Sashe 57
Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mubarak kuwa ya sauka ƙasar Beijing china lafiya dan sanin da yayi wa Ogan na sa kuma aminin sa da yake ma kallon ɗan uwan sa na jini ko ya kira sa ba lallai ya samu zuwa ɗaukar sa ba hakan ya sa koda ya fito daga cikin jirgin bai yi gigin kiran sa ba sai ma ƙokari tare taxi da yake yi.
Sai dai kamar an ce ya juya ya hango sa jingine da wata irin lafiyayyar mota mai ƙirar Naira ya harɗe hannayen sa cikin ƙirjin sa haka ƙafar sa ɗaya ya ɗan karkata ta da take sanye da kafiyayun baot masu kyau,yana sanye cikin kaya mara sa nauyi kamar shigar ɗazu guntun wando mai kyau da wata yar riga armless sai uban rado dake kan fuskar ta da wanda har yanzu bai cire shi ba daga nesa gashin sa sai sheki yake yi wanda yake shan gyara.
Murmushi Mubarak ya É—an saki kafin ya taka izuwa inda yake.
Yana kaiwa wajen da yake ya shafa kan sa yana furtawa a hankali " thank you sir "
Ko kallon sa MAHAJ bai yi ba sai koma wa da yayi bayan motar yayi zaman sa kamar yadda ya zo dan yana da driver da ke kula da shi idan Muby baya nan dan ba kullum yake tare da shi ba saboda shine yake taimaka masa a wajen kasuwancin sa nan da yake gudanarwa.
BuÉ—e masa drivern yayi ya shige yana masa godiya kafin suka bar filin jirgin.
Koda suka isa masaukin su dan wani Babban apartment ne mai dauke da gidaje masu kyau irin tsarin ginukan Chinese masu kuɗi komai ya ji tabarkallah.A wani irin Babban fili na ajiyar motoci suka yi parking cike da ƙasaita ya fito bayan driver ɗin ya buɗe masa.
Ficewa yayi ba tare da ya magana da kowa cikin su ba.
Shima Mubarak da ya bude da kan sa murmushi kawai yayi yana ayyana wa a ransa miskillancin na asali ya motsa dan haka ya karɓi jakarsa hannun Drivern da ya Fiddo masa a boot godiya yayi ma ba chinen mutumin kafin ya shige ƙofar da na ga ya shiga mai ɗauke da wadattacen glass,sai da akayi scanning na sa sannan ya shige bayan ta wangale.
Ƙaton Falo ne na alfarma da yake ɗauke da komai hanyar upstairs ya kalla kafin ya saki murmushi kawai sannan ya Miki hanyar.Tafiya yayi kaɗan ya iso wata ƙofa mai ɗan kyau itama ta glass sai da ta gama scanning ɗin sa sannan ya shige kayan sa kawai ya ajiye ya faɗa toilet domin samun damar sauke gajiyar da ya kwaso.
Duk da tafiyar jirgi ce amma yana jin jikin sa yama da tsami dan sun É—auki a wanni da dama a saman iska.
A ɓangaren Mahaj kuwa ƙudundune yake cikin ƙaton duvet sai dai bai rufe jikin sa ba gaba ɗaya dan kana iya hango fresh skin ta sa da take ta sheki kasancewar babu riga a jikin sa yana shigowa ya zare ta.
Wani irin kwalba ne kamar na gold mai cycle sai ƙyalli yake yi ajiye yake a gefen sa kan bed side drower ta makeken gadon na sa dake ɗauke da bedside lamp a kowanne gefe gefe da gefe.
A hankali ya lumshe idanun sa da yake jin sun masa nauyi saboda rashin samun isasshen bacci tun dawowar sa ya maida hankali akan presentation ɗin domin zai wakilci school ɗin su ne su uku aka zaba shi daya daga Nigeria sai wani dan China da wani dan america guda dan haka ganin Makarantar ta nuna bukatar kulawar su yake iya ƙoƙarin sa wajen yin research mai ma,ana da gamsar wa.
Zuƙar hayaƙin flavour shi shi yayi yana jin wani iri a kan sa da yadda yake jin hayaƙin nan na kawar masa da komai da yake damun zuciyar sa.
Zuƙa yake yi a hankali sai dai irin zuƙar nan mai ja da yawa dan da ganin yadda yake shan ta kasan ya saba da ita,zuƙa yake yi sosai wanda take hayaƙi turneƙe ɗakin, tari ya fara a hankali yana jan numfashi lokaci ɗaya idanun sa suka yi jaa.
Mubarak da yayi wankan sa ne ya fito ya faɗa wa MAHAJ ɗin saƙon Samrah ya faɗa Bedroom ɗin da sauri cike da tashin hankali bayan ƙofar ta wangale.Aiko da wani irin mugun sauri ya kunna na'urar da ke korar hayaƙin abun ka da kasar da ke da technologia take ya fara ɓacewa da sauri ya matsa ya fisge shi shi ɗin dan har yanzu tarin yake yi kuma ya ƙi daina zuƙar ta.
Kashe ta yayi gaba É—aya cike da damuwa ya ke kallon mahaj da ya zuba masa idanun sa da suka rikiÉ—e yana kallon sa irin na ban son shisshigi.
Mubarak yi yayi kamar bai fahimce sa ba dan haka ya sauke kan sa ƙasa dama ba kasa fai yake haɗa ido dashi ba duk da yana masa maganar bai son munafunci ya daina masa hakan amma saboda girmamawa yake kasa wa sai irin wayen nan lokuttan.
