← Book details Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 110

Sashe 42

Kurman Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___________Tunda suka kama hanyar barin ƙauyen yake ta sakin murmushi yana ƙara jin wani lamari na ginuwa a zuciyar shi game da Shatou.Shi kan shi Mubarak Murmushin yake saki a gaban mota yana driving hankali kwance yana ji ina ma ace tare da MAHAJ suka zo ya ƙara ganin Abokiyar rigimar sa dan ya san har yanzu abun na ranta daga Hararar da ta ta sakar masa.
Ƙasa haƙuri yayi ya ce " Mubarak Ka san wannan yarinyar ne,hala,naga yadda take ta jefa maka Harara a ɗazu ɗan shafa kai Mubarak yayi kafin ya furta " eh wanchan zuwan da muka yi sai da aka yi rigima da ita da MAHAJ ".Ya kai ƙarshen zancen yana sakin ƙaramar dariya.Abbu kuwa idanu ya ɗan waro cikin mamaki yana furta " shi Mahaj ɗin ".Kai Mubarak ya gyaɗa masa kafin ya fara bashi labarin yadda komai ya faru.Kai Abbu yake girgizawa fuskar shi cike da murmushi babu ma abun da yafi bashi dariya furucin ta na ko shi ɗan gidan waye ne,ko ɗan gidan elibabeth da donath trup.Dariya ya ƙara saki mara sauti yana ƙara mamakin yadda Mahaj ya biye mata har da mayar mata da amsa ya kira ta mai bilicin.Ji yayi ya so ace a gaban shi komai ya faru dan haka next time ya ƙudurta wani abu a ransa.
" Baku kyauta ba ai da ya bada haƙurin amma na san ba lallai ma ta samu kalmar ba lallai MAHAJ ya haɗu da dai dai shi waton duk rashin son maganar ɗana sai da ta saka shi magana " Ya kai ƙarshen maganar ya na ƙara ƙawata fuskar sa da murmushi.
Shi ma Mubarak Murmushin ya saki kafin ya ce " abun da ba zai taɓa yuyuwa ba kenan Dady ".
Kai Abbu ya girgiza yana jingina kan sa da sit É—in kafin ya sauke numfashi da ajiyar zuciya a hankali ya cigaba da karatun jaridar sa sai dai duk bayan É—an lokaci zai saki murmushi wani irin nishaÉ—i yake ji a ran sa.
Baffa na kuwa gida ya wuce shima cike da jimamin lamarin da ya ke gani kamar alamara haka kawai abawa yar sa kuɗi irin wannan bai taɓa riƙa irin wayen nan kudaɗen ba kuma a hakan ma basu burge sa ba dan sai yake ganin kamar ba dan Allah Abbu yayi ba,ya san halin yan siyasa ance suna bada kuɗin tsafi,kuma suna bada kudaden su Badan Allah ba sai dan wata rana su nemi wani abu a wajenka,shi bai hango hakan gun Abbu ba dan a ɗan zaman da suka yi ya hango nagartarsa da kuma mutuncin sa da addinin sa da suka kai shi matsayin da yake kai yanzu domin a kallo ɗaya zaka shaida Abbu mutumin kirki ne mai nagarta.
Har yaje gida yana juya kuÉ—aÉ—en cikin aljihun sa.
Tun da ya shiga ya kafe Shatou da idanu yana kallon ta ita kuwa tunda ta ma sa sannu da dawowa ta cigaba da yan wasannin ta na kitson ɗiyar a guro ta toton rake tana kitson tana labta ma kan mai kamar na mutun,tunda ta fara Inna ni tayi mata faɗan ta daina saka mai,kar ta ƙarar musu dashi,ta amsa da, to ta tashi ta mayar da kwalbar,sai dai ashe ta ɗibi wani ta saka a saman ƙafar ta.
Dan haka Inna ni bata lura ba,tayi zaton ta mayar da shi dan haka take yin abun ta hankali kwance,hankalin ta ya É—auku dan haka bata kula da kallon da Baffa na yake Binta da shi ba.
Inna ni ce ta lura bayan fitowar ta daga É—akin ta yanzu kai tsaye ta ce " lafiya Baffan su kuwa ? "
Kai ya jinjina mata yana ƙawata fuskar shi da murmushi kafin ya ce " Babu komai A'ee kawai Shatou nake kallo naga sai girma take ta ƙarawa da hankali " .
Ba shatou ba har Inna ni murmushi tayi ita kuwa SHATOU wani daÉ—i ne ya mamaye ta dan haka ta É—aga idon ta ta kallo Baffa na Sannan ta ce "Allah Baffa na Dagske " ?
Kai ya gyaɗa mata kafin ta miƙe cike da wani irin tsalle tana furta " Yee na kusa yin Aure Nima "
Ido Inna ni ta waro kafin ta rarumi mabur kaki ta bi Shatou da shi aiko a Guje Shatou ta shige ɗakin Baffa tana Dariya dan ta san nanne kawa zata shiga ta tsira.Ai ko Inna ni bata matsa ba sai murmushi ta saki tana hararar ta saboda Baffa na ba zai barta ta taɓa ta ba saboda a ƙofar ɗakin ya zauna kan yar kujerar sa.
Murmushi ya saki yana furta " A'e kar ki karye mini ƙashin ya da wannan abun "
Yayi zancen yana nuna maburkakin.
Kai Inna ni ta girgiza kafin ta sauke a jiyar zuciya idan ta tuno da furucin Shatou.
Shi ko Baffa miƙewa yayi yana furta " fito yar albarka ".
Fitowa tayi tana Dariya.Bibu ma dake gyaran wasu tsofaffin fitilu da ya fara koyon aikin ya ƙara sakin dariya yana cewa kedai Adda SHATOU Allah ya kai damo ga harawa,Allah Ranar Auren ki akwai bidiri a ƙauyen nan ".
Dariya ta saki tana wani farfar da idanu inna ni da ta gani kai kawai ta girgiza tana yiwa SHATOU Allah ya shirya a cikin zuciyar ta.
Ita kuwa zama suka yi suka fara tsara yadda za,ayi bikin na ta ita Bibu suna dariya kamar yadda kuka san wadda take da tsayayyen saurayi.
Inna ni da take jin su bata kula su ba sai ma wani abun in an faÉ—a tayi dariya ta ji hawaye sun wanke mata fuska wanda take kaikaitar idanun su ta goge.
Har Baffa na ya ƙara fita bayan kiran da aka yi masa zancen da suke yi kenan.
Daga karshe da suka ishi Inna ni Sai ta watse firar ta sanya su shirin makaranta dole haka suka shirya suka wuce gashi yanzu lokacin zuwan bai ƙara sa cika ba ma amma saboda sun ishe ta ta ce su tafi kar suyi lattti.Haka ko suka fito suka wucewar su kowa fuskar sa turneƙe babu ma kamar Bibu dan bai gama gyaran da yake yi ba aka ce su tashi su wuce dan sallah kawai sai abinci da suka ci ya sa ya tashi daga aikin ita kuwa sana,a guda domin kuwa ɗiyan toton rake ɗin sun kusa goma kuma duka nata ne,haka take bin su layi layi kamar an zo gidan kitso tana kitse musu gashin wasu ayi musu hannu biyu,wasu zane.

