← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 110

Sashe 99

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gama Sallah muby ya riga kowa fitowa daga masallaci haka kawai baya son haÉ—uwa da mahaj É—in musamman yanzu da ya ganshi tare da Abbu.
Ai ko MAHAJ da yake lura dashi bai ce masa ƙala ba har ya fice yana gama addu'ar sa kuwa shima ya fito.
A nan Babban falon dukkanin su suka hadu har Aiyah da take dan jifar shi da harara.Dinner zasu yi wadda dama haka suke yi Shine kawai yake tsame kan sa saboda wasu dalilai bayan takurar idanun Aiyah a kansa da na wasun ta dan mutun ne da ya tsani kallo yana cikin dalilin da ya sa baya shiga mutane sosai bayan rayuwar kaÉ—ai ci da ya ratsa jikin sa.
Ɗunguma suka yi zuwa kan Dinning hannun sa riƙe da na Abbu shi da kan sa ya ja masa kujera ya zauna yana furta " Yau ɗure zanyi wa wani babu ruwa na "
Shi kuwa sai ƙara ɓata kyakkyawar fuskar sa yake yi dan ji yake cikin sa cike yake saboda ya sha chocolate a ɗazu bayan ya farka daga bacci kafin aka kira sallah ya fice bayan yayi brush da watsa ruwa,bayan tashin sa daga baccin wuraren ƙarfe shida da yan mintuna.
Abbu kuwa ko a jikin sa kuma bai damu da idanun Aiyah da yake ji kan sa ba.
Dan shi ganin Mahaj yake yi yana rama bai sani ba ko idanun sa ne kuma ya san cewa rashin saka abinci ne isasshe a cikin sa.
Kasancewar ya san yanayin tsarin cin abincin sa ya zuba masa kunnun gyaÉ—a mai kyau da basa rabo dashi a koda yaushe kan dinning saboda Abbu da yake mugun son sa duk da shima Mahaj É—in yana son sa amma saboda bai damu da cikin sa ba anfi yiwa abbu dan haka koda yaushe ake masa shi a duk girkin da masu aiki zasu yi sai sun yi shi.
Ajiye masa cup É—in yayi gaban sa yana furta " Shaaa yanzu kuma bana son ganin komai sai cup idan ba haka ba zan saka Samira da Salma su matse mini kai na yi maka É—uri ".
HaÉ—e rai yayi jin sunayen da Abbu ya ambata yana tura bakin sa gaba kamar yaron da ke shan nono.
Yar ƙaramar Dariya Samrah ta yi wadda ta warke har ta koma ayyukan gaban ta dan har school ta koma.
Yar hararan ta yayi kafin ya ɗauki cup ɗin ya na zuba masa idanu,daddaɗan ƙamshin sa ne ya daki hancin sa hakan ya sa ya ja ɗan numfashi yana kai cup ɗin bakin sa bayan yayi bismillah.cike da kulawa Amma ta ce " Yau dai wani zai ci dole ".
ÆŠan kallon ta yayi bai ce komai ba bai kuma nuna alamar ya san da shi take ba.
Inda sabo Ammah ta saba da hakan dan haka cike da rashin damuwa ta kalli fuskar Abbu dake ta sakin murmushi yana kallon MAHAJ dake shan kunun sa a hankali.
" Kuna damuwa da wanda ko ciwon kan sa bai sani ba,idan yunwa zata masa illa me ye naku a ciki da har ake maganar yiwa garjejen ƙato ɗura ". ta kai ƙarshen maganar tana jan ƙaramar tsuka.
Furucin Aiyah ne ya sa shi ɗan dakatar da shan kunun sa kafin ya ɗan saci kallon ta dan haka kawai kwana biyun nan yake shafa ma kan sa lafiya ya daina leƙa wajen ta kwana biyu kuma cike take dashi a kan hakan jira take ta samu dama ta masa tass shi da uban sa dan a cewar ta shi ya ɗaure masa.Abbu ɗan ɓata fuskar sa shi yayi sai dai bai ce komai ba.
Dan baya da amsar bata sai dai ya san shi ke da komai a ciki kuwa domin shine wanda zai fi kowa fita hayyacin sa idan ciwon yunwa ya kama masa É—aan sa abin son sa farin cikin sa.
Shiru wajen yayi kasancewar kowa ya fara cin abincin sa da aka yi serving É—in sa.
Su Samira da Salma kuwa dukkanin su wani irin kallo ne suke jifan MAHAJ da shi wanda Ni dai Ban gane ma kan sa ba kuma yana É—ai daga cikin dalilin da ya sa baya son zaman kan dinning É—in tare da su.
Yana jin idanun su jikin shi sai dai bai nuna yama lura da su wajen ba koda Abbu ya saka su cikin zancen sa kuwa bare yanzu.
A haka aka gama dinnern inda shi ya riga kowa ta shi duk yadda Abbu ya so ya ƙara saka wani Abbu ya ƙi dan kuka yake neman ma sa a cewar sa ya ƙoshi da ƙyar ma yake numfashi.
Ganin hakan ya sa Abbu bai matsa masa ba ya masa sai da safe yayi hayewar sa.
Koda ya shige É—akin direct jallabiyar ya cire dan dama bai fita da wayan sa ba towel ya É—aura ya shige wanka bai jima ba ya fito bayan ya É—auro Alwallan kwanciya bacci.
Wasu riga da wando ne ya saka na bacci silky masu kyau guntun wando maroon color kafin ya ƙara gudun Ac ya hayewar sa kan bed ɗin sa bayan kashe hasken ɗakin da barin bedside lamp na gefe ɗaya.
Bacci dai ya ƙi zuwa duk yadda ya shirya yin sa yanzu kasa ɗaukar sa yayi domin kuwa sai juye juye yake yi wanda shi kan sa bai san dalilin ba ƙaramin tsaki ya ja yana jan ƙaton duvet na sa mai taushi blue color mai kyau ya rufa jikin sa tun daga kan fuskar sa har ƙafafu yana turje turje shi kaɗai tare da jan tsaki.
zaune ya miƙe yana hargitsa gashin kan sa dake ta walƙiya A hankali ya furta " Ya rabb.."
Idanun sa ya lumshe a hankali wata sabuwar Addu'ar ya ƙara yi kafin ya kashe light ɗin gaba ɗaya.
Ya kwanta babu abin da ke tashi a dakin sai ƙarar aikin na'urori da sanyayyen ƙamshin sa dake maƙale da ɗakin yana a hakan bacci ya kwashe sa rungume da filon sa wanda inda sabo ya saba hakan tun bayan da ya zamana yana kwana shi kaɗai ya saba wa kan sa da hakan ko da ya manta ne sai ya farka ya rungume filon sa yana jin hakan a matsayin cewa kamar mahaifiyar sa ce ya rungume duk da bai waye ta ba.
A suba ta gari ɗan Abbu.✍️

