← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 110

Sashe 106

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alishat ce ta furta " Mamma ce Abbi ya tafi kawai kar ya makarar da shi ".
Murmushi Mamma tayi kafin ta ce " ÆŠan nema yau Abbi fushi zai yi da kai ".
Ta fice tana Murmushi.
Shiko Asad jikin Alishat ya shige daga tsayen da suke.
Hannun sa ta riƙa tana Murmushi sannan suka shige toilet guntun wandon dake jikin sa kawai ta cire masa ta masa wanka da brush sannan suka ɗaura Alwallah tare suka fito bayan ta ɗaura masa towel karami.
Koda suka fito short kawai ta saka masa na yara mai kyau da tsada sannan ta saka masa jallabiya mai kyau itama ta saka ta ta a bayan akan rigar ta ta barci mai tsawo da take da ɗan buɗaɗɗen gaba wanda har albarkatun ƙirjin ta da suke a tsaye chik suka bayyana.Ɗan kwallin ta yana akan ta kafin suka kabarta Sallah a tare a natse daga ita har shi suka yi sallar sannan suka sallame,a tare suka yi addu,a gwanin burgewa.
Karatun Alqur'ani ta fara bita masa yana Amsawa bayan sun yi azkar a tare na safe.
Sai da suka karanta kusan page biyu sannan suka rufe qur'ani.
Dai dai lokacin kuma Momma ta shigo É—akin da sallama É—auke a bakin ta murmushi kawai ta saki kafin ta ce " Allah ya sa yau an muna Addu'a ".?
ÆŠan guntun murmushi Asad ya saki kasancewar ya san da shi ta ke kafin ya ce " Na Miki kuma har da Dady na ma ".
Ya kai ƙarshen zancen yana washe bakin sa da yake ɗauke da yan tsirarun haƙoran sa da suke fara re sol kasancewar yana fira.
Zuba masa ido dukkanin su suka yi babu ma kamar Alishat ƙirjin ta da ya buga ne ya sa ta haɗiye wani abu mai nauyi a zuciyar ta kafin ta sauke numfashi ba tace komai ba sai ma Wayar ta da ta ɗauka a gefen bedside drower da ta sanya Chaji da dare.
Zama tayi bakin gadon tana kunna wayar ta ba tare da ta ƙara kallon gefen da Asad yake tsaye ba dan a duk lokacin da zai yi maganar mahaifin sa jikin ta mutuwa yake yi ta kan ji wata irin kunyar sa kunya mafi hana motsi domin kuwa duk duniya yanzu ba ta da kamar sa shine kawai abun da take kallawa tayi farin ciki sai kuma su Mamma da suka zame mata bango.Domin bata san ainahin abun da zata ce masa a kan mahaifin sa ba.
Mamma kuwa numfashi ta sauke kafin ta saki murmushi ta ce " Me ka roƙa mini " ?
Ta tambaya tana kallon kyakkyawar fuskar sa dake shar da ita.
" Na ce Allah ya sa kar ki tsufa "
Dariya Mamma tayi kafin ta ce " Yau wannan na samu kuma, toh nagde,Amma fa Asad tsufan nan sai ya zo wa Mamma ".
Shi dai murmushi kawai yake yi yana kallon Mamma dan shi yaro ne da bai cika hayaniya ba.
Ummiee yau ba zan je school ba ko "?
Ya furta yana mayar da kallon sa ga Alishat.
ÆŠan É—agowa tayi a hankali ta Kalle sa da idanun ta da suka É—an sauya kafin ta É—an yi luu da su kamar zata rufe sannan ta buÉ—e ta girgiza masa kan ta tana sakin guntun murmushi.
Ɓata fuskar sa yayi hakan ya sa itama ta ɓata Tata fuskar kafin ta ce " Asad yau fa akwai wasa ".
Cike da murna Asad yayi tsalle yana furta " yeeeh zan yi wasa da su Chuchu ".
Dukkanin su dariya suka yi mai Sauti.
