← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 110

Sashe 32

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da tashin hankali Ummah ta kalli agogo dake nuna ƙarfe goma na dare gashi dama suma sun yi kiran na sa layuka shiru har su Sir sun gwada dukkanin su dai hankali tashe dan yayi abin da bai saba ba.Ya tafiyar sa babu Sallama.
Gashi bayan haka sai da su Reena suka ƙara kwata wani damben gurin bada haƙuri da Ummah ta saka suyi wa juna,su yafewa juna.LINA uwar rashin haƙuri daga kawai REENA ta share ta shikenan ta fara ƙoƙarin kaima ta duka,A fusace,duk da tana cike da tausayin ta,kuma tana son bata haƙurin Allah ya sa Ummahn tana kusa,sai faɗan ya tsaya nan, sai dai har yanzu babu mai yiwa wani magana a cikin su sai gidan ya koma babu daɗi daga ita sai su Rabi ne suke ɗan sakewa suma ba wai suna jin daɗin bane saboda dama su LINA ke ƙawata gidan yau gashi kowaccen su kamar an mata mutuwa.
Ga tashin hankalin yadda ya yan na su yake ciki dan haka estate ɗin ta koma ko ina shiru dan tun rana suke kiran layin sa daga ƙarshe suka bar shi haka tun da sun binciki yaran sa since lafiya lau yake.
Yana bacci koda suke kiran bayan isar su,sunyi hakan ne suma ba tare da suna da tabbacin bacccin yake yi ba.

" Yanzu ya za,ayi a fito dashi ina tsoron kar ace wani abun ne ya same sa,bari na kira Abban su kawai AB ".
Ummah ce ke zancen cike da wani irin raunin ta da ya bayyana.

AB yana niyyar ƙara furta wata magana sai ya ga an buɗe ƙofar bedroom ɗin dan haka ya ce ma Ummah " Ya fito he's fine " kafin ya katse kiran yana sara masa (Solidarity)cikin girmamawa.

Numfashi Ummah ta sauke mai nauyi kafin ta ja ajiyar zuciya tana tunanin yadda zata kira Abban su ta tada masa da hankali duk da ta san shima ɗin zai iya kira kowane irin lokaci ƙila ma ya kira bai same sa ba.

Daga chan ɓangaren kuwa kallon AB yayi kafin ya ɗauke kan sa dan ko bai tambaye sa ba ya san da wa yake waya ganin yadda ya natsu dan suna mugun girmama Ummah suna jin ta kamar mahaifiyar su saboda mutuncin ta ga kowannen su sun ɗauke ta kamar uwa.

Direct kan dininng ya nufa tea ya haɗa kawai mai kauri ya sha sannan ya miƙe ya dawo falon yana sauke numfashi.Tashar labarai ya kunna ko hakan zai rage masa Damuwar da yake ciki.Mayar da hankalin sa yayi ga labaran da ake haskawa a tashar sai dai ba wani fahimta yake ba,dan hankalin sa na ga su REENA yana son ya ji ya ƙannen na sa suke amma ya san yanzu sun isa yin Bacci saboda da wuri suke kwanciya bacci saboda school.

Ganin babu abinda zai fahimta a cikin tvn hakan ya sa ya miƙe ya koma bedroom ɗin sa.A chan ma ya daɗe zaune kan cusion kafin ya miƙe ya doshi bed ɗin sa, zuciyar sa daƙushe.Dan tunda suka iso ɗin ya shige ya rufe kan sa saboda damuwa,chan yayi sallolin sa,ko abinci bai ci ba sai shayin da yasha yanzu ko shi saboda yaji yunwa na neman illata sa ne.Duk ya tuna da yadda ya daki Lina sai zuciyar sa ta yi zafi saboda ya san bata kai ta samu irin wannan ba duk da chan baya yayi bugun ta amma chan bata yi hankali ba yanzu kuwa ta san zafin jikin ta.Dukkanin su rarrashi suke so saboda yarinta ce dukkanin su ke damun su amma ba yadda zai yi dashi har mahaifiyar su haka, Allah ne ya basu nasu yan biyu ɗin haka.Numfashi ya sauke mai karfi yana kawar da duk wani tunani tare da yin addu'ar bacci take kuwa bacci ya ɗauke sa mai nauyi.

***

Tun da ya shigewar sa bedroom ɗin na sa ya faɗa toilet saboda haka kawai yake jin jikin sa babu daɗi yar tafiyar nan da suka yi ko ina tsami yake masa saboda yanayin tafiyar hanyar duk da manya motoci ne ba gane yanayin hanya suke yi ba amma shi duk ya gaji haka yake ji dan haka ya cika ƙaton bathtub ya faɗa ciki da ruwa masu ɗumi da ƙamshi yayi haka ya kai sau uku kafin ya fito bayan ya ɗauro wanka tare da yin alwallah.
Tsaye yayi gaban mirror madaidaicin jikin sa mai cike da ƙira wadda take mummurɗe ya ke ƙarewa kallo kafin ya fara murza mayukkan sa masu ƙamshi yana bin ko ina na jikin sa da su a hankali.
Turarukkan sa ya shafa masu ƙarfi da kyau.sannan ya tada Sallah bayan ya saka Jallabiya mai kyau da tsari.
Cikin natsuwa ya gabatar da Sallah azahar da ta fara gota lokacin ta saboda ya daÉ—e toilet bai lura da lokacin ba.