Mun kuwa komawa in da muka fito.
Masu niyyar fara payment su fara ba zamu jira kowa ba wayen da suka biya sun yi hakuri matuƙa dan haka babu jira in sha ALLAH.

Kuna da wani page an jima In Sha ALLAH.
Na yau kenan wannan bashin jiya ne.🤭🙏🙏

Kuna ƙwarin gwiwata readers Allah ya sakawa kowa da Alkhairi.
Masu bibiyar wannan labari na cikin group da na waje,mutanen facebook,mutanen Wattpad,mutanen Arewapens ina yiwa kowa fatan Alkhairi.💔🙏✍️💫

To subscribe yours contact this number
08069059746

_*KURMAN ƘADDARA*_

*_©®Faiza Almustapha Murai_*

_*FA'EEH BG*✍️_

P________4️⃣ 5️⃣

*BOOK ONE*
*_FREE_*

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_

*Wannan shafin naki ne kacokam Uwata*
*_(Maman Abba)_*💕💕🥺kiyi yadda kike so dashi.Shatou na godiya.🙏🙏

***

A ɓangaren Abbu ma sai da safe kawai yayi wa Aiyah ya shige da matar sa.
Yau ko yar firan da suke taɓawa as a family ba,ayi ta ba saboda yadda Aiyah ta ɓata mood ɗin Abbu.

A ɓangaren shatou kuwa suna gama cin abinci kowa ya watsa ruwa kafin suka fice zuwa makarantan islamiyya.Abin mamaki yau bata tsokani kowa ba har aka tashi dan sai da Inna ni ta mata kashe di ashe kuwa ya shiga kunnen ta.
A haka aka rabu lafiya da su malam Abu.
Bayan sun dawo makaranta kuwa sun samu Baffa na baya gida yana kasuwa dan haka suka shirya suka same shi Chan kasancewar an kusa Magriba hakan ya sa ya sako su Gaba suka yo gida yana jin daÉ—in firar su da ya yan na sa musamman shatou.Wadda ke bashi labarin yadda taga malam Abu na zare ido wanda ke jiran tayi masa laifi yau ya dake ta.
Alwallah kawai Baffa na yayi ya wuce masallaci shi da Bibu bayan isar su gidan.
Ita kuwa shatou tare da Inna ni suka yi sallama kafin suka cigaba da aikin da suka tarar Inna ni nayi na fige ganyen zogala da Baffa na ya tsinko musu daga daji.
Shigowar su Baffa na ce ta dakatar da su inda dama Kowa Inna ni ta ajiye Musu abincin su a tare suka ci suka ƙoshi sai dai ita kamar koda yaushe bata ci nata nan ba a ɗaki ta ci abin ta kafin ta fito suka cigaba da taɓa yar fira.
A hakan Kiran Sallahn Isha'i ya same su kowa ya yi wajen Sallah.
Suna dawowa kuwa karatu Baffa na ya ƙara bita musu sai da ya tabbatar kowa ya iya sannan ya bar su.
A ɓangaren shatou hankalin ta ya rabu gid a biyu domin kuwa tana son fita dandali tana tsoron abun da kan iya biyo wa baya kan rigimar ta da shamsu maƙiyinta.
Wata zuciyar ta ce mata kije da Bibu shiru tayi kafin wata zuciyar ta bata amsa da zai iya masa illa idan ke bai same ki ba.
To ai kina da mai kare ki baga iro nan ba.
Wata zuciyar ta ƙara furta mata.
Kafin ta yi shiru jin ɗayar zuciyar na ce mata ki rufa ma kan ki asiri yanzu idan baku haɗu da iron ba ke dai zauna gida bari ƙura ta lafa.

" Ke lafiya ,me kike tunani haka " ?

Inna ni ce da ta zuba mata ido tun É—azu ganin ta lula wata duniya abun har mamaki yake bata wai kamar shatou da tunani.Me take tunani wata zuciyar ta tambaye ta dan haka ta furta mata tambaya kai tsaye.
Bayan zuba mata idanun na ta.

"Babu komai Inna ni "
Chapter 99 · 0% Book details