Sai lokacin ne kuma Alishat ta kalli Mamma cike da murmushi ta ce " Mamma good morning ".
" Wannan yaron naki Mamma ya sa na manta bamu gaisa ba ".
Dariya Mamma tayi tana riƙo hannun sa ta ce " Shi ɗin ma yau bai gayar da Mamman sa ba ".
Murmushi Alishat ta saki a hankali tana kallon su musamman Asad dake ta miƙa ma Mamma hannu ta ɗauke sa.
Yana furta " Mamma Good morning ".
Cikin yar maganar sa ta yara da har yanzu bakin sa magana bata wani zauna ba.
ÆŠaga shi Mamma tayi tana Murmushi kafin ta ce " Fine,good boy, hope ka yiwa kan ka Addu'a kai ma ".?
Kai ya jinjina mata kafin ya ce " eh kuma har da Dady na na yiwa Addu'a ".
Kallon sa Mamma tayi tana Murmushi kafin tace " good,Allah yayi maka albarka ".
" Amin " Ya amsa yana jan jelar jallabiyar sa.
Ficewa da shi Mamma tayi zuwa na sa É—akin dan shirya sa kamar koda yaushe.
Har suka fita yana É—agawa Ummieen sa hannu yana murmushi sai kace wanda zai je wani wajen.Itama murmushi kawai ta Bisu da shi kafin ta ajiye wayar ta kwanta kan gadon tana sauke ajiyar zuciya ta tsirawa pop dake shimfiÉ—e a rufin É—akin.
Wayar ta ce da ta ɗan yi ƙarar shigowar saƙo ne hakan ya sa ta ɗan kalli inda ta jefa wayar kusa da ita kafin ta janyo ta a hankali.
Ƙaramin tsaki ta ja tana wurgar da wayar kafin ta rufe idanun ta tayi shiru kamar mai yin Bacci.
Miƙewa tayi zaune kamar an ce mata ta shi zaune.
Wayar ta janyo ta duba notification na saƙuna da suke kan shigowa wayan rutu tu da su musamman na new numbers.
Wani saƙo ne da ya shigo yanzu ta zubawa ido '' Yau ina son haɗuwa dake Dan Allah, wallahi ina son ɗanɗana zumar ki,ko nawa ne zan zube Miki,zan sakar Miki Naira kinji tauraruwa ta"
Sai daga ƙasa aka rubuta Alhaji Mamman.
Wani irin murmushi ta saki kasancewar ya fi sati biyu yana bibiyar ta kuma har yanzu ma ta kasa yin saving number sa,A hankali ta shiga what'sapp ɗin ta ƙara kalla saƙon da kyau.Tana jan Numfashi.
Fitowa cikin chat ɗin tayi inda ta fara bin sauran saƙunan da suke kamanceceniya da wanda ta karanta yanzu.
Sai da ta gama karance su tsaf sannan ta a jiye wayar gefe.
Alhaji Mamman kuwa dake zaune ya saka tumbin sa gaba a ƙaton bedroom ɗin sa ne yana jiran reply na ta ya ja ƙaramin tsaki yana fatan ganin wani alama bayan na duba saƙon da ta yi ma sa sai dai har ya ci zaman sa bakin gadon har ya miƙe ya fara Zarya babu alamar zata bashi amsa hakan kuma Bai dame sa ba domin kuwa ya ji labarin ta tsaf da izzar da take da ita da jan ajin ta dan bata hurɗa ma da ƙananan mutane sai manyan Alhazzawa dan ko yanzu labarin ta a bakin wani abokin sa ne minister ne na security.
Kuma tun da ya ga ƙirar ta shekaranjiya ya ji gaba ɗaya ya kasa zama kurumm dan haka yayi duk yadda zai yi har ya samu ñumban ta da bayanan ta shi ji yake ma zai iya auren ta idan ta bashi dama tun da Ance bazawara ce mai lasisi ba dole sai ta bariki ba.
