← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 110

Sashe 29

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har ƙasa Mubarak ya duƙa ya gaishe su cike da girmamawa.Cikin jin daɗi Hon Gagara yayi masa sannu da zuwa tare da yan tambayoyin ya komai ya wakana nan take kuwa Mubarak ya zayyane masa komai dan ya san dama shi ne zai yi aikin ba dai shi ba.

" Dama kuma shine zai yi aikin a cikin aljihun sa amma yace kar a faÉ—a maka ".
Mubarak ya kai ƙarshen zancen yana kallon ƙofar inda ya san zai iya ɓullowa kasancewar ɗakin sa yana da ƙofofi daban daban.

" Kai Masha ALLAH "

Hon Marafa ya furta yana cewa " Allah yayi albarka gaskiya koda yaushe ina taya ka farin cikin samun wannan yaro,dama zai iya shiga siyasar mu da munci riba sosai dan daga nin sa zai iya da kowane Shege ".Ya kai ƙarshen zancen yana dariya.

Hon Gagara da fuskar shi ta kasa daina bayyanar da murmushi ne ya girgiza kan sa cike da ƙaunar ɗan na sa ya furta " Baya ra'ayin ta da a ce yana da dama Ni kaina ba zan yi ta ba,sai dai yana girmama abun da nake so kamar yadda nake girmama na sa a matsayi na na mahaifin sa dan haka ma tun farko ban taɓa kwaɗai ta masa ba tunda ya nuna mini nikaina baya son ta da ni ".

Su ma sauran murmushi suka yi suna jinjina kai.
Mubarak kuwa miƙewa yayi cike da Murmushi.
Yayi musu sallama Sannan ya miƙe ya bi bayan Mahaj ɗin da wayoyin sa a hannun sa.Upstairs ne na alfarma mai kyau ya take da ɗan sauri.
Wata haɗaɗdiyar ƙofa ce ta alfarma ya bi inda sai da yayi yar tafiya sannan ya isa dai dai wata ƙofar mai kyau da tsari.Buɗe ta yayi a hankali.Ƙamshin ɗakin ne da ya daki Hancin sa ya san ya sa rufe idanun sa dan jin kamar an yi masa buɗaɗen turare bayan fitar su,wanda bai rasa na saba da yawan gyaran da yake samu daga wani daga cikin masu kula dashi. Sanyi ta ko ina lif lif sai tashin ƙamshi yake yi.Kasancewar babu wani shamaki tsakanin su hakan ya sa ya shige ciki da sallama ɗauke a bakin sa,bayan buɗe ƙofar.
Tsitt haka É—akin yake dama bai yi zaton zai same sa nan ba hakan ya sa ya a jiye masa su nan ba tare da ya neme sa ba.
Ajiye komai yayi sannan ya fice bayan ya rufo masa ƙofar.

🔏🔏🔏

SHATOU bata da kata ba sai da ta yi gudu mai nisa Sannan ta dakata tana sauke numfashi tare da bin su da kallo daga nesa dan ta musu nisa sosai,kawo War su kusa da ita ya sa ta sakin dariya cike da ƙuruciya ta shammace su ta ƙara falfalawa a guje tana waigen su.Su Amina kuwa a gajiye kowannen su ya dakata suna kallon juna,Kafin suka mara mata baya suna dariya.Dan sun fahimci yan wasar ne suka motsa take son wahalar da su.Dan ta kan yi musu haka a wasu lokuttan.A ɓangaren SHATOU kuwa ɗan wannan lokacin ta ji ta tsinci kan ta cikin nishaɗi kamar ba ita ta gama kuka ba ɗazu.Da gangan ta bi gefen da ta san abokan Iro suna zama duk da ba hanyar ta bace aiko aguje ta biyo hanyar tana kururuwa " Kura! Kura ! kura! " da farko basu tsorata ba sai dai ganin yadda take waigen bayan ta sai suka yi zaton wajen farauta ta kuskure ta biyo ta,duk da sun gan ta da uniform,A guje suka miƙe dukkanin su ganin Dagske take yi dan har da hawayen ƙarya irin na tashin hankali, A guje suka miƙe har wasu na faɗawa kan wasu ba su kaɗai ba har majalisar dattawa dake chan wata rumfa zaune a guje ko wannen su ya fara neman hanyar gudu dan tsira da rayuwar sa,tun da har ita yar mafarauci ta iya gudu su mai zai su tsaya a guje, aiko akayi ta kururuwa ana faɗawa gidaje.Iro da ya kamo hanyar zuwa majalisar ta su bayan isar da saƙon ga mahaifin sa ya an kara da abun sa ke faruwa ganin mutane na ta gudu ana kura ta gudo daga daji ta biyo SHATOU da farko tsaye yayi bai yarda ba sai dai bayan hango ta a guje itama kan ta hakan ya sa ya auna a masifar gudu yana waigen bayan sa cike da wani mugun tsoro da ya dirar sa tare da tsine ma shatou da ta jaji ɓo musu bala'i.Shatou kuwa da ta hango sa ƙara ƙarfin gudun ta tayi tana sakin ƙarar neman taimako tana haɗiye dariyar ta wadda take saki idan ta faki idon jama,a masu gudu.Mai gari da jama'ar sa dake ƙofar gida cike da farin cikin saƙon da ya same sa ya ga Iro a guje yana faɗin kura ta yi ɓatan hanya daga daji ta biyo SHATOUn Jibril farauta yadda zasu gane kai tsaye aiko ko rufe baki bai yi gaba ɗaya suka runtuma a guje suna neman gurin ɓoyo.
Daga mai gari har yan fadar sa wani É—aki suka rufe suka shige duk uban zafin da ake tsulawa a gari.Tsit haka garin ya koma kamar anyi mutuwa.
Cike da natsuwa ta shiga gida cike da murmushi a kan fuskar ta kamar an biya mata aikin hajji dan wani daɗi take ji musamman ganin yadda ta rama abun da Iro yayi mata cikin ruwan sanyi duk da har yanzu nata huce ba amma kina komai ta saka shi tiƙar gudu..
Ummah ce ta ke ta kallon baki sake kafin ta iya furta wani abu sai ga su Bibu sun faÉ—o a guje su huÉ—u.
Amina ce ta baya saboda ta gaji sosai.
Shessheka suka dinga yi a gajiye.Inni da É—ai É—ai take bin su da kallo ganin yadda kowannen su yake a hargitse cike da tsoro gashi da alama gudu ne Suka yi bana wasa ba.
Kallon SHATOU suka dinga yi harda leƙen ta suna cigaba da sauke numfashi.

