← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 110

Sashe 13

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Babbar matar dake zaune a kan kujerar alfarma tayi irin murmushin nan na masu aji da wata manufa.
Kafin ta É—an muskuta sannan ta ce " Ina son zan tura ki wani waje ma dan akwai aikin da nake son yi dan na fara hango matsala babba dole na sake sabon shiri,Ba zan lamunci ina kallo ba kasuwa ta watse dani babu riba"
" LINA rigimammar kan ta ce da kika sani luba,shi ya sa nake son yarinyar " Sai ta ƙara sa zancen tana sakin murmushin da ita kaɗai ta san ma,anar sa.

Dariya itama yar dattijuwar matar da aka kira luba tayi tana yiwa uwar ɗakin na ta kirari ganin ta miƙo mata bandir na yan dubu dubu guda uku.

Fitowar yar tace ƙwaya ɗaya tal mai suna Hamrah ya sa juya wa tana kallon ta fuskar ta cike da murmushi tana furta " Yar gwal an fito " Baki yarinyar ta cunno gaba irin na sakuwa kafin ta faɗa jikin mahaifiyar ta tana rungume ta...

" Momy na gaji da ya wallahi tun da na dawo school ƙafafu na suke ciwo gashi bakya nan bare ki rarrashe ni,Yawwa Momy kin sa wai su REENA yau dambe suka ƙara yi a schl kwana biyun chan ba su yi ba,har naji daɗi amma yanzu kin gan yadda suke dambe,ni dana ga ba,a zo ɗaukar su ba na san halin LINA nace wa yusuf driver kawai ya wuce ba sai na rage musu hanya ba,dan malam Adamu bai je ɗaukar su da wuri ba ".

Murmushi matar tayi kafin ta furta " Ya yan ku ne ya dawo shine ya tsayar da shi,suka je É—auko su tare,nima duk yanzu Luba take faÉ—a mini "
Ai bata bari ta rufe baki ba ta dire ƙasa cike da wani irin tsalle tana furta " Momy nayi part ɗin Ummah na ga Yaya ".

" A'ah karki je a haɗa dake gashi da baki kin ce dambe suka yi na san shi ma BILAL ɗin ba zai rasa ji ba ko gani,ba zan lamunci ya haɗa dake ya sakar muku ƙarfin sojoji ba,ki bar su chan da yawar su ".

Tabbatar da zancen mahaifiyar ta gaskiya ne hakan ya sa ta dawo jiki mace ta zauna kusa da Mahaifiyar ta tana É—aura kan ta a bisa kafaÉ—ar ta tana rungume ta,dan tayi kewar ya'yan na su.

Dariya Momy tayi haka Luba dan sun san Hamrah da Shegen tsoro.

Miƙewa luba tayi ta mata sallama tana ficewa daga part ɗin gaba ɗaya,cikin son isar da saƙon uwar gijiyar ta ta da ta san ko saƙon me ne ne.✍️

INA ƊAN FAMA DA ZAZZAƁI NE SHI YA SA KUKA JI SHIRU,KUMA IRIN ZAZZAƁIN NAN NE MAI TAKURA🥲😔.ALLAH KA BAMU LAFIYA MAI AMFANI.🤲

Masoyan SHATOU a yi haƙuri zamu koma gefen ta a next page in sha ALLAH.

Like share,and comment 🙏

Wannan littafi na kuÉ—i ne.
Amma in sha Allah Zan baku page goma sha biyu free kamar yadda nayi niyya..
Masu son fara yin payment zaku iya farawa ga details a ƙasa👇
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞

*TAFIYAR TA DABANCE SAI AN BIBIYA AKAN GANE HAKAN.✍️*
_Typing_

*💋KURMAN ƘADDARA💋*

*©®Faiza Almustapha Murai*

*FA'EEH BG*✍️

*BOOK ONE*

free pages👌

P..0️⃣7️⃣

>>>>>>>>>>>> > >>>>>>>>>>>>>

*CONTACT DIS LINE 👉08069059746 FOR ADVERT.*

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

Channel link
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

Posting room link
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn

*LITAFFAN MARUBUCIYA*
*A MAFARKI NA SANTA*
*RAYUWAR MU A YAU!*

🎀🎀🎀

***Sai da suka ci girkin Inna ni sannan suka watse kamar kar su rabu.
Dare nayi hankalin Inna ni ya fara tashi ta san cewa SHATOU dole sai ta fita, fira suke yi amma hankalin ta na kan ta har suka ɗauko abun karatun su Baffa na ya fara bita musu bata natsu ba.Kamar kullum sallar isha'i ce ta sanya su miƙewa domin gabatar da sallah akan lokacin ta,musamman ta isha da take mai nauyi.
A tsakar gida tayi Sallah tare da Inni amma duk da haka hankalin ta ba a kwance yake ba,Suna gama wa Nan bacci ya ɓingire ta wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar inni ni ganin baccin take yi Dagaske.Gyara mata kwanciya tayi ta ɗan sha iska kafin su tashi ta mayar da ita ɗakin ta.
Addu,oin ta ta cigaba da yi bayan ta gabatar da shafa'i da wutiri.
A haka su Bibu suka dawo daga masallaci suka tarar da ita tana baccin ta cike da natsuwa.
Murmushi Baffa na yayi yana gyara mata hannun ta ɗaya daya lanƙwashe.
Sannan ya furta " Shatouwa da bacci da wuri yau,halama dai A'ie Addu,a kika mata ta bacci da wuri ".?

