← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 110

Sashe 71

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune yake gaban wani haɗaɗɗen Glass mai kama da bango guda,wanda ke ta walƙiya yana haska yanayin da garin yake ciki.Sama ya zubawa ido yana kallon yadda Rana take ƙara haska garin Beijing,mutanen garin kowa sai harkar gaban sa yake yi wasu kan mota,mashin,Keke,wasu ƙafa.Komai cikin tsari gwanin burgewa.
Idanun sa ya É—an lumshe a hankali kafin ya buÉ—e su yana sauke ajiyar zuciya a hankali da numfashi a lokaci É—aya.
Wuyan vest ɗin sa da ke ta shinning fara ƙar da ita da ta haɗe da fatar sa ya gyara.Dan ita kaɗai ce jikin sa sai Short daga bakin guiwar sa bai ma kai chan ba dan haka Santala Santalan ƙafafun sa da suke ɗauke da gashi suke bayyane sai walƙiya fatar ke yi tana kashe ido. kasancewar yau yana Hutu ne zuwa gobe zasu gudanar da Presentation ɗin su dan haka yake zaune wajen yana hutawar sa.
Yar sofa É—in da yake kai mai zagaye wadda ke É—auke da HaÉ—aÉ—É—en center table shima a kusa da ita inda take É—auke da ruwa da glass cup mai kyau da tsada.
Ƙoƙarin tsiyaya ruwan yake yi a hankali cike da natsuwar sa jin maƙoshin sa ya bushe,Sai dai katawa tayi jin basu da maraba da ruwan zafi hakan ya sa shi jan ƙaramin tsaki yana Hararar ƙofa kamar yanzu Mubarak ɗin ya ajiye masa ruwan dan ya san zai buƙace su.Duk da ya san fushi yake yi dashi amma bai hana tun da safe ya zo duba yanayin da yake ciki ba,ganin sa nan zaune ya sa hankalin sa ya ɗan kwanta dan haka bayan gaisuwa bai ce masa komai ba,ya ɗauko masa ruwa ajiye yayi gaba.
Wanda har ya fita da gefen ido yake kallon sa,yana mamakin wannan fushi sai kace rayuwar sa zai ra sa.Rufe goran ruwan yayi da kyau.Miƙewa yayi ya matsa wajen wata na'ura kamar dai hot and cool sai dai ita wannan magana take yi abun ka da technologia sannan ga ta dai kamar na'urar Haɗa cupy amma ba ita bace.
Ƙaramin tsaki ya ja jin yadda na'urar ta cika masa kunne shi ya sa bai cika damuwa da taɓa ta ba ya fi gane wa ya ɗauko na fridge,ciwon sa ya san bai son sanyi dan haka yake takatsantsan yake kamantawa yana shan masu ɗan ɗumin sanyi,amma shi Mubarak muddin zai ajiye masa ruwa basu da ɗigon ko na sanyi kamar wani mai zunubi, shi gani yake ma kamar mubeey ɗin na ɗunama ruwan.
Dawowa yayi ya zauna bayan ta tsiyayo masa ruwan da ta saka shi magana,inda ya sanar mata masu sanyi.
Dan haka ya sirka da wayen da Mubarak ya ajiye masa kurɓa biyu yayi ya ajiye.
Wayar sa ce tayi ƙara kobai bincika ba ya san cikin biyu ko Abbu,ko Samrah,ko abokan kasuwan cin sa irin masu naci da suke matsa dole dashi suke son yin tsare tsare ba Mubarak ba.Dan haka kullum yake sauya layi saboda ya tsani takura.
Abbu ne ya bayyana akan screen ɗin sa dake ɗauke da wani hoto na mace Black beauty da kamala hoton da yayi kyau har ya gaji wanda bai daɗe da samun hoton ba a cikin takardun Abbu,Tare da sunan Mahaifiyar sa a bayan sa dan haka ya adana shi sai kwanan nan ya sa aka wanko masa hoton ya ƙara yin kyau kamar yau aka ɗauke shi..
Cike da girmamawa ya yi sallama kafin Abbu ya fara jan sa da fira yana amsa masa sama sama.
" Abbu bari na mayar video call "Ya faÉ—a a hankali kamar mai tsoron maganar.
Abbu cike da farin ciki duk da ya san ba wata maganar kirki amma ganin fuskar sanyin idaniyar shi na saka shi farin ciki dan fuskar mahaifiyar shi yake gani a tattare da shi kuma ita take É—ebe masa kewa.
Zuba masa idanu Abbu yayi cike da so da ƙauna kafin ya ce " Wai Ni ko kana cikin abinci kuwa MAHAJ?,Dubi yadda idanun ka suka Zurma ,me yake damun ka ".?
Gaban shi ne ya faÉ—i jin tambayar da Abbu yayi masa dan shi kan sa yan kwana biyun nan ya san ya faÉ—a ko Mubeey bai samu dama bane da ya sha tambaya jiya.
ÆŠan murmushin gefen baki yayi kafin ya ce " Abbu Stress ne ".
Ɗan shiru yayi tare da shanye idanun sa da suke ta walƙiya da maiƙon nan na su.
A hankali ya ƙara furta " kuma bana samun isasshen bacci ne saboda presentation ɗin nan ".
Ganin yadda Abbu ya zuba masa ido cike da damuwa.
Numfashi Abbu ya sauke cikin yarda da maganar sa ya ce '' Allah ya taimaka ya bada nasara,a riƙa cin abinci yan samari har da shi na ramar mini da kai,nafi son ka yi ƙiba ka tara damtse ".
Murmushi ya saki mai sanyi yana shafa É—an wadataccen Gashin kan sa da na gaba yafi ya wa kamar dai irin na india haka ko turawa.
Samrah ce ya hango ta shigo da sallama sai dai ganin MAHAJ wanze akan screen ɗin wayar Abbu mai tsada hakan ya sa ta rugo da gudu bata ma ƙarasa Sallamar ba kasancewar Abbu na sai ti ƙofar ne ya bada baya daga zaunen da yake yana karatun jarida a haɗaɗɗen falon na sa.
Kai MAHAJ yake ta gyaɗa mata sai uhmm tun bayan yar tambayar ya ya take da yayi mata cike da sakewa da ƙaunar yarinyar.
Fira suke ta masa ita da Abbu cike da ƙauna shi dai iyakar sa uhmm uhmm a haka suka yi Sallama ganin da Abbu yayi kamar ya gaji da Surutun Samrah sai dai shi a nasa ɓangaren bai gaji da kallon wayen nan fuskokin ba Surutun ne kawai da zasu zauna haka da ya ji daɗi yayi ta kallon su,dan haka wasu lokuttan yake a jiye wayar ko system yana jin firar tasu sama sama wata rana kuma yayi muting yayi ta Murmushi daga ƙarshe Abbu ne mai datsewa saboda ya san halin kayan sa.
Miƙewa yayi gaba ɗaya ya bar wajen cike da tafiyar nan ta sa ta ƙasaita.
Babban falon sa ya koma yayi zaman sa yana chan za tashar labarai.Cartoon yake kallo kamar wani ƙaramin yaro ya mai da hankalin sa kacokan kan su yadda ya mayar da hankalin su kan su ka san yana son kallon toon ɗin.
A haka har lokacin Sallah yayi alwallah yayi ya fice, a masallaci suka haɗu da mubeey sai dai bai ce masa ƙala ba haka shima sannan ana gama sallah yayi gaba ya ma riga mubeey ficewa.
Mubarak kuwa da yake son yi masa magana ne ganin ya fice kamar ya É—au fushin da ya fi na sa hakan ya sa ya saki murmushi yana shafa sumar kan sa da take shan gyara itama yanayin ta sa dai irin ta matasan mu ta cikakkun Hausawa.
" ÆŠan Abbu rigima "
Ya faÉ—a a fili kafin ya kalli gefen sa kamar akwai wanda zai ji ko MAHAJ É—in na kusa.Yar dariya yayi kafin yayi gaba.
Abin cin da ake kawo musu kullum wanda sun riga sun yi ordern sa irin abincin nan ne na Chinese da kuka sani dai kayan Ruwan nan,na halittun ruwa (Sea food )sai snacks sune abincin su idan ba su ra,ayin cin na China ɗin,duk da akwai Restaurant mai kyau dake kusa da su da ake kala.kalan abincin Nigeria sai ka zaɓa.Amma saboda sun saba da na China ɗin suke cin abun su.Idan sun je Nigeria su ci na gida.
Ganin shi da yayi har an ajiye hakan ya sa ya ɗauki na MAHAJ wanda ya san zai iya ci yanzu ya shiga falon bayan ƙofar ta masa Surutun ta na koda yaushe na maraba musamman shi da ta san shi harda ɗan chat take gwada yi da shi saboda gulma😂,kamar dai yanzu.
Haka ya ji tana furta Sir MAHAJ is watching TV toon channel.