Wayar ta sa yayi wurgi da ita kafin ya miƙe ya faɗa toilet har ya saka wa jikin sa kumfa ya fito da sauri jin motsi a ɗakin kuma ya san bata wuce matar sa ce ba aiko da kumfa da komai haka ya fito yana bin bango tare da kiran sunan matar ta sa yana furta bani wayata kasancewar wayar ta shi bata da password a kan ta dan haka ya yi azamar fitowa gudun tonon asirin sa.
Sake da baki matar ta sa ke kallon sa data zo sanar masa da lokacin breakfast yayi ta zata bai ma tashi ba.
Salati ta rafka kafin ta kalli wayar dai dai lokacin shima ya sanya wata Babbar rigar sa pitch color ya rage kumfar.
Wayar ya janyo jikin sa na rawa,sannan ya juya hanyar toilet jikin sa na ra wa.
Hakan kawai jikin ta yake nuna mata akwai matsala mijin na ta bai da gaskiya.
Dan haka ga zuba masa ƙofar da ya bi da kallo.
Ƙyafci ta yi kafin ta ce " Alhaji breakfast ya zama ready ".
Daga chan ya amsa mata da ya ji.
Hakan ya sa ta ficewar ta Alhaji Mamman dake tsaye bakin ƙofar toilet ne ya buɗe ƙofar ya leƙo ganin Babu kowa a cikin hakan ya sa ya fito da sanɗa ya ajiye wayar ya koma.
Aiko yana shigewa ta fito babu wahala sai gata cikin saƙonnin sa na what's app.
Aiko ƙirjin sai da yayi muguwar daka kamar zai fito daka ƙirjin ta sunan take ta nanata wa. A bakin ta.
" Leesha "
Inda ta taɓa jin sunan take son tunawa sai dai ta kasa dan haka jin motsin alamar fitowa zai yi hakan ya sa ta yi sauri ta ajiye ta fice cikin sanɗa tana nazarin sunan da ya tsaya mata a ƙirji.
Kitchen zata koma amma ta kasa dan haka bedroom ɗin ta,ta koma ta ɗauki wayar ta wata number ta yi dialing ringing ɗaya biyu aka ɗaga cike da azama bayan sun gai sa ta ce " Anty Ruƙy wai ni ko kamar na taɓa jin kuna labarin wata yarinya yar bariki haka na ga sunan a wayar Alhaji da chat da yayi mata,shine nake son tabbatarwa idan ita ce ".
Daga chan ɓangaren ne aka furta " Leesha kike magana kenan "?
Wani irin faÉ—uwa gaban ta ya cikin mazarin baki ta lailayo ashar ta sauke kafin " tace ita fa,ita nake nufi ".
Murmushi ta wanchan ɓangaren a kayi kafin ta ce " Makiyya ki raba kan ki da yarinyar nan dan bomm ce ina faɗa Miki zata iya rabaki da Alhaji Mamman wallahi rabuwa ta har abada,ki bi komai a hankali a rabu lafiya,duk yadda kike tunanin yarinyar nan ta wuce haka,ita nata jawarcin mai lasisi take da barikin ta,dan haka ki bar komai hannu na".
" Wai ni me take dashi haka suke ta tura kan su gare ta haba wallahi dole mu É—auki mataki ".
Hajiya Makiyya ta yi furucin a hasale.
Ta ɓangaren Anty ruƙy kuwa numfashi ta sauke kafin ta iya furta " Wallahi da kika sani Alhaji sai da na kauce sannan na samu ya rabu da ita,saboda yarinyar ta haɗu ko ni da nake mace na sara ma baiwar da Allah yayi mata ta sura bayan haka ga kyau kamar wata ɗiyar aljanu wallahi sai dai kin gan ta a fili zaki iya fahim ta ta,kuma duk masifar nan taki wallahi ta na iya shanye ki,dan magana guda zata faɗa Miki ta kashe Miki motsin zuciya saboda zafin ta ".
Chapter 106 · 0% Book details