Bai ce masa komai ba sai ficewa da yayi da kwalbar yana jin babu daɗi a zuciyar sa dan ya san muddin ciwon sa ya tashi a kwai matsala kafin a samu farfaɗowar sa sai ya ci wahala gashi har yanzu babu wanda ya san yana da wannan ciwon sai shi Mubarak ɗin da Ayyah Abbu bai san komai ba saboda ciwon bai taɓa ta shi a gaban sa ba,a mafi yawan lokutta zuciyar sa ma idan ta motsa tana tayar dashi dan haka Mubarak yake kaffa kaffa da shi dan daga baya ciwon ya bayyanar masa sai chan baya ayyah ta san yana tasar masa dan ta taɓa kai shi asibiti aka faɗa mata matsalar harda maganin sa tunda kuma ya tashi ya san abinda ke damun sa yake saurin danne fushin sa,sai gashi ta silar wannan hayaƙin yake shirin tado ma kan sa da lalurar da yayi kwana biyu babu ita dan ya manta ma da yana da ita ta daina ta shi sosai chan baya harda damuwa take ƙara mata ƙaimi kuma duka Mubarak ne yayi kula dashi a lokacin yana school tare dashi kuma suka ɓoyewa Abbu itama Ayya abun bai wani dame ta bata taɓa faɗawa Abbu ba a cewar ta ba zata kashe ɗan ta ta raya na wata ba saboda ta san yadda Abbu ya tsani ciwon ko kan ƙani ne a jikin MAHAJ ɗin sa take yake sauyawa saboda damuwa Bpn sai ya tashi.
Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanun sa da suka garwaya daga asalin farin madarar su.
Ƙofar da Mubarak ya banko ce ta sanya shi ya mutsa kyakkyawar fuskar sa kafin ya ɗan harari ƙofar yana sakin murmushi a zuciyar sa dan haka yake ƙara jin ƙaunar Mubarak saboda kyawawan ɗabi'un sa yana bashi kulawa kamar ta mahaifin sa da mahaifiyar sa yana iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya riƙe amanar da Abbu ya basa dan koda ya fahimci MAHAJ na shan shi shi bai matsa masa da dole sai ya daina ba yayi dai koƙarin ganin ya yi yadda zai yi ya rage har Allah ya sa a samu ya daina tunda itama shan ta baida fa'ida dan hayaƙi ce itama yadda taba zata cutar haka itama zata taɓa huhu.Sannan bugu da ƙari cutar da yake fama da ita.
Jan jikin sa yayi ya kwanta yana yana sauke numfashi ya san Mubarak yayi fushi daga jin yadda ya banko masa ƙofa.
Kasancewar dare ya riga yayi dan a gogon ƙasar har ya nuna sha biyu na dare wanda gari yake kamar rana hakan ya sa ya tofa addu'oin kwanciya bacci kafin ya miƙe ya kashe haske ya bar bedside lamp wanda itama ta gefe ɗaya kawai ya kashe ya bar ɗayar tare da rage ta..
A haka barci mai daÉ—i ya kwashi É—an Abbu.
Mubarak da ya dawo yanzu ne ya tura ƙofar a hankali ganin ya kashe haske ne ya san cewa yayi barci hakan ya sa ƙatuwar TV dake aiki a hankali wadda take dai dai da saiti gadon ya kashe ta kafin ya matsa ya kashe masa Hasken bedside lamp tare da rage masa gudun Ac saboda ita kan ta illa ce a gare sa amma haka ya ke ƙure ta.Dan haka yake fama dashi a kullum idan suna kasar nan.
Baya shigo masa Bedroom sai yayi barci ko ya same sa a irin haka amma iyakar sa Falo.
Ficewa yayi bayan ya gyara masa kwanciyar ta sa dan filon mai taushi ya bar kan sa sai ya zama na ya aza kan sa a kan hannayen sa da suke ta shinning da alama zasu yi taushi dan Jawur haka suke sai alamar taushi da suke da shi a bayyane kamar na sabon jariri.
Kyakkyawar fuskar sa da take Baby face wanda zaka tabbatar jikin ne kawai amma yaro ne shakaf MAHAJ matashi mai tasowa cike da burikan rayuwa da wani irin raunin zuciya da ya rayu dashi,wanda yake fatan wata rana ya sauke wannan nauyin ya samu farin ciki.
Murmushi yayi cike da tausayin sa sannan ya fice daga ɗakin take kuwa ƙofar ta rufe ruf wadda take kamar ta Karfe kamar kuma glass dan itama sai ta bincike ka tsaf amma idan ta saba da ɗaukar baya nan ka kana zuwa take buɗe maka ka shiga.
Shima kasancewar ya kwaso gajiya hakan ya sa yana dawowa ya nemi waje ya kwanta shima cikin haÉ—aÉ—É—en bedroom É—in sa mai kyau sai dai duk da haka na MAHAJ ya fi sa nema ba kusa ba.
Asuba ta gari.
" Ta baiwa ki cigaba da aiwatar da komai cikin natsuwa muna samun nasara an kusa Haska duhun da ke bai baiye dake yanzu kawai jini za'a ƙara ba wa su ɗan duhu zasu bazama kuma suna son na sabon jariri da na mai ciki dan haka aiki ne Babba "