Na'urar ƙofa mai GULMA sai a KURMAN ƘADDARA 🚴🚴😂Kai fa'eeh shariii🚴

Murmushi yayi kawai ya shige ba tare da ya bata amsa ba.
Shi ko MAHAJ da ke zaune bai ma ji shigowar Mubeey ɗin ba dan hankalin sa yayi nisa sosai,Baki sake Mubeey ke kallon sa kenan dai Dagaske na'urar chan ke yi shi yayi tunanin ko tsohon labari ne waton har yanzu yana kallon toon ɗin lallai da aiki gaban sa garjejen ƙato da kallon Cartoon ina lafiya,shi bai ɗauke sa normal ba kana namiji kana kallon cartoon kamar wani Baby.
ÆŠan gyaran murya yayi hakan ne ya farkar da MAHAJ da ya saki jiki yana enjoying kallon sa.
Chanza tashar yayi zuwa ta wrestling da sauri saboda tun chan baya ya taɓa ganin sa sau ɗaya yace masa kayan yara ne fa wannan yallaɓai har ya rika masa tsokana dan haka ya dena kallon su kusa da mubeey ɗin.
Mubarak kuwa shanye dariyar sa yayi kafin ya ajiye kayan kan haɗaɗɗen Centre table dake ƙawace da falon kamar dai kujerun.✍️

Jama'a Allah ya shirya muna TA BAIWA.🥺🤲

Shatou i miss You🥺Ta gida na.😍😁

Wannan labari na kuÉ—i ne akan Naira#800

# _FA'EEH BG CE✍️_

Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haÉ—a document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746

Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞

_*KURMAN ƘADDARA*_

_©®Faiza Almustapha Murai_

_FA'EEH BG✍️_

P________3️⃣4️⃣

*BOOK ONE*
_FREE._

*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*

*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y

*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t

*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
Chapter 71 · 0% Book details