← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 110

Sashe 34

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Inna ni ta juyar gefe kamar bata ga yadda take zaro ido ba yanzu dan ta fahimci halin da take ciki dan haka tace " Wuce ki samu waje ki zauna " Sai dai bata kai ga rufe baki ba Shatou ta faɗa Makewayi a Guje bayan ta runtumi buta.Sai da ta ɗan jima sannan ta fito tana ɓata fuska dan sabon tsumma ta chan za tana jefar da wanchan dan nan Inna ta ajiye mata kayan ta san zata buƙace su.

Inna ni kai kawai ta girgiza kafin ta zubo musu abincin a waje É—aya dan wasu lokutan tare Baffa na yake cin abin cin sa da ya yan na sa.
Koda Shatou ta fito har sun fara ci sun yi fiye da rabi da sauri ta nemi waje kusa da Baffa na ta zauna.Sai dai har ta ɗora hannun ta akan filet ɗin ta cire tana ya ƙunar fuska wasu daga cikin spoon da Inna ni take da su ta ɗauko ɗaya cikin su duk da kasancewar su yan ƙanana.Babu wanda ya ce mata ƙala daga Inna ni har Baffa na da yake nuna musu cin abinci da hannu ya fi lada da albarka.

Tare suka cinye abincin sai dai suna cinye wa itama ta miƙe dan jin cikin ta famm duka kallon ta suka yi cike da mamakin ɗan abincin da take cewa ta ƙoshi kan sa.
Bibu ne ya ka sa haƙuri yayi wa Baffa na rigaye da yake son yi mata magana

" Adda SHATOU wannan É—an abincin zai ishe ki keda bakya zama sai kinji ko ina tab".

Ya kai ƙarshen zancen yana kallon ta yar Hararar wasa tayi masa dan Dagske dai ta ƙoshi ɗin bata jin ma zata iya cin abincin dare dan ji take ko ina yayi mata baƙebaƙe.Inna Ni dai bata ce komai ba dan ta san hakan bai rasa na saba da yanayin da take ciki dan haka mutun yake komawa kamar mai lauyayi a wannan lokacin bare mata shine farkon ta.,dole zata samu ire iren waɗannan abubuwan.

Ganin Dagske ta ƙoshi ɗin dan kai tsaye ta cewa Bibu " Wallahi Allah Na ƙoshi ko Baffa n,a shafa ciki na kaji ".

Ta na sauke ayar zancen tare da kamo hannun Bibu da yake kusa ƙwace hannun sa.Yana ɓata fuska saboda ganin ya kw yi kamar har yanzu jikin ne dan duk da yake bata da lafiya da ta farfaɗo sai ta ɗan zubawa cikin ta ko ba da yawa ne,amma gashi yau ta ji sauƙi sosai ta kasa cin abincin.

Baffa na ne yayi Murmushi tare da shafa kan Bibu yana cewa " Habibullah bafa koda yaushe mutun yake zaune akan halayyar sa ba a wasu lokuttan ya kan iya aro na wani,dan haka ka daina damuwa Addan ka zata samu ta samu lafiya,gata nan komai tanayi,akwai abinda ya sauya mata cikin ."
Kai Bibu ya gyaÉ—a cike da tausayin yar uwar ta sa.

Ruwa ta sha kafin tayi gyatsa tare da yin godiya ga Wanda ya ƙara tabbatar musu da ƙoshin ta.
zaman ta nan gurin tayi tare da Inna ni da ta rage a wajen saboda sun tafi cire kaya su watsa ruwa su huta.

A ɓangaren su ALINA kuwa yau kusan kwana biyar babu mai iya yiwa wani magana acikin su dukkanin su sun koma kamar wayen da basu da lafiya saboda yadda suke azabtuwa da rashin kula junan su, ALINA tana son yiwa REENA magana sai ta kasa musamman dan ta bata haƙuri da Auntyn su tace ta bata saboda itace ƙarama idan ma faɗa su kayi komai zai wuce kasancewar an ga sun dai na ko chachar baki ne a aji babu mai kula kowa.REENA tsoro ne maƙil a zuciyar ta ga Tausayin yar uwar ta da ta san ya damuwar bugun da BILAL yayi mata a matsayin ya tsane ta ta tabbatar ko kashe ta zai iya yi in ya samu dama a ƙuruciyar ta dan haka ta sha alwashin babu ita babu magana da ya'yan na ta idan ma ya zo ba zai ƙara ganin ta ba har ya koma gurin aikin sa,tun da bai son ta,dan a zuciyar ta cewa take yi bada gangan tayi wa REENA haka ba ita kan ta bata iya cewa ga yadda aka yi ta mata wannan dukan abun da kawai ta sani shine ta hau ruwan cikin ta da faɗa ya fara.

Yau ne suka É—an sake dan kowaccen su É—akin ta take bacci ita É—aya a wahalce Umma tayi rarrashi ta saka musu ido.
Tana son sanar da Bilal sai dai shima har yanzu ba wani sakewa yayi ba duk daya kira kowannen su daga kakanni na sa har iyayen sa ya basu haƙuri na rashin sanar da tafiyar sa,ya sanar da su tafiyar gaggawa ce ta same su.

