← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 110

Sashe 97

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Shiru haka take zaune ta kafe waje ɗaya da kallo ga idanun ta cike da ƙwalla ta sha igiyoyi a jikin ta na ɗauri saboda kwanakkin nan da suka shuɗe tun bayan dawowarsu Canada abun ya ƙara hauhawa sai ta ƙara ƙaimin ji wa kan ta ciwo akwai lokacin da ta yanke gefen cikin ta glass wanda har yanzu ba,a san inda ta same shi ba, wanda da ƙyar aka ceto ranta kasancewar ba sosai ta samu yan kan ba amma duk da haka ta zubar da jini sosai.
Komai na jikin ta ya sauya saboda yanayin jikin na ta.
Wani irin kuka ta fashe dashi tana rufe idanun ta,tana sake buÉ—e su.
Tana ƙokarin nuna inda ta kafe da idanun ta sai dai hannuwan nata a ɗaure suke baiwar Allah daga ɗauren ta fara buga kan ta da bango haka kake jin sautin ƙuu ƙuu tana gwara kan ta a bangon fillern da aka ɗaure ta akai,dai dai lokacin ne kuma ya zo kawo mata abinci domin kuwa yanzu shine kawai yake iya shigowa batare da tayi har gowa ba,domin tsoron kowa take yi dan ko su Amoh da Dady sai ta samu bacci da su Nurse mirra suke zuwa duba ta da tsaftace mata jikin ta,cikin wani irin sauri ya buɗe ɗakin da key da ya zo da shi kafin ya shige da sauri cike da tausayin ta da tsoro gudun kar ta yiwa kan ta illa duk ya san ba lallai ta iya ko dogon motsi bane saboda yadda Uncle Yaqub ya ɗaure ta dan shi kasawa yayi haka ma Dady dan Tausayin ta suke ji sosai kowannen su ji yake kamar ya da wo da lalurar ta jikin sa,Amoh kuwa tun da jikin Isha ya ƙara rikichaɓewa itama jikin ta ya tashi,yanzu haka tana fama da Bp.
Wasu irin hawaye ne yake jin suna neman sauko masa sai dai kasancewar sa namiji mai ƙarfin hali da zuciya hakan ya sa ya shanye ya matsa kusa da ita yana ajiye wayar sa akan gadon dake ɗan nesa da ita kasancewar an chan za mata ɗaki yanzu tana kusa da Suhaila ga ƙofar ta gata ta.
" MA'ISHA " !
Ya ambata yana haɗiye wani irin abu mai ɗaci a cikin zuciyar sa kafin ya fara ƙoƙarin kunce ta dan bayan ɗago fuskar ta da tayi kacha kacah da hawaye tayi jawur ya ji ya kasa jurewa ganin ta hakan,sai dai yana fara kunce ta, ta fara kai masa bugu da ƙarfi tana cigaba da kuka mai tsuma zuciya.Idanun sa ne suka yi jazir kuma ya kasa hana ta dukan na sa ganin yake yi kamar shin e abun da zai rage mata raɗadi. Uncle Yaqub da ya shigo gidan yanzu ne ya zo direct nan dan ya gan ta kasancewar suhaila tace masa Suhail na nan aiko cikin sauri ya matsa ya riƙe ta yana katsawa Suhail tsawa mai girma ganin abun dake faruwa domin ya san tsaf zata iya ji masa domin ba acikin hankalin ta take ba,maimakon ya hana ta bugun sa shine ya saki jiki tana ta jibgar sa gata da ƙarfi kamar na maza goma.
Da ƙyar Uncle Yaqub ya ɗaure ta yana furta " Are you in your right sense Suhail , What's this " .?
Ɗagowa Suhail yayi ya kalle sa da idanun sa da suka ƙara rikiɗewa na damuwa da tausayi dan shi kwata kwata bai ji zafin dukan da ta masa ba.
Rufe idanun sa yayi da yake jin sun masa wani irin nauyi.
Babu abun da ke ƙara hargitsa tunanin sa irin jin kukan ƙanwar ta sa dake ratsa dodon kunnen sa.
" Gaskiya baka cikin hankalin ka Suhail so kake kai da ita ku zama ɗaya ne,me ye wannan,ita fa ba,a cikin hankalin ta take ba,Amma kai fa ".?karamin tsaki yaja kafin ya ƙara furta " Gaskiya kaima kana buƙatar Ganin likita Suhail because what you did,person that's has normal sense can not do it Wallahi,yanzu kai ne kadai take sakewa da kai idan ka bari wani abu ya same ka ita kan ta da take a wannan yanayi ba zata taɓa yafe maka ba Suhail haba ".
Kara É—ago jajayen idanun sa yayi ya zubawa Uncle Yaqub.
" Yes kalle ni da kyau na ce ba zata taɓa yafe maka ba,Suhail dan Allah ka kula da lafiyar ka taka ita zata taimaka mana mu samu ta Ishaaa,domin ka san abinci ma kai ne ka wai ke iya saka ta cin sa ,to idan ka samu rashin lafiya duk wazai yi wannan zata zauna cikin damuwa da rauni na jiki da na zuciya."
Miƙewa Suhail yayi yana cigaba da jin faɗan da Uncle Yaqub ke masa na kwance ta.
Allura ya haɗa wanda tunda ta hango yana haɗa ruwan ta fara sakin wani Marayan kuka mai tsumaa zuciya tana girgiza kan ta,alamar bata so.Duk yadda yake jin Tausayin ta haka ya cije ya zube mata ruwan nan tare da taimakon Uncle Yaqub ko minti ɗaya bata yi ba kuwa bacci ya kwashe ta wuyan ta yayi gefe. Tare wa yayi ya jinginar da ita ga ban gon yana ƙ ara zuba mata idanu.Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya miƙe ya fita tare da abincin da yazo mata dashi dan ya san yau ba za ta iya saka komai ba a cikin ta saboda baccin da zata yi ta yi har wayewar gari,ko kuma tsakar dare.✍️✍️

Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800
Book one zai kare a page 50 Dan haka wadda ta shirya sai ta saka kuɗin ta dan babu wanda zamu jira zamu cigaba da wannan tafiya in sha ALLAH.🙏🙏🙏

# _FA'EEH BG CE✍️_

*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔

_*KURMAN ƘADDARA*_

*_©®Faiza Almustapha Murai_*

_*FA'EEH BG*✍️_

P________4️⃣ 4️⃣

*BOOK ONE*
*_FREE_*

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_

💕💕💕💕💕

Amoh ce zaune idanun ta sun sauya na Zallar Damuwar da take ciki.
"Amoh ki yi Haƙuri kin ga ko ɗazu sai da Yaya Suhail ya ce ki rage ya wan damuwa Bpn ki yana hawa yana sauka ".
Ɗan kallon Suhaila Amoh tayi dake maganar kafin ta sauke numfashi ta ce " Suhaila yaushe Ya ta zata samu lafiya,yaushe Auta zata zamo kamar kowa,a koda yaushe ina yin mararin wannan mafarkin sai dai kamar abu ne mai matuƙar wahala,Ya Allah ka yaye wa baiwar ka, ka sa iya kar wahalar kenan,Allah ka bata lafiya ''.

Amin Suhaila ta amsa jikin ta sanyaye.
" Amoh zata samu lafiya in sha ALLAH,jarabawa ce,Ke kike faÉ—a mana Allah yana jarabtar bayin sa ta hanyoyi da ban daban lallai mu tamu jarabawar kenan,Allah ya bawa Ishaa Lafiya,ka nuna mana ranar da zamu zauna muyi fira da ita ".
Kai Amoh ta girgiza cikin karyewar zuciya ta ce " Amin ".

" Allah ya sa "

Shigowar Suhail ce ta sanya Amoh zuba masa idanu.
Kawar da kan sa yayi daga kallon ta shima yana zama kusa da ita,jikin sa sanyaye.
" Ta samu bacci ai "
Ajiyar zuciya Amoh ta sauke tana cewa " Allah ya bata ikon farkawa cikin aminci "
Amin dukkanin su suka amsa.
Uncle Yaqub ne da ya gama masa faÉ—a bayan fitowar su saboda shima yana da mugun jinini kuma ganin sa a bunda Suhail yayi wauta ce kawai da rashin hankali dan haka gudun kar ya maimaita yake ta nanata masa illar abun da yayi.
Zama yayi kusa da kujerar da ke kallon ta su Amoh.
Yace " Amoh ya ƙarfin jikin ki,ki yiwa Yaron nan magana ya riƙa kulawa da lafiyar sa ".

ÆŠan Hararan sa Suhail yayi da ya É—aura kan sa jikin Amoh.
Yana sauke ajiyar zuciya jin Uncle Yaqub bai tona sa kai tsaye ba.
Yar ƙaramar dariya uncle Yaqub yayi.
Amoh kuwa ce wa tayi " ka riƙa kulawa sosai Baba na ka ji ".Tana shafa sumar kan sa.
Kai Suhail ya jinjina mata yana ƙara shigewa jikin amoh.
Ko da Dady ya dawo haka ya isko su kowa dai zugum sai a hankali tun daga nan ya fahimci akwai matsala dan haka bai tambayi kowa ba ya dai yiwa yar sa addu'a cike da tausayin ta bayan ya leƙa ta window ya gan ta cikin yanayi na tausayi dan har da ƙwalla ya fitar mata.

💫💫💫
Chapter 97 · 0% Book details