← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 110

Sashe 107

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dace ta yi hakuri ta fuskanci rayuwa zuwa yanzu, ya dace ta dubi mahaifinta ta yafe masa"
Mama ta sauke ajiyar zuciya da kula ta ce"
Saura kiris in sha Allah
Mama ta sauke ajiyar zuciya da kula ta ce" In sha Allah daga nanma zan je wajenta dan dazu ta fita, yaya jikin Zahrah ne?"
Dan murmushi ya yi yana dan sada kansa ya ce" Alhamdulilah Mama, dan zazabi ne lokaci zuwa lokaci, shima ba koda yaushe ba, kuma baya yin tsanani yake sauka, likitan yace min ba komai daga ta cike wata uku yana iya barinta shima yanzun kuwa ai ta kusa cike watan uku "
Mama ta yi murmushin itama tana mikewa ta ce" Allah ya karra lafiya, ai yata dama akoy hakurin ciwo"
Daga wajen Babangida Mama bangaren Aunty amarya ta je
Da ta je ta sameta zaune tana kallon series irin na india na soyaya, hakan ya saka Mama yin murmurshi ta zauna bayan sannun da Auntyn ke mata ta mike dan kawo mata ruwa
A lokacin da ta shige ne wayarta kirar iphone ke kuka a saman kujera hakan ya saka Mama daukan wayar tana fadin ana kiranta, nan ta ga sunnan mai kiran hakan ya sake sakata sakin murmushi harda karra samun kwarin gwuiwar yi mata maganar, dan tana kyautata zaton zata amshi maganar, domin Aban Zahrah a da sunnansa a wayar macuci, yanzun kuwa sunnansa Abu ZAHRAh, ko menene kam su tafia ta masu sauki kuma an ga amfaninta sosai
Dawowa ta yi da ruwa da kuma jus din kankana irin wanda Mama ke so sosai tana murmushi ta zubawa Maman sannan ta zauna ta ce" Mama, dazu mun yi waya da Luba, kai Allah ya shirya min Luba , ama ina so na shirya na kai mata ziyara Mama ta dage sai na je"
Mama ta yi yar dariya ta ce" Ku dai kuka gano, ama tafia kam ni dai ba ruwana kin dai ga yadda yaron cen ke hannawa, banma san yaya aka yi ya rainawa mutane wayo ba, wai fa shekaran jiya zan je anguwa cewa ya yi jiyama na fita na bari sai satin gaba, ban gane biyaya na masa ba sai da na haye dakina na yi kiransa na zazageshi tassss , ya min shiru kamar baya wajen"
Aunty ta saka daria , watau diramar ta Mama da Babangida ai sai su, idan ya yi wani abin sai daga baya ta tuna ta ringa jaje kennan wai yanzu ita baba ya cewa kaza?

Ko ya hanna
anta kaza?

Bama irin y'arta kafin a hada auren nan tsaf zata wanke mutun a kan Y'arta......, Sai kuma jikinta ya fara yin sanyi a hankali dariar ta ragu sakamakon babban mikin dake mata zafi a zuciyarta, Abanta yace zai zo su sameta da kansa, ama du gani take yi da wahala ta dubeta, ta yi dabarar ta yi rarashin ama irin yadda take amsata kamas din nan na daga mata hankali, idan kuwa tace da ita Aunty sai ta ji babu dadi a ranta har ta ringa jin inama tace da ita Mama itama?

Ta yiwu itace kadai rabon da Allah ya tsaga mata zata samu a gidan duniya
Mama ta bada hankalinta kanta sosai da kula ta ce" Nana wajenki na zo, a karro na biyu dan na taso maki da maganar da kika jima da min inkiyar kar na kuma yi maki,ba dan komai ba sai dan mahinmancin maganar, na san cewa zuwa yanzu kina iya gane cewa ko me ya faru da rayuwarki tun daga barinku gidan mahaifinki da mahaifiyarki har zuwa yanzu kadara ce ta ubangiji, domin a cikin laifukan da ake iya yiwa juna a zamantakewar yau da gobe ina iya sheda maki ana yin sama da haka, ke na takaice maki ta yiwu rabon Zahrana ne ya tisa keyar mahaifiyarki waje da kuma kasarta dake kauyen nan, zuwa yanzu na san kin gane ba laifinsa bane dan mahaifiyarki ta rasu ba kuma laifinki bane, zuwa yanzu na san koda bakya kallon wa'azinsa , bakya sauraron redio, a gari zaki tsintsinci wanene mahaifinki koda tunanin yarinta ya boye maki waye shi ko kuma nace a lokacin bai taka matakin da yake kai a yanzu ba....., Nana mahaifinki malami ne, almajiri ne, mai hidimtawa al'ummar annabi ne, mahaifinki da kansa yake maganarki a dukkan inda ya san ana iya taimaka masa da addu'a, burinsa kar ya koma ga ubangijinsa ba tare da ya ganki ba ke da mahaifiyarki, hasalima bai san ta bar duniya ba, y'ar uwarki da aka haifa masa baya cikin tsarin duniyarta, ke din kece kike tsaye a duniyarsa kuma kin kasa yafe masa....., Ki yi hakuri, inada naci a duk inda na fahimci inada daraja, Nana mahaifinki duniyarki ne kuma ke yake jira, kin ga a taron nan na addu'ar gobe ta malan idan Allah ya nuna mana, mahaifinki ne zai bayar da addu'a, Nana ki yi kokari ki ribanci lokacinki, idanma akoy ciwo da kuma taurin kai a tare da ke, ki watsar da komai ki ribanci jarabawar rayuwarki, ki yafewa kowa dan idan kin yafe din sakamakon yafewar a kanki take mai kuma dadi ce, idan baki yafe ba kuwa zaki ci gaba da rikon nauyi a zuciyarki ne , ni dai na sake fada maki sai ki yi tunani ki gani kin ji?"
Daga haka Mama ta sake shan jus dinta sosai harma ta dauki Jug din dan tafia da shi domin tana son tataciyar kankana ba siga ba komai sai madara kawai ta ruwa, tana jin dadinta a jikinta sosai , idan ta shata ko abinci bata nema
A hankali Nana ta sauko daga saman kujerar a lokacin da Mama ke kokarin tashi ta duka sosai kaffafuwanta a kasa tana kallon kasa sannan ta hade hannayenta tana ta murza
Muryarta a raunane ainun ta ce" Mama........"
Ta dago idannuwanta sai kuma ta fashe da kuka a hankali ta dora kanta saman kaffafuwan Maman
A hankali ta ce" Mama, in sha Allah zan saurareshi, idanma da hali zan yi masa magana a goben mama, in dai zai saurareni zan je na duka na fuskanci mahaifina.....domin a halin da nake ciki a yanzu Mama zuciyata sake kakaryewa take yi, du wani kuzari nawa barina yake yi, Mama hankalina a kulun tashi yake yi, ki duba ki ga muka je muka dawo muka koma muka dawo Zahrah bata tako inda nake ba, Mama ita ba zata yafe min bane?

