Sashe 61
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafaɗa take girgizawa tana cigaba da yin kukan duk da ta na jin sarai abun da Inna ni ke faɗa,miƙewa Inna ni tayi kamar Dagaske take yi dan Muryan Almajirin ta ji a maƙota tunda ta kangar su babu wata girma gare ta dan ma duk haka gidajen na su suke na ƙasa dan ma Baffa na ya ƙara ma ta su girma sai suka ɗan banbanta.
Aiko cike da sauri ta miƙe tana ƙara sautin kukan ta.
Gefen madafar su ta É—auke shi a inda yake killace cikin wata yar Samira.
Inna ni dariya ke cin ta sai dai bata nuna a fili ba tayi a zuciya sai dai kawai a bayyane ta girgiza kan ta cike da ƙaunar yar ta.
A wannan karon kammm sai da ta yi Murmushi a bayyane ganin yadda SHATOU ke cin Tuwon kamar tana cin kashi sannan ga hawaye jage jage akan fuskar ta.Ga kan ta da take ta langaɓewa gefe cike da Sangarta irin ta ta tana yi tana Sharar hawaye.
Chan kuma mai ta tuna ta ture kwanon baki ture cikin shesshekar kuka ta ce " Ni Bama zan ci wannan É—in ba,haka kawai a yi ta bawa mutun tuwo,Ai Baffa na suna wajen Farauta na san zai zo da kaya masu yawa shi ya sa nafi son aje farauta saboda mugun Tuwon nan ".
Ta yi zancen tana share hawaye tana Hararar Tuwon Inna ni da yayi kyau na dawa ne sai ƙyalli yake yi ya tuƙu sosai kuma yayi taushi ya sha miyar mu ta kuka mai kyau.
Baki sake Inna ni take kallon ta jin tana kira ma Tuwon ta mugu aiko da sauri ta Æ™wala kiran Almajirin.âœï¸
Damm🤔
Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CEâœï¸_
Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga AlÆ™alaminâœï¸
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS ðŸ™ðŸ¥ºðŸ’”
_*KURMAN ƘADDARA*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BGâœï¸_
P________2ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
Almajiri kuwa dake kusa da sauri ya kwaÉ—a sallama bayan jin kiran da Inna ni tayi masa.
Zuru haka Shatou tayi da manyan idanun ta da suke ta wani maiƙo na hawaye tana dakatar da kukan na ta tare da zuba ma Inna ni idanu ganin in da gaske zata aiwatar da ƙudurin ta,ita kuwa Inna ni ba tare da ta ƙara bi ta kan ta ba, ta ɗauke Samiran ta karɓi roban Almajirin ita da kan ta,ta juye masa shi fuskar ta haɗe.
Shatou kuwa Wani sabon babin kukan ya buɗe haka ta zauna ta cigaba da rera kukan ta dan an kyautar da Tuwon da ba lallai ma ta cisa ba Inna ni ta san da hakan amma shine take ta uban kuka haka,Inna ni kuwa har lokacin Sallah yayi bata kula ta ba dan ta lura yan taɓarar sun ƙara motsawa.
Da maburkaki ta kora ta wajen Sallah ai ko tana gama sallahn ta É—aura daga inda ta tsaya ta zauna inda ta tashi ta cigaba da kukan na ta abun dariya.A haka su Baffa na suka same ta shida Bibu Sai rusar kuka take yi kamar wadda aka yiwa mutuwa.
" Wa ya ta ɓa mini Shatouwa ta matar ɗan birni " ?
Baffa na ya tambaya saboda yanzu firar ce suke yi da Bibu yana sanar masa ta ce bata son Iro ita matar ɗan birni ce dan haka bata ma son ko ganin Iro wai ya zo da sunan ko ganin ta ne shi ya sa take ta guje gujen ta cike da ƙuruciya.
Hawayen da suka ƙara silalo mata ta share kafin ta kalli Inna ni tana ɓata fuska sannan a hankali cikin shesshekar kuka tace " Ba Inna ni ba ce ta bawa Almajiri Abincin da ka rage mini,shine nace ina jin yunwa na fara ci ta bawa Almajiri ".
ÆŠan murmushi Baffa na yayi kafin yace
"A'ie baki kyauta mini ba,yar amanar tawa zaki yiwa haka ko Tausayin mu ba,a ji "
Ya kai ƙarshen zancen yana share mata wasu hawayen da suka silalo mata.
Inna ni dai bata ce musu komai ba sai ma yar madafar ta su da ta shige tana cigaba da aikin ta fuskar ta a sake dan kamar murmushi ke son fita sai dai ta ƙi bashi dama saboda shirmen na shatou a bun dariya ne.
" Share ta kin ji nama gasasshe ma yau zaki ci dan kamar mun sani muka tsaya muka gasa abun farautar mu tun a chan ungo gashi ".
