← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 110

Sashe 39

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

••••••••••••A ɓangaren SHATOU kuwa duk yadda Inna ni take ƙoƙarin ɓoye wa Baffa na sai da ya fahimci cewa yar sa ta girma dan haka addu'o,i kawai ya bita da su cike da farin ciki da mamakin ɗan mutun girman sa babu wuya idan akwai rayuwa wanda ya sa har ya tuno da wani shuɗaɗɗen lokaci da bai taɓa tsammanin shatou zata zama mutun ba.
Sai dai mutuniyar taku babu abinda ta ɓoyewa su Amina.Suka dinga murna suma sun kusa girma kamar Shatou tunda Inna ni tace ta girma nan gaba kaɗan zata zama Babba.
A ɓangaren rigimar ta da Iro sai abun da yayi gaba domin sai da ta rama cin kashin da yayi mata bayan ta tabbatar shine dai wanda yayi rubutu akan allunan makarantar su.
Dan haka ta fashe masa tayun keke gaba É—aya,fashi kuma irin na babu gyara.
Koda Iro yayi bincike ya gano Shatou ce dan haka ya ƙullaci sai ya wulaƙanta ta,tare da ɗaukar zugar ƙawayen sa.Yanzu haka yar ɓuya ake yi tsakanin su.Dan ita da kan ta ta san tayi masa illa babba wadda kuma take farin ciki har cikin ranta.
Inna ni kuwa mugun daɗi take ji a tunanin ta shatoun ta yi hankali tun ganin kwana biyu bata ɓallo masu wata rigima ba da iro tunda shine abokin faɗan ta.
Sai dai kamar haka ne dan ta rage yawon Sosai,ko farauta yanzu ba kullum take bin su ba.
Tafe Suke a hanya su huɗu,sun kaiwa Maman ramata aiken da ta musu,suna tsalle tsallen su na yara masu ƙuruciya.Ta furta "So nake Ɗan gidan elibabeth ya dawo na rama cin kashin da yayi mini dan ban manta ba " Kai Amina ta ɗan juya tana dariya saboda ta san maganar ramuwa ce dan kwana biyu da suka wuce Shatou kullum cikin jini nin sa take in ta haɗu da shi sai ta masa wulaƙanci,kamar yadda ya wulaƙan ta ta.Tana batun furta wata kalma akan zancen na zuwan sa sai kawai taga SHATOU na sakar mata harara da ta sakata haɗiye maganar ta.Kafin kuma tayi gaba tabar su nan cirko cirko.
Da sauri suka bi bayan ta har da haÉ—awa da É—an gudu,kamar yadda ta fara gudun itama.
Ramata ce ta furta " ki jira mu Don Allah shatou "
Chak ko ta tsaya saboda jin sunan Allah da Ramata ta ambata,saboda SHATOU akwai taƙawa duk abinda ka haɗa ta da Allah kan sa kagama dan haka su Ramata da sun fara abu ta zille sai su haɗa ta da Allah sai kiga ta sauko anyi komai cikin natsuwa.
Suna isowa kusa da ita suka jera suka cigaba da tafiya kowannen su na sauke numfashi dan sai da suka haÉ—a da gudu.
Turus tayi ganin Wanda ke gaban ta,kamar an jefo sa, cike da masifa take kallon sa dan duk da ta san ta masa rashin mutunci bata jin zata nuna masa ta ji tsoro dan bai isa ba.
Kallon kallo aka fara tsakanin su,suko yan zugar abokan sa sai wani ciccira suke yi jira suke yi kawai ya basu umurni su hau ta da bugu dan bulali ne hannun su masu girma,ashirye suka zo bayan samun labarin an ga Shatou ta wajajen Layin Audu mai chemist itada su Amina.
Su ko su Amina tsoro ne ya mamaye musu zukata musamman ganin wayen nan bulolin sai hankalin su ya ɗaga matuƙa babu ma kamar Amina.

" Yau dai na kama ki bayan gama ɓoye ɓoyen ki,ke Ni zaki wulaƙanta,yau Bama zan jira hukuncin mai gari ba da kaina zan hukunta ki,kuma in kin isa ki rama ".

IRO yayi zancen cike da gadara da rashin mutun cin da ya zo da shi.
Hanɓare baki tayi bayan ta kyaɓe sa tana galla masa harara cike da rabin tsoron ta.Sai kuma ta saki guntun murmushi irin na rainin wayau kafin ta riƙe ƙuguu tana cewa " Ai dama jiranka nake yi,mu haɗu fuska da fuska,dan na shaida maka cewa ba zan taɓa yafe maka ba,abunda nayi maka bai cire mini zafin abubuwan da kayi mini ba,wai har Ni zaka ƙaryata kai da wayen nan ban zayen abokan na ka,saboda son ranku baka san abun na raina bane ko me,Sannan ka koma ka yi mini wani suna chan da bai da daɗin faɗa ma,kuma ka sake ƙarya ta ni,ai nikaina wannan karon ba sai an je gun mai gari ba "

