← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 110

Sashe 51

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da murmushi kwance akan fuskar sa ya tallabi Reena ta dake gaba juya ta yayi kamar yar kaza suna ta dariya haka ma Leena dukkanin su dariya suke yi cike da farin ciki mai tarin yawa mai cike da kewar ya'yan na su.Matashin saurayi ne kyakkyawa kamar dai yanayin sa da Bilal sai dai Bilal ya É—an É—ara sa ko daga yanayin fata dan shi ta sa mai duhu ce kaÉ—an.
Samir kenan ma'aikacin Custom service kamar yadda muka sani shine É—a na farko a wajen Hajiya Maryam Uwar gidan Ibrahim Sada Saleh.
Samir yana aiki a kano kuma ya kan shigo gida ya ga yan uwan sa idan sun samu hutu ko ya É—auko hutun.
" Yaya Sannu da dawowa, shine ranar da muka yi waya da kai a wayan Ummah,ka ce ba yanzu zaka dawo ba sai bayan an gama a zumi ".
Reena ce tayi zancen tana shige wa jikin sa bayan sun zauna a tare a kan ɗai daga Cikin manyan kujerun dake a cikin ƙaton falon.
Hajiya Maryam dai da suke kira Hajiya murmushi ne ta ke ta yi cike da dattako da tsantsar ƙaunar ta ga yaron na ta da yan uwan sa take kallon su.
" Yanzun ma Reena ba zama na zo yi ba na zo ganin Baby ta ne,nayi kewar ku baki É—ayan ku ".
Ya yi zancen yana kallon Leena da taɓata rai,dan a tunanin ta Hamrah yake magana dan itace bata kusa tun da duk yana kiran su haka,sai dai ita yafi kiran ta hakan.
Yar ƙaramar dariya yayi kafin ya mai da kallon sa kan mahaifiyar sa da take cewa bazai je ya watsa ruwa ba ya dawo ta san rigimar su da Leena yanzu idan aka fara babu ranar ganawa.
"Hajiya bari ba lallashi Baby na tayi fushi "
Ya bawa mahaifiyar sa amsa yana sakin murmushi.
Hannun Leena ya riƙo da kyau yana mata raɗa a kunne ban san a bun da ya furta mata ba take ta washe baki tana furta " Allah Yaya " Kai ya jin jina mata shima cike da sakin murmushi.
Hajiya dai bata ce komai ba sai ma murmushi kawai da ta saki tana kau da kan ta bata re da ta damu da shiriritar ta su ba dan ba yanzu aka fara ba tun kan su kai haka,yake biye wa Leena dan sun fi shaƙuwa da shi a cikin yayyen na su,shi ne komai Leena dan haka ta ji zai dawo ta kama murna kenan a wasu lokuttan harda kitso da lalle take matsawa Ummah sai anyi mata saboda Ya Samir zai dawowa idan ya sanar musu, tasan school ɗin su ba,a barin lalle amma haka zata je ayi mata idan ta je su zane ta shi ko Samir da ya gane hakan sai ya daina sanar musu idan zai dawo dan haka har yanzu akan turban yake.
Tafawa suka yi da juna kamar wasu sa'o'i.
Ita ma Reena rigima ta aza sai ya tafa da ita dan haka cike da farin ciki suka tafa da ita.
Shigowar su Abduljabbar ce da Ayman,da suka fita wajen ball suka shigo cike da murna ganin motar sa sai ga Junaid shima a bayan su wanda ya fito yanzu da niyyar fita sai ya ga motar ya yan na su.
Cike da farin ciki da girmamawa suka masa sannu da zuwa yana amsa musu da sakewa da murmushi haka suka gama gaisawa yana ɗan musu tambayoyi suna Amsawa kafin kowannen su ya kama gaban sa musamman su da suka dawo daga wajen ball suna buƙatar saka ma jikin su ruwa zafi ya taso musu duk da sanyin Ac dake ta aiki a ƙaton falon.
