← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 110

Sashe 76

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A kausashe ya ce" Babu wace na kawowa shawarar zabin macen da zan zauna da ita, daga yau kuma sunnan matata FATIMA ZAHRA ba wancen mumunan sunnan ba, du wanda ya kuma zaginta ni ya zaga, kuma sai na rama!"
Tabas a budewar idon harda MAMAH tana kallonsa a lokacin da ya juya ya je ya bude kofa ya ce" Kunna iya tafia"
Su dukansu biyun Mamah suka juyo sunna kallo tamkar idannuwansa zasu fado kasa
Ita kuma ta dauke kanta tana mayar da fuskar Zahrah kafarta ta kwontar dan a zabure ta dago da dubanta tun jin furucinsa jikinta kuwa ya fi na da
aukan rawa
Gannin bata ce komai ba ya saka su daukan hanyar fitar kowace na sake yi masa kallon mamaki suka fice
Dawowa ya yi ya karasa inda Yayar marigayiya ke zaune
Hannayensa ya dora saman kujerar ya dan duko ta yadda ya mata rumfa, kasa kasa sosai ya ce" Kin ga, wannan din mahaifiyata ce, ke kin san bana hadata da kowa da komai, abinda kika yi sam ba ilimi bane ba kuma dabara bane, ko je zan neme ki"
Daga haka ya mike ya barta fa sha
ar kanshin turaransa ya koma daf da Mama ya zauna , shi fa har ga Allah baima ga yarinyar ba, a zamansa daf da Maman idannuwansa suka sauka a kan fari kal din hannunta mai dauke da kunshi ja cikin na Mama, hannun na rawa MAMAH kuwa tana ta shafa bayanta ta kuma rike mata hannunta
Fitar Yayar marigayiya ya saka MAMAH sauke wani irin ajiyar zuciya tana girgiza kai ta ce" Ban san rashin hankalin mutanen nan ya kai nan ba Baba, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, aurenka da ZAHRA kuwa sai dai du maki gani ya mutu dan bakin ciki, bi'izinillah ta shiga kennan sai kuma ta mulki dan uban kowa a gidan nan?"
Da dan mamaki ya dan kalli fuskar Mamahn, da idannuwansa kuma ya mata alamun ta daina fadar haka mana gaban yara?, A zuciyarsa kuwa ya ringa ayana' Toh fa, wa ya ga mulki kamar wata wace aka aurawa sarki?,'
"Mama" ya fada a hankali, amon muryarsa da ya sake yin kasa kasa da kwinciyyar hankalin ZAHRA, har ta sake rike hannun Maman da kyau
A hankali ya dora da fadin" ki yi hakuri kin ji?

Ki daina saka damuwa har haka a ranki"
Mamah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Dole ne na ji hankalina ya tashi Babangida, ka duba fa ka ga tijara"
Dan murmushi ya yi , ya saba idan magana yake yi mata yana rike da hannunta, yanzu gashi hannun nata cikin na wannan lafafiya a jikin sai yake ji du hakurin da yake bata bai isa ba, ya dan sake karkatar da kansa kadan ya ce"
Ya dan sake karkatar da kansa kadan ya ce" ki yi hakuri, ba za'a sake haka ba kin ji MAMAH?"
Mamah ta gyada kanta ta ce" Ai gwara da aka watse taron, kowama ya tafi kawai Allah ya saka da alkhairi, baban abin farin cikina an daura shikenan Allah ya zaunar da kowace a dakinta"
A saman lebensa ya iya amsawa da amen, sannan ya mike ya ce" Bara na je, akoy baki cen gidan Aban Docter, in sha Allah zamu dawo da wuri kafin dare dan a fara daukan amaren nasu, na nan din kuma a tabatar an shiryasu da wuri dan a mika su dakunnansu da wuri"
Mamah ta amsa tana ta shi masa albarka har ya tafi
A hankali ta sauke dubanta a kan ZAHRA, muryarta a tausashe sosai ta ce" Y'ar Mamanta "
ZAHRA ta yi shiru, shiru mai tafe da tsoron amsawar
Mamah ta yi murmushi ta ce" Ai dai ba haka zamu wunin ba ko?, Kya tashi ki koma wajen yan uwanki ku ci gaba da bikinku ko?"
A zabure ta dago tana zarro idannuwanta muryarta a raunane ta ce" Mamah su zane ni?"
Mamah ta zarro idon itama ta ce" Tap, ba sai ya tataka su ba, baki ji yace kar a kuma ba?"
Sai ta samu kanta da zubawa fuskar Mamahn ido, muryarta kasa kasa sosai kamar mai rada ta ce" Mamah, wai wai me ake cewa?

Wai da gaske ko kuma dai kawai dai dan a dagan hankali ne?"
"To menene na daga hankalin a nan?

