa ta dauke kai daga inda kowa yake ya kalla, ya ga abu ficik wai ama Luba tace aunty Zahra, lalle zasu zauna su yi magana shi da Lubabatu ne
Kin amsar ledar ya yi ya juya kawai ya fice
Lubabatu ta juyo wajen Mama tana murmushi ta ce" Mamah ya fa ki amsar sakon wai bai san meye a ciki ba aka bashi"
Mama cikin basarwa dan itama ta kula cikin Luba cike yake da neman fitina ta ce" To kin ga ba Zahra ta wuce ta bace min da gani a wajen nan tun kafin na harzuka"
Luba ta karasa inda Zahra take ta kamo hannunta ta saka mata ledar ta ce" Kin san Allah Fati, idan kika yarda kika harzukani a wajen nan tsaf zan saka kaina a uku ta hanyar dundugura maki mari, wai Maman taki ba gida daya kuke ba?

Dama ai ba daki daya kuke ba kuma ta jima rabonta da rakaki barci, dilla wuce ki tafi sai munafurcin sisine kai kike yi kamar baki san me ake nufi ba, to kim ga idan kika yarda kika aikata aikin gidadanci ko?

Tsaf za'a saka ki uku kina ji kina gani, kin ga dai ba zan rantse ba ama ina mai kyautata zaton da ran Hajiar cen dai gaskiya babu maganar aurenki ya mutu sai dai wani ikon Allah, kuma idan kika yi sake tsaf wata zata warce shi ki zamo mai masu tuwo sunna sama a kulle a daka, dan kin ga du azabar da zai gana maki babu wanda zai ce ya sake ki, ke fa kin shigo sai dai ki binne shi ko ya binne shi, gwara ki yiwa kanki karatun ta nutsu ki yi watsi da komai ki ba marada kunya , masu tunanin ba zaki zaunu da shi ba ya fi karfinki kuwa ki maka masu kunya mu zo sunna kin ji yar kanwata?"
ZAHRA ta saki hawayenta ya bale a saman kuncinta tana kallon Aunty Lubabatu, yanzu Fisabililahi wannan kalamai da Aunty Lubabatu ke fadi ina zata shiga ta boye su kar wani ya ji?

Haihuwa?

Ciki?

Ita?

Da yayansu?

Astagfrulah, astagfrulah jama'a astagfrulah.........

Turata take yi tana sake yi mata magana kasa kasa da zarro ido har ta bude kofar ta turota ta mayar ta rufe tana jan dan karamin tsaki a ranta tana jin takaicin ZAHRA, kai yo in ba takaici ba me zata hada wannan iya shegen?

Yaran zamani dai babu abinda basu sani ba shi yasa iyayenma suka daina wani ba kansu wahala dan wata yar idan ke uwa takamarki kin haifeta zaki koya mata wani abin sha kutuminki ki huta, dan wa bilahilazi idan ta saka ki a classs na eh yane watau yadda ake kula da shi ainahin miji ko? summa ne zaki ringa yi ana dawo da ke dan mamaki , kuma ba dan ta je ta lalata kanta ba, no, jarabar bincike da bin kwakwafi a wajen y'ayanmu na yanzu sai hamdallah da fatan Allah ya tsare mana kawai, ita ta san Zahra ba dai maganar wai duhun kai za'a yi mata ba, aa sai dai ace tana tsoron shi, kuma tsoronma so take yi ta yi anfani da shi tsoron ta riki wuyan baban Abah har ya ringa kukan awakai a daki
Mamah dake hararanta ta gala mata harara ta ce" Luba walahi idan har ya dakar min y'a sai ranki ya bace na fada maki, ke baki san Babah bane kina tunzurashi da ita ko?

To na ji, ni na taba gannin ki hanna ni fir a kai yarinya?

Ba damuwa ki kwana da sannin idan wani abin ya samu y'ata ranki ne zai bace!"
Lubabatu ta saki baki tana kallon MAMAH har ta haye sama
Ido ta dan zarro tana kaiwa zaune saman kujera ya dauki nadi daya cikin hudun da ta ware ta warware ta baje shi a saman kujera ta sasauto ta shiga yaga tana fadin" Allah gamu gareka ka sa kar ya dakar mata y'a ta rama a kaina"
Sai kuma ta yi murmushi kasa kasa ta ce" Wai duka, ya dai san wa zai yiwa muzurai ba dai ita ba, da yana yi da ya jima da dukanta .............."
Tana jan hanci take dan tafia tana waige waige, a cen kasan zuciyarta ta tsinci kanta da jin kadaici, da tashin hankali mai girman gaske, uwa uba a yanzu da take cikin tafiyar nan ta rasa ina zata dosa, shin kai kanta zata yin da gaske dakin mijin ko ta yi kwana ta yi tafiyarta ta koma wajen Mamanta ta yi kwonciyarta ne?

Ita bata san me yasa aunty Luba take haka ba, kiri kiri ta sa Mamanta yin aikin da ba shikenan ba, hum wai Aunty Luba harda cewa ta ringa saka kannanun kaya tana yiwa Yayansu rangwada?

Astagfrulah, astagfrulah wannan aikin ai ba aikin mutanen kirki bane sam
Maganar zuci take yi tana tafe a hankali har ta raba tafiyar kawai zuciyar ta komawarta ta fi rinjayarta, ta cuno baki sosai tana ta tunanin ai ba'a taba yi ba amarya ta tafi ita daya kwal a hausa, walahi komawa zata yi an bata rikon kaza ko me ake nufi yo?

Ta je da kaza ta shigo sak irin yadda ango yake yi ya zo da kaza , lalle
Tana yada harare ta juyo da nufin komawar, sai dai juyowar tata ta saka gabanta kwonci kwonci ya fadi sakamakon ganninsa a bayanta da dan nisa kadan hannayensa zube a cikin aljihun wandonsa ita yake kallo ne ko kuwa katari aka yi da ta juyo din suka yi ido hudu?

Ita dai bata taba jin juyawar ciki irin na tau ba dan zata iya rantsewa a inda yake tsaye tabas ya ji kukan cikinta, zama ta iya cewa kamar ya bi wajen da kallo sai kuma ya dauke dubansa
Wata irin ajiyar zuciya take saukewa sannan ta juya zugwui zugwui ta ci gaba da tafiyar a ranta tana ayana' Allah, Allah ka cire min jin tsoron bawanka a raina, Allah Allah yanzu ni din di zan je da kaina?

Ashe yana bayana ya min shiru?

Wayo Allahna 'tunda aka fara gyaran gidan nan bata taba takowa ba, hakan ya sa sunna barin ainahin balbalin gidan doctor sai ya ringa rage tafiyarta da dabara har ta so ta ji ya kusa wuceta, sai dai bata ji hakan ba sia jiyo muryarsa da ta yi yana fadin" Mu je mana "
A hankali ta dan juyo tana sada dubanta ta ce" Ban, ban san wajen ba Yayanmu"
Fuskarta ya dan sake kallo, gargadar muryarta ya saka shi dan kallon bakinta, sai kuma ya dauke kansa ya yi gaba ya zamto yanzu ita ke binsa a baya
Yana tafe yana tunanin watau sai da aka bata kazar nan ko?

Sai ta ci ai shi dai babu abinda zai yi da kaza bai san abinda Aban Ahmad ya saka a ciki ba, shi yanzu ya fara tsoron Freind wai ace Freind ne zai ci amanarsa haka?
Chapter 79 · 0% Book details