Wata leda ya Fiddo da ita daga jakar da kayan na farautar su ke ciki da Bibu ya miƙo masa.Wata irin gaashi ce Baffa na suka yi dan dama har gashi suna yi idan sun je chan yunwa ta riƙe su sosai sai su gasa rabin abunda suka samu,yau ma hakan ne dan gashi suka yi na musamman akan abun farautar ta su, tsarkakakken nama ne kamar na kaji kamar kuma na tsuntsaye an banƙare su sun ji gashi mai tsafta sai tashin ƙamshi yake yi.
Take bakin Shatou ya fara motsi jin ƙamshi ya bugi hancin ta tun kafin a ciro shi daga ledar ita sai yanzu ma ta fahimci ta ji ƙamshin tun shigowar su rigimar ta ta hana ta ta tabbatar.
Guda ɗaya Baffa na ya ajiye mata akan wani ɗan madaidaicin filet da Bibu ya ɗauko yana murmushi ganin yadda hawayen Shatou suka ƙafe ƙaff.
Miƙa mata yayi yana furta " Yi Bismillah kici ki ƙoshi wannan duka na ki ne ".
Wani ya Fiddo da ban sannan ya ce " Bibu wannan na Innar ku ne ".
Miƙa ma Inna ni naman yayi cike da fara'a karɓa ta yi tana furta " Angode " dai dai lokacin ta fito daga yar madafar ta su kamar dai ta rumfar kara haka da aka ɗan shinge.
" Inna ni dan Allah mu ji naki ko yayi daÉ—in nawa "
Mara zuciya ya ji haushi Inna ni ta furta acikin zuciyar ta tana murmushi.
A fili kuwa cewa ta yi " Zo gashi kwaÉ—ayatu "
Cike da jin daɗi kuwa shatou ta matsa ta miƙa ma Inna ni nata zata saka mata baki.Ɗan kallon ta Inna ni ta yi kafin ta ɗauke kan ta ta ce " ɗibi na wan kawai tunda naki baya isar ki "
'' Nidai sai kin ci nawa sannan ki ji yadda gashin sa yake nawa gashin ya fi daÉ—i "
Babu musu kuwa Inna ni ta yago kaÉ—an tana neman kaiwa bakin ta.
Karaff Baffa na da ya fito yan zu daga ɗakin sa bayan shigar sa yace " A'ee kar ki janyo ma kan ki rigima ƙyale ta naman ta na farar tantabara ne "
" Naki kuma na ɓaƙa ne,barta ta ci ".
Cike da tsoro kuwa Inna ni ta mayar maa Shatou da shi a cikin filet É—in tana zuba masa idanu kamar ta ga abun tsoro.
Baffa na kuwa bai ƙara cewa komai ba ya faɗa wajen wanka da ruwan da ya ɗiba yanzu.Ba tare da ya wahalar da Inna ni ba dan wasu ayyukan yana yin abun sa ne ba tare da damuwa ba dan haka ita har ta saba.
Shatou kuwa kallon Inna ni tayi ganin yadda ta tsira ma naman ta Idanu hakan ya sa '' Ta ce Bafa duka zan cinye yanzu ba zan ajiye wa su Amina ne "
Numfashi Inna ni ta sauke kafin ta fara tsakurar nata naman da ya ji gashi mai kyau dan har da kayan gashin akwai a cikin sa ba Zallar naman ba ne.
Bibu ma É—akin sa ya shige ya canza kayan jikin sa kafin ya fito yana bawa shatou labarin yadda suka yi farautar yau dan harda gasa suka yi da wasu yan farautar kuma su suka yi nasara tana ta murna tana cin naman ta sai da ta ga ta ci rabi sannan ta ce " wannan na su Amina ne, Ramata Jawairiyya "
Haka ta raba naman a ledar kowannen da gefen sa ana yi ana suÉ—ar hannu.
Inna ni ma ta tsakuri nata jin cikin ta ya ƙoshi ma hakan ya sa abin cin da take neman zubo musu ta ke neman samun murfin samira ta rufe sa saboda tunda suka yo gashin nan ta san sun ƙoshi dan haka babu buƙatar tambaya,amma saboda tantance wa ta ce " Habibu na na zubo maka abincin ".
Cikin sa ya shafa yana cewa " Wallahi ji nake kamar ma zanyi Amai Inna ni a dai bar shi sai anjima ".
Kai ta jinjina.
Baffa na da ya fito kuwa shima ta tambaye sa lokacin yana alwallah kai tsaye ya ce " Wallahi Mun ƙoshi sai dai anjima "
" Ai dama ɗana ya ce kun taƙe cikin ku,na dai tambaya ne kawai "
Murmushi Baffa na yayi kafin ya ajiye butar da ya gama alwallah da ita a mazaunin ta.
" Assalamu alaikum Wai ance ana Sallama da shatou "
Wani yaro ne ya shigo yana zancen bayan yin Sallama wadda ko amsa masa ba ayi ba ya jero kalamin.
" Inji uban wa "?
Shatou ta tambaya cike da Hasala dan ko ba,a faÉ—a ba ta san nataccen ta ne.