Inna ni dariya tayi tana furta " gata nan dai,nikamm babu ruwa na Allah dai ya dubi zuciya ta ya kwantar muna da ita da wuri yar neman,dan haka karku ƙalubalance ni" Ta kai ƙarshen zancen tana Murmushi tana miƙewa ta zubawa Bibu abincin sa da ya bai ci ba ɗazu yace ya ƙoshi sun ci abinci a makaranta kuma cikin shi ya cika sosai.
Dan haka kowa yaci nashi ba dashi ba.

Fira suka taɓa kaɗan kafin aka mayar da Shatou ɗakin ta,Sannan dukkanin su kowa ya koma na sa ɗakin bayan sunyi wa juna sai da safe.

Kamar ko da yaushe bayan dukkanin sawu ya ɗauke ta miƙe bayan tabbatar da Baffa na yayi bacci ta miƙe ta haɗe kai da gwiwa ta fara wani irin kuka mai tsuma zuciya,kuka ne mai fitowa daga ƙasan zuciyar ta wanda yafi na ko yaushe,yau zantukan SHATOU sun ƙara mata wani irin rauni a cikin zuciyar ta,ta kusa ɗaukar Awa tana yin wannan kukan mai cike da rauni da kewa sannan ta share hawayen ta ganin tana neman jazawa kan ta ciwon kai.
Miƙewa tayi ta fita da zummar wanke fuskar ta sai dai Turus ta ja ta tsaya domin kuwa bakowa taci karo dashi ba face Baffa na fuskar shi cike da tausayi idanun sa sunyi jazir dan akwai farin wata sosai.
Kan ta ta sauke ƙasa,ta raɓa shi tayo alwallah.Shi ma bai ce mata ƙala ba har sai da ta kusa shigewa ɗakin na ta sannan ya ambaci sunan ta cike da tausayin ta.

" Komai yayi tsanani maganin sa Allah,hakan da kika yi shine dai dai, Sannan ba zan gaji da maimaita Miki ba A'ie ki fito ki faÉ—i wata maganar da zata sa mu fahimci wani abun da yake damun ki,zancen da kika bani a baya ba zai iya saka a fahimci komai ba,har a san abun yi,amma kiyi tunani ina son sanin komai dake faruwa,amma ba zan matsa Miki ba ina jiran ranar da kika tashi faÉ—a zan saurare ki ".
Yana gama maganar sa ya shigewar sa É—akin sa dake kusa da nata kaÉ—an.

Jikin ta ne ya ƙara mutuwa wani sabon kukan na son ta so mata dan Dagske tana cikin damuwa,kuma tana buƙatar mai Rarrashin ta.

Shigewa tayi ta shimfiÉ—a sallaya ta tayar da sallah sai da tayi raka'a shida sannan ta fara kai kukan ta ga Ubangiji hawaye na kwaranya a cikin idanun ta.
" Allah idan har abun da mutanen Shatou suka faɗa gaskiya ne Allah ka kare mini su,a duk inda suke,Allah ka bata lafiya,Allah ka yaye mata,Allah bani da tsimi bani da dubara Allah ka yaye mini damuwa ta,Allah ka kawo mini mafita,Allah ka kare mini rayukkan su a duk inda suke " Kuka ne ya ƙwace mata mai zafi da raɗaɗi da ƙuna sai da tayi mai isar ta anan sannan ta kwanta nan kan sallaya bacci ya kwashe ta mai nauyi.
Baffa na dake tsaye bakin ƙofar ɗakin ne da ya ji komai da take faɗa ya koma ɗakin sa da sauri cike da tambayoyi a cikin zuciyar sa ya je da zummar ƙara bata baki ya ji abinda bai san inda zai saka kalaman na ta ba da ba komai ya fahimta ba sai dai ya sanya su a cikin zuciyar sa cike da mamakin mutane shatoun da ya ji ta faɗa wanda shi dai duk iya sanin sa da yar ta sa ba ta da wasu mutane tun da basu taɓa tashi ba bare a gan su.
Addu,ar kwanciya bacci yayi bayan ya ƙara tofekke su Shatou da Addu,a ya sayo gidan sannan ya kwanta shima cike da tunani a haka har bacci ya kwashe sa jiki mace.

Yau Litinin hakan ya sa tun da suka tashi sallar asuba basu koma bacci ba,saboda yin ayyukan gidan da wuri da kuma zuwa makaranta akan lokaci tsaf suka shirya bayan sun jido ruwa tare da yiwa Inna ni share share,karin kumallo suka yi sannan suka fice a tare bayan yiwa iyayen na su mun tafi.Addu,a suka bisu da ita.Ba a ɗau lokaci ba shima Baffa na ya fice kasuwa dan yana da ɗan ƙaramin shago a kasuwa yana siyar da kayan farauta duk wani nau'in kaya na farauta,da kuma Ganyen shayi ko wane iri ne ana samun sa a wajen sa.

Tun da suka isa makaranta tsirarun yaran da ke wajen ke kallon su musamman shatou sai su kalle su suyi dariya sai suyi gaba.Tun abun na bawa shatou mamaki har ya daina bata.Bata ce ma Bibu komai ba haka shima sai dai kowa ya shigewar sa aji cike da mamakin kallon da ake musu.
Da shigar ta Ajin su ta ji ƙana nan maganganu na tashi sama sama gashi sai kallon ta suke yi.Kamar ance ta kalli allo saboda ta iya karatun Hausa tsafff ta zaro ido tana kallon Allon da ya ƙunshe da rubutu kamar haka " daga yau ni Shatou suna na ya koma Kosongo,ko shatou kosongo ".

Abun gugar allo ta É—auka tana furta " Uban wa yayi wanann rubutun nayi imani da Allah ko waye yayi shi sai ya É—an É—ani azaba ta sai ya gwammace Ni shatou banzo duniya ba ".
Chapter 13 · 0% Book details