Shima Junaid ficewa yayi yana zuwa kuwa ya sanar ma Ninah cike da farin ciki ta baro sashen Mahaifiyar ta da ta baro da kayan da Abba ya saya musu wanda ta ke ta fama gwaggwadawa ai ta na jin cewa ya Samir ya dawo ta cire kayan da sauri ta fito daga sashen tana dosar sashen Hajiya.
Dai dai yana cewa " Girls Bari na watsa ruwa na zo muyi fira dan ba zan ma yi baccin ba sai na sha labari ".
Da gudu ya tara Ninah da ta shigo itama a Guje tana kiran sunan sa.
Baki washe ya tarbe ta yana rungume ta kafin itama ya ɗaga ta sama yana lilo da ita tare da faɗin " Little naga kin ɗan ƙara girma,Keda Reena,Baby na kawai naga babu wani chanji gata nan yar firit ".
Dariya duka suka yi sai Leena da ta tura baki gaba kafin ta fara hawaye tana ɓata fuska tace " Ba yaya B bane ya sako ni gaba gashi harda karya mini kashin baya na yayi,kuma Ni ban yiwa ma Babyn sa komai ba,amma aka mun ƙazafi ".
Ta kai ƙarshen zancen kamar Dagaske jawabin nata.
Waro idanu yayi shima ya ɓata fuska yana cewa "Wai meya sa ya'ya Bilal ya saka mini Baby gaba,Ni na san baki taɓa Leena ba ai,ke da babu ruwan ki ko yatsa aka saka Miki a baki na san ba zaki ciza ba "
" Gaskiya bai kyauta ba,kuma zan masa magama kar ya ƙara shiga sabgar Baby na ". Duk da akwai tazaran shekara ɗaya a tsakanin su hakan bai hana su mu'amala da juna yadda ya dace ba duk da shi Bilal bai da irin muguwar sakewar nan kamar shi Samir ɗin.
kai ta lanƙwashe tana Murmushi tana jin. wani daɗi a ranta jin zai masa magana duk da ta san Bilal ne Babba amma ta san zai saurare sa saboda kamar ƙawaye haka suke tare suka tashi su biyu.
Ita kuwa Reena ka sa haƙuri tayi dan haka ta ce " Yaya fa bugu na tayi har ta sumar da ni,shine fa yaya ya dake ta kuma har yayi fushi da ita,yanzu ma duka faɗa take yi dashi,shima yaya B babu ruwan sa da ita ".Ta kai ayar maganar Tata cike da damuwa kamar zata yi kuka.
Uwar Harara Leena ta makawa Reena taana ji kamar ta jawo ta ta ƙara jajjagawa,sai kawai ta buga ƙyafci dan taji Haushin Reena ta ƙarya ta ta tunda ta san bai son tana faɗa ce faɗacen nan kamar dai Bilal shi bugun ta kawai bai yi sai dai ya yi fushi da ita.
Shi ko Samir murmushi kawai yake yi saboda ya san Gaskiya ya san komai dake faruwa ya ji a bakin Bilal ɗin,kuma ya roƙe sa ya daina dukan ta ƙuruciya ce,dan haka bai nuna musu ba kawai ya share zancen Reena ta hanyar furta " Ku jira na zo,ku bani labaruka "
" Hajiya ta bari naje na watsa ruwa na dawo yunwa ma nake ji " Ya na zancen yana shafar É—an tumbin sa.Kai Hajiya ta gyada masa wadda ta fito daga kitchen yanzu tana Murmushi cike da jin daÉ—in ganin su Leena a arha dan ba su cika shigowa sashen na ta ba sai ko gaisuwa idan ta kawo su dan ita bata da mace ko É—aya duk maza ne.
Su Leena kuwa kowaccen su waje ta nema ta zauna bakunan su É—auke da murmushi sai kuma aka koma fira da Hajiya da take tambayar su ya Ummah take dan kwana biyu ba su haÉ—u ba koda wajen gaida sarakkan su ne dan itace kawai Ummah bata cika sakewa da ita ba.
Chapter 51 · 0% Book details