Yanzun ko kiranta na yi da safe irin yadda na saba Mama ba kulun take dagawa ba, ranar da na ji alamun tana cewa yayansu awara take so na yi kiransa sai nace bara na yi na kawo mata Mama a lokacin nan take tace bata so, Mama zuwa yanzu karfi da yaji na fahimci uzurin da sauran al'uma suka yi min ita ta ki ta yi min ne, ta ki gane ba yin kaina bane Mama, a jiya da dare da mahaifinta ya yi kirana na kasa hakuri na fashe masa da kuka ina fadin yanzun yama fini alfarma a wajen yarinyata, Shi har ya rikice ya fara bani hakuri wai ya zata kiran nawa da ya yi ne na yi fushi har yana cewa dan Allah na yi hakuri koda sau daya ne a sati ya ringa kirana, sai na gane ashe kin zuwansama inda nake din kamar yana tsoron hakan ya bata min rai ne.........Mama sai kace wata kura ?

Su ringa guduna????"
Ta karashe tana girgiza kanta tare da fashewa da wani kukan, domin Allah yana gani wannan din itace babar damuwar da ta hanna mata sukuni a cikin zuciyarta, tana matukar wahaltuwa da wannan jarabawa, bata san yaya zata musalta ba, ta sani ta aikata aikin da ta bada gudunmawa dan gannin haka, ama kuma ta tuba afuwa take nema, yarinyarta take so ta shiga cikin jikinta itama ta ji duminta, itama ta zanta da ita ta ji dadi irin na kowa
Mama dake hawayen farin ciki a sanyaye ta ce" Nana ki daina kukan hakanan, Zahranki babu wanda ya kaita sonki haka mahaifinta, kin ga wannan baya baya da take yi ta riga ta ginu a shi ne, Nana tun tana karamarta kike nuna mata hakan shine zaman lafiyarta a tare da ke har ta yarda ta dauka ta kuma amince ta hakura da ke.........., Zuwa yanzu da Allah ya sa muka ga wannan rana hakuri zaki yi ki jure, duda aikin ba zai kai tsayin na korarta daga jikinki ba ama fa dole zai yi tsayi shima domin ko yayane sai kin jajirce kin kuma nuna mata cewa bata da wajen da ya fiki ta hanyar shiga jikinta da karfi da yaji da juriya da hakuri da kuma babar watau addu'a sai ki ga an wayi gari Zahranki ta dawo maki irin na da.........., Ki sani ba Zahrah ba ni da kaina fin karfina kika yi har na dangana na dawo nake dubanki sanadiyar irin abinda kike yi mata a da idannuwana na gani, kina kallo fa kece kofar da ta fara budawa har wani ke zagar maki ita, kece kika karra bada kofa aka wulakanta yarinya danma Allah ya yi ita din mutun ce mai hakuri?, Ama duda haka ni na san jarabawa kadan zaki yi ta sake shigewa jikinta zata sadakas, domin baki taba fita a ranta ba, a hankali ne tsoronki ya yi tasiri a zuciyarta da tsoron furuci irin na tsinuwa daga bakinki ya sa ta yi nesa da ke"
Sosai aunty amarya ta sake yarda cewa babu hanyar da zata bi da ta wuce sake yin hakuri da ba kanta dama ita da kanta ta san soyayar nan ta Uba, ta abokin rayuwa, da kuma ta y'arta ta cikinta, takan ji wani ciwo a zuciyarta in tana wasu tunanikan, takan yi tunanin to ina sanninta a addini ya shige ne take rayuwa kamar daba?
Chapter 107 · 0% Book details