Yana gamawa duk da yunwar da yake jin akwai ta acikin sa dan ko breakfast bai yi ba haka ya haye lafiyyayen gadon sa bayan cire Jallabiyar da yayi ya koma da ga shi sai short, duvet ya yi cover dashi mai taushi fari ƙar dashi kafin ya ƙara gudun ac daga kwancen sannan ya rufe idanun sa take bacci mai nauyi ya kwashe sa.

Mubarak da ya san tabbacin sai yayi baccin nan na Hutu dan haka shima ya wuce na sa gefen ya huta kamar yadda ya huta ɗin dan shi ma ya ɗan gaji dan su suka yi yawon ma,sai dai duk ya tuna da Shatou da mai gidan na su sai yayi guntun murmushi ya girgiza kan sa ya rasa dalilin da ya sa yarinyar ta kasa fice masa arai amma ya san tabbacin MAHAJ ya manta da wata halitta ita Shatou dan sun ji sunan ta bakin Iro.Ya rasa har yanzu dalilin da ya sa ya kula yarinyar shi da ko su Sajida da Salma da ba su ishe shi kallo ba duk da kuwa gida ɗaya suke zaune dasu kuma yan uwan sa ne.Amma ita har ya kula ta gata wata figaggiya da ita dan ya san a ƙalla ba zata wuce shekara goma ba ma a duniya dan bai tunanin ta ma hau da sha ɗaya saboda yadda take yar cukul da ita ga rashin tsawo ga rashin jiki.

"Amma Ya MAHAJ ya dawo fa tun É—azu "

Wata yarinya ta furta mai matsakaicin jiki sai dai ita ma a kallo É—aya zaka san tana da yarinta dan zata kai shekara sha uku.

Kallon ta matar da aka kira Amma tayi kafin ta furta " shine bai shigo ba kuma har yanzu Samra "

" Amma akwai gajiya kin sani ko Amma ai na san zai shigo dan bana jin ko gefen Ayya ya shiga,Nima ga Yaya Muby na gani yanzu yace ai sun dawo ".

Kai matar ta gyaɗa kafin ta ce " Sun kwaso gajiya kamm gashi ko breakfast ɗin sa bai yi ba gashi har lunch ya gota,ban san ƙiyayyar sa da abinci ba,haka yayi tafiyar nan ".

Ta kai ƙarshen zancen tana cigaba da ɗan duba saƙonni dake shigowa a wayar ta.

Yarinyar da aka kira da Samra kuwa ɓata fuska tayi tace " Amma dagaske bai yi breakfast ba,kuma shine har yanzu bai fito yayi lunch ba ".

Murmushi Amma tayi kafin ta ce " To Sarkin kuka kar ki fara yi mini kuka gurin nan idan kuma Ayya ta isko ki babu ruwa na ke da ita ne,wanda kike Tausayin ko ajikin sa hasalima É—abi'ar sa ce hakan,gwara kiyi shiru yadda muka saka masa ido ki saka masa,idan ya ga dama zaki gan sa ya fito yanzu ".

Takai ƙarshen zancen tana share ma Samra hawaye dan har sun fito kuwa dan tana mugun son ɗan uwan ta da Tausayin sa shi ya sa a duk lokacin da yazo nan take cikin farin ciki duk da basu wata magana dashi amma wulgawar sa na saka ta farin ciki.Ko fitar nan ba ta so ba saboda ta san zai sha wahala, Allah ya ɗaura mata ƙaunar ɗan uwan ta,Ammah har cewa take yi ta fi son sa fiye da ita sai tayi dariya dan ita ta san tana son kowa a cikin yan uwan ta bare ma mahaifiyar ta.

Miƙewa Samra tayi da sauri.

" Ina zaki je Samra kuma ba dai gurin shi zaki je ba "
Cewar Ummah ganin ta miƙe tsaye kamar an tsikare ta.

" Gurin Ayya zani ko zata iya Fiddo da Ya MAHAJ ya yi lunch kar yunwa ya kama sa "

Shiru Amma tayi kamar zata hana ta sai dai ta san ko ta hana ta tunda tayi niyya sai ta kai jiki dan haka ta ce " Samra ki bari zai fito kinji ba sai kin je wajen Ayya ba ".

Ai ko Samra bata ma jira ta kai ƙarshen zancen ba ta falfala da gudu tana dariya.

Da sallama ta shiga wani ƙaton falo wanda ƙofar shi take a cikin ƙaton falon na Amma dan ƙofofi ne gasu nan birjik wasu sama wasu ƙasa ta Ayya tana ƙasa saboda tsufa.

" Ke lafiya kika faÉ—o mini falo babu Sallama,ita Maryam bata ga fitowar ki haka bane,kamar zaki je gasar Guje Guje "
Yar dattijuwar tsohuwar da Hutu da kwanciyar hankali ya ratsa ta tayi furucun,sai dai daga nin ita fitinannun tsofaffin nan ne masu rigima.Dariya Samra tayi kafin ta haye kan rugs na ƙaton falon na Ayya sannan cike da tausayi ya yan na ta ta ce " Ayya Yya MAHAJ yau gaba ɗaya bai saka abinci a cikin sa ba fa,gashi sun yi tafiya sun dawo kuma bai nemi abinci ba,dan Allah ki je ki tado dashi ko bacci yake yi ".Ta kai zancen tana ɓata fuskar ta tare da riƙe hannun Ayya ɗaya.
Chapter 32 · 0% Book details