" Me yake faruwa ne,ku ka shigo gidan wani hargitse kuma daban daban " .?

Inna ni tayi tambayar kafin su bata amsa sai ga Baffa na ya shigo fuskar sa cike da tashin hankali mai girma.Dan ko sallama bai samu ya yi ba sai ganin sa suka yi.
Idanu ya zuba ma SHATOU ganin ta hankali kwance sai murmushi take saki, kafin ya mayar da idanun sa kan su Bibu suma sai dai su tasu a tashe take sai nishi suke saukewa.
"Allah yasa lafiya,Baffan su "?Cewar Inna ni

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " Babu komai dama na zo duba wani abu ne ".
Yayi zancen yana shigewa ɗakin sa da sauri cike da jiran ta kwana dan yasan magana ce Babba shatou ta janyo dan yana kasuwa yaga ana guje guje.ya tambaya lafiya aka sanar masa da yar sa ce kura ta biyo yanzu haka kowa neman wurin ɓuya yake yi dan haka babu ɓata lokaci ya rufe yayo gida cike da tashin hankalin da ya kasa barin ƙwaƙwalwar sa da mamaki dan ya san dai Shatou na makaranta ya za,ayi ta je gurin farauta duk da ya san halin ta tana iya zamewa ta tafi tun da wani lokacin ta kan yi hakan,wannan tunanin yasa ya zo gida cike da sauri.
Sai dai bayan shigowar sa gidan ya gan ta zaune kan yar guntuwar kujera hankalin ta kwance ta cire hijab É—in,tana wasa da jelar gashin ta da ya sauko har kan kafaÉ—un ta.
Su ko su Bibu kowanensu su shima hankali tashe kamar yadda yake.Numfashi ya sauke yana neman mafitar wannan case ɗin domin kuwa ya sa akwai matsala Babba saboda SHATOU garin ta taɓa gaba ɗaya yau.
A tsakar gida kuwa kallon tuhuma dukkanin su Inna ni take bin su dashi tana son karantar wani abu kafin a hankali jikin ta mace ta ce " Amina me ta aikata " ?
Shiru Amina tayi fuskar ta cike da damuwa ganin yadda SHATOU ta marairaice mata ta san faÉ—in zai iya zame mata illa.
Kan Ramata Inna ni ta koma dan ta ji ko zata samu amsar tambayar ta sai dai itama ɗin shiru ce sai kai da ta sunkuyar ƙasa ita fuskar ta na son bayyanar da dariya saboda tuno yadda ta ga mutane nata guje guje harda manya masu ƙaton tumbi na ƙauyen su,koda suka iso hanyar da shatou ta bi basu ga ƙurar ta ba sai dai sun samu labarin kura ta biyo ta daga wajen farauta,dan haka tun chan suka fara sheƙa dariya dan duk sun san ƙarya ne,tun da tare suke da ita.Sai dai saboda sanin da suka yi akwai matsala ya sa suka yo gida cikin sauri dan sun san akwai rigima Babba zasu yiwa SHATOU abun da zai saka ta farin ciki dan haka suka yanke shawarar abun da zasu ce,ba zasu taɓa ƙarya ta ta ba,ba kurar bace zasu ma bada shedu.
Chapter 29 · 0% Book details