Duka Idanu suka zuba mata sake da baki ƙaramar yarinya na zaro zance cike da rashin tsoron ta yadda ma take juya ɗan ƙaramin bakin ta yake kallo wasu miyau iro ya haɗa yana ƙarewa Shatou kallo daga sama har ƙasa irin kallon da bai taɓa yi mata shi ba.
Idanun ta da take ƙara juyawa cike da masifa yake ƙara bi da kallo.
Sai dai kafin ya iya cewa wani abu ya ji saukar bulala bulalar nan ba jikin kowa ta sauka ba face jikin Shatou wani daga cikin su ne mara haƙuri wanda yake mugun jin Haushin ta ya far mata saboda ta kira su da wawaye dama wanchan karon cike yake da ita.Cike da Masifa Shatou ta kai ƙasa tana kururuwa kafin ta kwaso ƙasa ta fara auna musu a jiki idanun ta a rufe cike da masifa.
Dai dai lokacin kuma manyan motocin da ke ratsa hanyar suka wuce su.Su Amina kuwa cike da tashin hankali ganin an fara da Shatou suka fara neman hanyar gudu itako babu alamar zata motsa sai dai cikin ikon Allah tayi musu wankan ƙasa yadda take so musamman wanda ya dake ta dan gaba ɗaya idanun sa sun rufe da ƙasa dan bai ankara ba ya jita kamar yadda itama bata zaci jin bulalar ba.Iro dai da ya ga Kamalu ya riga ya gama aikin da bai bashi dama ba hakan ya sa ya kakkaɓe ƙasar da ta gama musu wanka da ita wadda ya cire ta idanun sa da ƙyar sannan ya ce " muje kamar baƙin nan sun shigo fa " Yana yi yana kallon suturar jikin sa da tayi buɗuɗu.Yana ma tunanin yadda zai je wajen haka yaron nan ya masa kallon banza.Basu kula Shatou dake Masifa ba tana Allah ya isa kuma yanzu yanzun nan sai ta je ta samu mai gari da cin fuskar da suka mata bata musu komai ba dan ta riƙe shatin bulalar da ya ɗan kwanta mata.
Basu kula ta ba suka miƙe hanyar da suka ga baƙin motocin nan sun wuce saboda inda za,a fara aikin ne yau ne ranar ƙaddamar da shi.

Ita ko shatou cike da masifa ta miƙi hanya bata zame ko ina ba sai fadar mai gari sai dai ta tarar da ya tafi chan gurin dan haka ta nemi ƙofar gidan na sa ta zauna tayi zaman nan na duk wanda ya tara ya samu dan jira take wani ya mata ko kallon banza ne ta masa rashin mutunci.Kamar ko sauran ya yan mai gari sun sani duk wanda ya zo da yayi mata kallo ɗaya ya shigewar sa gida Mutun ɗaya ne Abu shine ya tsaya tambayar ta me take yi zaune cikin wannan rana.Sai dai kamar yadda bangon da take jingine da shi ba zai iya magana ba haka itama bata tanka masa ba.Yar ƙaramar dariya yayi kawai ya shige cikin gida dan ya san ɗayan biyu baza a rasa da wani a gidan take rigima ba ko Zaidu ko Iro da ya rasa dalilin da ya sa yake biyewa yarinya yar firit da ita amma ya biye mata shi idan shine da tuni ya fita iskan ta.Dan shi Mutun ne mai daraja mutane ba halin su ɗaya da Iro ba da Zaidu dan ko Iro rashin jin na sa sai ta kama yake yin sa ko ta Shero masa.
A dai dai lokacin da SHATOU take ƙara cika tana batsewa kuma alokacin ne aka ƙaddamar da fara aikin Gina manyan bohole da kuma fanfuna tare da aikin makarantar su Shatou.
Cike da farin ciki mai gari ya kamo hanyar gida tare da jama'ar sa tare da manyan motocin nan a bayan su saboda yadda mai gari ya Matsa da akwai babbar kyautar da zai basu dan haka babu musu Abbu da ya samu zuwa yau É—in saboda MAHAJ ya koma schl akan wani uzuri na gaggawa shi ya sa bai samu dawowa ba dole Abbu ne ya gabatar da aikin cike da farin ciki da alfahari.
Isowar su gurin ya bawa jama'ar dake tare da mai gari gyara wajen shimfiɗar cike da farin ciki dan abu ne da basu taɓa tsammani ba domin sun ji farin ciki sosai ba,a taɓa samun wani mai muƙami da ya kula da su ba kamar sa,koda suka kai koken na su ba suyi tunanin zai karɓu ba dan suna ɗan fama da matsalar ruwa kaɗan saboda a rafi ake ɗebo su kuma bohole ɗaya da suke da ita da wata ƙungiya mai zaman kan ta ta gina da daɗewa itama bohole ɗin sai a hankali Saboda ya tsufa kun san halin ƙarfe da ta tsufa sai dai a yi ta haƙuri.
Chapter 39 · 0% Book details