Bayan ad
u'ata Allah ya amsa?, Kin kuwa san Abankuma burinsa kennan, kuma gashi Allah ya nuna mana"
A raunane ta dora kanta a gefen kafar MAMAH tana furta" Wayo Allahna na shiga uku, ni kuwa me ya kawoni cikin wannan rikicin?

Baba fa, MAMAH baba fa?

So ake yi ya kasheni ne?"
Mamah ta dagota tana kallonta ta ce" Wa kika ga ya taba kashewa?

Wani irin kisan kuma"
Zahra da hawaye ke bin kumatunta a raunanen ta dake fadin" Mamah, idan fa ya zane ni?

Dukana ne zai yi, cewa zai yi tsaurin ido ne wannan ai, Mamah ni kuma?

Ba ga aunty cen da akace itace yayanmu zai aura ba?"
MAMAH ta yatsina fuska, ta fara dauko yan fadan tana hararar ZAHRA, dan kuwa yar tata ta cika shagwaba da kaucewa wollah, gaba daya tsagwaron tsoronsa ne take karanta a fuskarta, bayan ta san waye danta, ko matarsa ta farko inda ta kasa kai labari kennan da take masifar tsoronsa sai ya zamto kamar wani aljaninta, ya yi nan da ita ne ya yi cen, abinda yace ko meye a kansa take, ko me take so kuwa in ya yi niya dan isa irin ta maza yace no , no din ne sai dai ta yi hakuri, kuma a haka ta rayu babu ruwanta da su, idan ka ganta a familly hause wani abu ake yi, ta zo da safe ta tafi da yama irin na wa'inda aka gayata, ta kawo gudunmuwarta ta fecewarta, ita dai shi shi kadai ne nata daga shi sai shi kuwa
Mama ta dubeta ido cikin ido ta ce" Kukan nan fa zaki daina, wannan zaburar zaki daina kin ji?

Dan ba zata taba kwatar maki yanci ki ba, ba nice zan ringa yi maki fada ko zan maki zaman gidan miji ba, dole ne zaki zubar da du wasu abubuwa dake rike ki ki fuskanci rayuwarki yadda ya dace, kin ga mijinki ba wanda yake iya fahimtar salo salo bane, aa, dole ki gane ki kuma gyara abinki yadda kike so, du abinda kika tsara na rayuwa da waninsa kanki tsaye a zuciyarki shi zaki gabatar da shima dan mutun sunnansa ba aljani ba, maganar kar ya kasheki kuma shirmen banza kennan, ko ya zane kannensa ya daki wani ke ai kin fi karfin hakam, ki gane haka, tashi maza ki je sama toh tunda ba zaki koma din ba"
Da kyar ta iya daukan kafafuwanta ta sada kanta da dakinta
Tunda ta shiga nan ta silale ta zubawa waje daya ido, kwakwaluwarta ta ki bata hadin kai dan yin tunani wa abinda yake faruwa da rayuwarta
Bata fi minti goma da shiga ba tana nan zaune aka bude aka shishigo
Ya'yan MAMAH ne masu auren da su aunty Rukaya
Da mamaki Aunty Husnah ke kallon ZAHRA dake zaune a kasa, lafayarta ta yaye sai bak'ar rigar dake jikinta doguwa lafafiya kawai, ta yi wani irin zuru zuru da ita tana kallonsu itama su dukansu kamar yadda suke kallonta
Rukaya kam abin dariyama ya so bata, dan ta san wacece ZAHRA sarkin tsoro da firgicewa, ta san da za'a iya shiga zuciya a ji tarin firgicin da take ciki sai an sha mamaki
Da mamaki Aunty Husnah ta ce" Ke kuwa ya da zama kafa a watse kamar an aiko maki da sakon tashin hankali haka ko dai a dukan da yarinyar cen ta maki ta raunataki ne?

Tashi na gani tashi?"
Da takaici Lubabatu ta zauna a saman kujera tana dafe kanta, ta sha mahaukacin leshh da abun hannu da na wuya masu masifar kyau ta ce" Yau na ga tsabagen tsagwaron rashin kunya, dan bama nan ne har tsagerun anguwa ke shigowa gidan nan kunna kallonsu rukaya baku tayaka banzaye ba?, Yanzu ace wannan yarinyar da bata da kunya bata san kunya ba, bata san darajar kanta bane wai take ihun yayanku take so?

Dan yayan namu ya zama kuka sha dadin hawa?, Lalle yau na kunshi takaicin da na jima ban kunsa ba kuma kafin na bar garin nan sai na zane yarinyar cen da dorina dukan da babanta ba zai mata shi ba, walahi sai na tatakata jahilar banza da wofi, ita yanzu a yanzu haka tana kan ganiyar wulakantar da kan nata me take nufi da mu?

Lalle an fara kawo raini a gidan nan dan an ga shi bai fiya magana ba, bama ya son tsunguri tsoma ko?
Chapter 76 · 0% Book details