Sai shige da fice suke yi an chaɓa ado idan ka Kalli fuskar Ummah sai ka ƙara kallawa tayi kyau har ta gaji saboda tarbon mijin na ta dan yau sashen ta yake kafin ya yi tafiyar itace dan haka kai tsaye nan zai sauka kafin ya zagaya ya gano sauran.Ko Ina ya amsa a estate ɗin SSS zai dawo kowana cike da farin ci,sai kai komo suke yi ana ta gyare gyare dan kowane sashen suna cike da farin cikin Dawowar sa.
Su ALINA ma sun sha kyau matuƙa cikin shigar jeans da t shirt shigar ta su iri ɗaya dan duka kayan su iri ɗaya ne.Sun yi kyau sosai idan ba ka sansu ba zai yi wahala ka iya tantance ALINA ko SARINA a tsakanin su kamannin su suka ƙara bayyana masu cike da kyau da haiba da zallar Hutu da yake ƙara musu kyau da annuri.Koda kowaccen su ta ga iri ɗaya suka saka sai aka koma kallon kallo murmushi ne ya suɓuce ma Rina bayan ƙare ma yar uwar ta kallo dan ta riga ta fitowa.Ita kuma boss ɗin ɗaure fuskar ta tayi dan kar ta raina ta,dan tunda Umma tace ta riƙa sassauta mata kodan saboda tana babba ba ƙarfin su ɗaya ba..
Ummah ma murmushi ta yi tana janyo hannayen su ta zauna tare da su bakin ta washe kamar gonar Auduga.

***

" Hmmm wai kin san Hamida duk saurin nan da nake yi na gama exams na je Hutu wajen Ummah ashe ya koma gurin aiki tun daren da ya kawo ki da safe ".

Matashiyar budurwa ce ke zancen wadda a ƙalla zata kai shekaru ishirin a duniya tana zaune akan makeken gadon royal mai kyau

Murmushi Hamida dake zaune gaban fankacecen madubin da ya ƙara ƙawata ƙaton bedroom ɗin na su ta ce " Yaya Samira ke dai ba zaki raba kan ki ba ko,kin fi son Ya BILAL yana disga ki,kin san dai abun da kike yi baya so ".

Budurwar da aka Kira Yaya Samira ce ta galla ma Hamida Harara kafin ta ce "Ai Ummah na so dan bata taɓa ce mini komai duk da ta lura da abun da nake yi dan haka babu ruwan ki,idan kika matsa mini kuma yanzu na sassaɓa ki kina haɗa ki da Ummu " ta kai ƙarshen zancen tana jan mugun tsaki.
" ai da na sani da ban faɗa Miki ba,kuma ma gashi ya koma sai kije ki ƙara "...

Hamida ke zancen ƙasa ƙasa.

" Me kike faÉ—a "

Cewar Samira.

Baki Hamida ta turo gaba bata tanka ma Samira ba.

Ƙara jan dogon tsaki Samira tayi tana saka earpiece a kunnen ta.

***

" Amoh ta ƙi karɓan abincin ta nayi nayi ta ƙi karɓa har Sagir ya shiga ya bata ɗazu ta ƙi karɓa,gashi Nurse ɗin ta bata zo ba ".

Shiru Babbar matar da aka kira Amoh tayi wadda ke zaune cikin ado na alfarma daga nin ta ka san akwai dukiya a jikin ta,Numfashi ta sauke sannan ta furta " Suhaila kodai kiran Suhail É—in zamu yi duk da na san akwai ayyuka gaban sa,yau suna ganawa da patient ".

" Bari na gwada idan bata karɓa ba sai musan abunyi dan yunwa zata iya yi mata illa,gwara ya bata ko zata karɓa ".

Kai matashiyar budurwar da aka kira Suhaila ta girgiza fuskar ta cike da damuwa.

Tare suka kama hanyar wani lungu sai gasu tsaye ƙofar wani ɗaki mai duhu ko ina lif lif babu hayaniya.

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

Sai monday idan Allah ya kai mu.
Ina alfahari da ku masoyan wannan labari 🥰💋

Comment and like pls 🙏

_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P..1️⃣8️⃣

*BOOK ONE*
PAID

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*

🌙🌙🌙

Zaune take ta takure waje ɗaya jin hasken da ya gauraye ganin ta ya sa ta zabura da ƙarfi tana neman hanyar gudu.Saboda bata son haske ko kaɗan a cikin sa ne take ganin wasu irin halittu kala kala da ban tsoro shi ya sa ta ke natsuwa a duk lokacin da take cikin duhun.Cike da tausayin ta Amoh ta kashe hasken tana jin hawaye na wanke mata fuska kamar Bazasu tsaya ba.Haka ma Suhaila.Ɗaki ne dai mai kyau ko ina tsaf dashi sai tashin kanshi yake yi.
Haka wacce ke zaune ta da kan ta yake hargitse yana walƙiya cikin shigar kaya mara sa nauyi saboda akoda yaushe yana samun kulawa.Dan wasu lokuttan abun yana sakin ta amma a lokacin da duk abun ya motsa ɗakin ma sai ta hargitsa sa da ita kan ta dan kayan jikin ta gaba ɗayan su take yaga su bana ta ba har wanda ya matsa kusa da ita.Kwana biyu an samu sauƙin abun na ta ciwon ya kwanta.Sai dai yau ɗin nan akwai alamar tashin ciwon duk lokacin da taƙi karɓan abinci hannun kowa sai ciwon ya motsa Suhail ne yake mata dole shi kaɗai take shakku a cikin halin da take ciki dan duk tafi sabawa dashi a gidan,idan bata yi niyyar karɓa ba ko Daddy ya zo bazata karɓa ba sai Suhail dan Haka Amoh ta ce bari ta gwada in zata karɓa kafin a tado da Suhail ɗin daga aikin sa.
Chapter 34 · 0% Book details