Yau tun asuba haka ta tashi da a hargitse Saboda ciwon ya motsa gashi ta rufe ɗakin,Babu wanda ya ankara da halin da take ciki sai Nana da take kwana da ita a ɗayan wani ɗaki dake cikin bedroom ɗin dan ƙofar shi Anan take.Kamar ta dai irin hanyar da Suhail yake biyowa daga part ɗin.
Duk yadda Nana take kururuwa babu wanda ya ji ta saboda ɗakin a rufe yake,ta kasa buɗe nata ta kawo mata ɗauki saboda tsoro duk da ta na jin yadda take faffasa komai da ya ke na fasawa da wanda bana fasawa ba a ɗakin.Gashi sai wani irin Dariya take ban kawa tana cigaba da aikin hargitsa ɗakin dan abun da bai wuce mintuna goma ba ta lalata komai da ke cikin ɗakin.Ta daɗe hakan kafin Nana ta ji shiru dan haka koda Nana ta ji haka cike da tausayin ta ta buɗe bedroom ɗin na ta tana leƙowa sai dai a matuƙar razane ta saki wata irin Mahaukaciyar ƙara domin kuwa Ba kowa ta gani gaban ta ba face Ishaa Tsaye fuskar ta jina jina sai soshe soshe take yi tana ganɓalan dariya,ga kayan jikin ta duk sun lalace nan kwalba ta shige nan ta fasa ko ina ta ji ma kan ta rauni.
Ai kamar jira take yi dama shine tsayin da tayi ta faɗa cikin bedroom ɗin kamar an jefa ta sai ga Nana ƙasa tana neman agaji domin haye ruwan cikin ta tayi tana nusar ta,bugu na fitar hankali cikin abun da bai wuce mintina uku ba ta mayar da Nana kamar ta dan har kayan jikin ta ta yayyaga.
Rayyan da ya shigo ta ƙofar bayan ne ya ji kamar sautin kuka na ta shi sanin cewa suna da mara lafiya a gidan hakan ya sa babu tsoro ya fara ƙoƙarin tura ƙofar sai dai kamar an buɗe Kunnuwan sa tarr ya ji kukan Nana,dai dai lokacin da Nana take sakin wata irin ƙara kuma a lokacin ne Allah ya bashi ikon sanya spare key dake maƙale a chan kan wata yar fulawa mai kyau ta yan gayu da ya zaro.
Da Inna lillahi ya matsa wajen yana cigaba da Nana ta sunan Allah domin kuwa wuƙa ce Ishaa ta ke riƙe da ita wadda bai san inda ta samo ta ba.Cike da tashin hankali ya ambaci sunan ta " Ishaa "Ganin ko juyowa bata yi ba ta kalle sa hakan ya sa ya ƙara furta " MA'ISHA " shiru ta masa sai dai tana nan tana yaƙen nan da wasu marasa hankali suke yi.bata juyo ba sai da yayi mata kira biyu sannan ta juyo tana saita mishi wuƙar da take ta sheƙi dan da ganin ta sabuwa ce dall.
Dariya ta ɓalle da ita kafin ta ce " Sai na kashe su,sai na kashe su dukkanin ku,bana son su ".
Chapter 42 · 0% Book details